[Book] Al'adun Wasu Complete Hausa Novel by Batul Mamman

Al'adun Wasu

Title: Al'adun Wasu

Author: Batul Mamman

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Fiction

Doc Size: 582KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2019

Description: Sauke littafin marubuciya Batul Mamman mai suna "Al'adun Wasu" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu cikin sauki.

Book Teaser: Bismillahir Rahmanir Rahim Mal Bashir dattijo mai kimamin shekaru hamsin da takwas na shigowa cikin layinsu yara suka fara binsa suna oyoyo Baban yara. Da yake kullum haka suke masa shiyasa baya rabo da yar tsarabar da zai kawo musu. 

Hannunsa daya yasa a aljihu wanda daga tsintsiyar hannun a yanke yake ba yatsu sakamakon zarton da ya fada kai har ya tsinka masa jijiyoyin hannu. ya sha wahala sosai likitoci suka ce hannun ya mutu dole a yanke shi. Duk da haka bai dena zuwa wurin sanaarsa ba ta kafinta. 

Da dungulmin hannun ya bude aljihunsa ya saka mai lafiyan ya zaro carbin malam ya mikawa yaran. Suna ta murna suka tafi su raba. Yayi gaba yana dan murmushin suka hada ido da wani matashi a layin. 

Da sauri ya taba na kusa dashi kai don ubanka kashe ga Baban yara nan. Tare suka tashi suna karkade jikinsu. Baban yara barka da yamma suka fada da ya karaso kusa dasu. Ya dan bata rai bazan amsa ba Sani. 

Yanzu don Allah baza kuyiwa kanku fada ba da shaye shayen nan? Ya kalli katon ciki Anas so kake ciwon babanka ya sake tashi saboda kai ko? Wanda aka kira Anas ya girgiza kai. Kayi hakuri in Allah Ya yarda bazamu sake ba. 

Yayi murmushin takaici Allah Ya bada ikon denawa. Kuna ta batawa kanku rayuwa a banza. Idan baku sani ba abinda mutum yayi da kuruciya yakan bishi har girma. 

Na tabbatar babu wanda zai so nan gaba a bawa dansa labarin ya taba busa wiwi a tarihin rayuwarsa. Sani ya dan yi murmushin jin abinda ya fada. Baban Yara ya ce au dariya na baka ko? Ya kama bakin ya murde. 

Muna nan da ku idan baku dena ba wata rana kwata zaku shiga ku kwanta kuce gado ne. Yayi gaba abinsa yana ta mitar halin da yara ke saka kansu a yanzu. A kantin kofar gidansa ya tsaya suka gaisa Munkaila mai shago. 

Mal Bashir ya dauko naira dari ya mika masa. Gashi nagode sosai. Munkaila ya karba na meye kuma wannan Baban Yara? Darin da ka bawa Zuhra mana da safe. Ina shirin fita ta tambayeni kudi zata je karbo sakamakon jarabawarta. 

Lokacin bani da chanji shiyasa nace ta karba a wurinka. Munkaila ya mika masa kudin, ai yau ko sau daya banga fitowarta ba. Mal Bashir ya karba ya shiga gidansa da sallama. 

Zuhra na yanka yakuwa taji muryar Babanta a soro. Hantar cikinta ce ta kada sosai ta tashi da gudu ta shiga bandaki. Garin sauri ta zubar da yakuwar da take yankawa. Ummanta ta soma fada ke lafiyarki kuwa. 

Mal Bashir ya karasa shigowa tsakar gidan. Ina ta sallama babu mai amsawa kamar babu kowa a gidan. Atine Umman Zuhra ta ce yi hakuri Baban Zuhra. Wallahi bari tayi min nake fada banji sallamar ba.

Takalmansa ya cire ya zauna kan tabarmar dake shimfide a tsakar gidan. Fitsari ta bari ya matseta shine take wannan gudun ko. Umma tace anya kuwa? Hira mukeyi fa kana yin sallama ta tashi kamar wadda ta ga abin tsoro. Baban yara na jin haka yasha jinin jiki.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post