[Book] Alheri Danko Ne Complete Hausa Novel by Ummi A'isha

Alheri Danko Ne

Title: Alheri Danko Ne

Author: Ummi A'isha

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Fiction

Doc Size: 238KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2015

Description: Sauke littafin marubuciya Ummi A'isha mai suna "Alheri Danko Ne" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu cikin sauki.

Book Teaser: Tafe yake yana cire  safar hannun dake hannunsa yana cillar da ita akan tile din dake malale aharabar runfar asibitin, leburorin wurinne suke biyeda shi suna tsince duk abinda ya yar awurin shikuwa sai faman yatsina fuska yake yi sai kace yaune ranar farko wadda yafara karbar haihuwa kokuma yafara operation,ahankali yake tafiya sai kace marar jini ajiki yana sanye da light blue colour din t shirt mai dogon hannu da black din jeans idonsa sanye cikin farin gilashi amma da alama gilashin nasa na gayune bana kara karfin ido bane, duk inda ya ratsa babu abinda kakeji sai weldon sir! Shi kuwa gogan baya magana sai daga hannu domin magana tana mutukar bashi wahala saboda yangarsa da jan ajinsa gashi da iyayi kamar mace amma hakan yana mutukar kara masa kyau kuma da alama iyayi nature dinshine, ayanda na hango fuskarsa zan iya kiyasta shekarunsa bazasu haura 27 ba aduniya,fari ne dogo siriri lange lange kana ganinsa zaka gane baya aikin wahala kuma hutu ya zauna ajikinsa, cikeda yanga ya karasa office dinsa wanda yake jere a rukunin ofisoshin manya likitoci ( consultants) wani office yabude yashiga wanda asaman kofar aka manna wani dan katako aka rubuta DR TAFIDA ajiki da manyan harrufa, ahankali yashiga cikin office din wanda yayi tsananin tsaruwa kamar ofishin shugaban kasa, kan wata doguwar kujera baka yaje yakwanta yamike yatasa kansa da hannun kujerar yafara cire (neck tied) din wuyan rigarsa yacire gilashin fuskar sa yalumshe manyan idanuwansa wanda suke zagaye da bakaken gashi masu mutukar baki sai da yadan huta sannan ya mike a hankali tamkar mace ya isa kan teburinsa yadanna wata kararrawa aguje wasu fadawa guda uku sanye cikin jajayen kaya suka shigo, suna shigowa suka fara zabga kirari, Allah ya taimaki mai girma tafida, dan sarki jikan sarki kuma sarkin gobe da yardar Allah, Allah yakara maka nisan kwana!

Also Download: 

Hannu yadaga musu take sukayi shiru saboda sun gane nufinsa kuma dama can shi baya son yawan magana duk maganarshi atakaice yake yinta itama sai takama mutuka amma in bakamawa tayi ba sai dai yayi umarni da hannunsa, kallonsu yayi yanuna musu kan table dinsa tuni suka zabura suka fara harhada takardun dake kan table dinsa gamida dibar wasu files manya, laptop dinsa da brief case dinsa suna gama harhadawa sukayi waje yayinda shi kuma dr tafida ya sake mikewa a kujerar da yake kai sai da ya shafe sama da minti 20 ahaka sannan yatashi yahau kan kujerarsa ta aiki yajawo drawer dinsa yaciro tabar wiwi (ganye) yadauki ashana ya kyasta yafara busa hayaki, wani dan madaidaicin glass cup ya ajiye musamman akan table dinsa inda yake tara tokar tabar da yakesha kuma da alama yana sha akai akai domin har kofin yakusa cika da tokar tabar, zukar tabar wiwin yaci gaba dayi har ta kare sannan ya kishingida ajikin kujerarsa nanma yashafe fiyeda minti goma sannan yatashi ya dauki phones dinshi da gilashinsa yafita daga office din yana fita fadawansa suka zabura suka nufi motarsa dasauri suka bude masa gidan baya yashiga yazauna suka rufe kofar motar suka runtuma tasu yayinda daya daga cikinsu yashiga mazaunin direba ya zauna yatashi motar ya harba suka bar harabar cikin asibitin.

Fita sukayi daga harabar asibitin mutane sai kallon motocin nasu sukeyi gamida daga musu hannu amma dan mulkin yana daga kishingide acikin kujerar baya hannunsa rikeda jaridar daily trust yana karantawa da haka har suka isa kofar fada inda anan gidansu dr tafida yake, wani makeken gida nagani gaba dashi kuma filine babba tuni digarawan dake zaune abakin kofar gidan suka mimmike tsaye saboda ganin motar tafida,kan motocin suka kutsa cikin babban gidan wanda yasha zane iri iri da adon kala kala irin na sarakai nidai ummi Aisha tun daga nan nagane cewar gidan sarki nashigo domin gaba daya tsarin gidan namasu sarauta ne, cikeda iyayi da takama hadida kasaita dr tafida yafito daga cikin motar yatasamma cikin gidan wanda akalla sai da aka wuce zauruka sunfi 5 sannan yakarasa wani babban fili mai dauke da part part akalla zasu kai guda 5 kansa tsaye yawuce wani sashe mai mutukar kyau wanda yasha ado da kwalliya, budewa kofar falon yayi yashiga nan nahango wani dattijon mutum wanda akalla shekarunsa zasu kai 65 yana kishingide akan kilisan dake malale acikin falon wanda yawansu zai iya kaiwa guda biyar kala kala gashi jikin bangon dakin yasha zane na sarauta, gefensa tumtum ne wanda yajingina ajiki ga kayan marmari nan agefe dangin itatuwa kamar su inibi, tufa, ayaba, kankana, gwanda, zaitun, ruman, da sauran kayan itatuwa cike cikin wani dan madaidaicin kwando wanda aka tanada musamman dan adana kayan marmari, cikeda alamun gajiya yayi sallama ahankali yashiga wannan al'adarsa ce duk lokacin daya dawo daga office sai yaje ya gaida mahaifinsa da. Mahaifiyarsa,washe fuska dattijon yayi ya amsa sallamar da Wa'alaikas salam wa rahmatullahi wabrakatu, barka da zuwa ibrahim cikin jin dadi yakarasa inda mahaifin nasa yake yazube akasa yafara kwasar gaisuwa,barka da hutawa mai martaba dafatan mun sameku lfy, ya akaji da jama'a? Cikin jin dadi yace alhamdulillah ibrahim dafatan ka dawo lfy? Lfy lau yafada yana murmushi gamida mikewa yana fadin nabarka lfy ranka yadade, Allah yakara nisan kwana, Allah yaja zamani.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post