[Book] Alhini Complete Hausa Novel by Zee Maman Khady

Alhini

Title: Alhini

Author: Zee Maman Khady

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Fiction

Doc Size: 181KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2019

Description: Sauke littafin marubuciya Zee Maman Khady mai suna "Alhini" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu cikin sauki.

Book Teaser: kuka take kamar zata cire ranta, idanunta sun kad'a sunyi jawur saboda tsananin kuka, fuskarta tayi face-face da hawaye, zaune take cikin d'akin kan tabarmar kaba, jikinta wata atamface Riga da zani, simple da ganin atamfar kasan tad'an kwana biyu saboda farin data d'an yi Alamar kod'ewa, sai wani madai-daicin hijabi data sanya, shima dai dagani kasan ba sabo bane, amma kuma wankakke ne, duk kayan jikinta basu tare da datti.

"Haba laraba kiyi ha'kuri ki daina kukan nan, sabi'u dai yariga ya mutu kuma kinsan kukannan naki baze dawo dashiba, Addu'a kawai yanzu yake bu'kata daga gareki, ta dafa kafad'arta kiyi hakuri dan Allah ki daina kukan nan.

Sai lokacin Balaraba ta kalli wacce keta faman rarrashinta tace "Haba indo dole inyi kuka, kukan nan danike shi kad'ai ze ragemin rad'adi  da ba'kin cikin danake tartare dashi, (tacigaba da kukanta,)

Indo tana matu'kar tausayama halin da 'kawarta take ciki, itama wasu guntayen hawaye ta zubar sannnan ta'kara matsaowa kusa da 'kawarta ta dafa kafadarta da hannu guda,

    gudan hannun kuma tana goge mata hawayen dake kwarara daga idonta, tace

    "Tabbass nasan rabuwa da masoyi akwai ciwo, baranta kuma rabuwa ta har abada, Amma dole kiyi ha'kuri ki d'auki wannan a matsayin jarabawa ce daga ubangiji.

Laraba ta fashe da wani sabon kuka, tace indo bazaki ta6a gane halin ba'kin cikin danake cikiba, ki duba kiga irin soyayyar da muka shimfid'a nida Iro acikin 'kauyennan muna burge Kowa, amma lokaci guda ana saura sati d'aya bikinmu yaje wanki rafi yafad'a ruwa sai dai gawarsa aka fiddo, tafashe da wani sabon kuka, indo ma kukan take, amma hakan be hanata rarrashin 'kawar tata ba.

Cikin sheshshekar kuka tacigaba da cewa "yanzu kuma :yau an wayi gari sabi'u shima ya mutu kamar yanda Iro ya mutu, wannan wane irin iftila'i ne yafad'amin.

Assalamu Alaikum, inna ce tashigo da sallama, indo ta amsa mata sannan tashigo d'akin, ta cire ijabinta ta rataye kan 'kyauren d'akin sannan takai dubanta ga Balaraba wacce taketa faman kuka indo kuma na rarrashinta wacce itama kallo d'aya zakayimata Kazan kukan tayi.

 Indo takai dubanta ga inna dake shirin zama kan kujera tace "lnna har kun dawo? 

   "Har na dawo indo ay anriga anrufoshi sai dai muyi mashi addu'ar samun rahamar ubangiji, sabi'u kam yayi mutuwar ban mamaki, duk da ba mamaki cikin lamarin ubangiji, amma mutane da dama sunce lafiya lao ya kwanta, kawai aka wayi gari ya mutu, wasu siraran hawaye suka zubo daga idon inna dan tana tausayama tilon yarta, wacce tayi rashin masoyi a karo na biyu.

Laraba ta fashe da wani irin kuka, ta taso daga inda take tafad'a jikin inna tana kuka,  "shikenan inna yanzu narasa sabi'u wayyo nashiga ukku, sabi'u miyasa kamin haka saida kabari na sha'ku dakai sannan zaka tafi ka barni, innalillahi,wa'inna,ilaihirraji'un, ta fad'a kawai sai ji sukayi tayi shiru ba Alamar numfashi tattare da ita, duka jikinta ya saki

Nan inna tashiga wani irin rud'ani tana girgizata tana kiran sunanta, "fatima..... Fatima innnalillahi nashiga ukku, 

    Indo dake tsaye hankalinta duk ya tashi tarasa inda zata sa kanta da gudu tafita daga gidan tana neman taimako.

"Dan Allah Hashim ka taima mani kada ta mutu, wanda takira da hashim yace "wacece zata mutu, bata bashi amsaba tacigaba da kuka tana cewa ka taimakeni, mutuwa zatayi, dan Allah, da gudu takoma cikin gidan.

Har yanzu laraba na rungume jikin inna ba Alamar numfashi tattare da ita, inna kuma sai kuka take tana kiran sunanta.

Da gudu hashimu yanufi gidan me gari ya aro baro,

Kofar gida ya ajiye baron, sannan yashigo gidan da taimakon, indo da lnna aka dora Laraba kan baron, Hashim ne ke tura baron da gudu.

 Lnna da indo suna biye dashi hankalinsu tashe suka nufi 'karamar asibitin dake 'kauyen.

Sannu Laraba sannnu kinji, kallo kawai take bin mutanen dake gurin dashi, idanunta suka ciko da hawaye, Inna tasa gefen mayafinta tana goge mata.

Sai da musalin 'karfe biyar na yamma aka sallamesu daga asibiti, bayan 'karin ruwan da aka sanya mata ya 'Kare, 

Indo kuwa duk abinnan tana tare dasu sai gab da magrib inna ta umarceta data koma gida kada anemeta,

    haka ta wuce tana me tausayama halin da 'kawarta ta tsinci kanta.

Hashim kuwa tinda akaje asibitin yaketa hidima da Laraba dan kusan duk kud'in da aka kashe shine yabiya, yana mutu'kar tausaya ma Laraba, 

Shima sai lokacin yabar gidan yanama Laraba fatan samun lafiya, inna kuwa godiya kawai take mashi dan ya taimakesu ba kad'anba, dan in baccin shi da batasan inda zata samu kud'in da zata biya na magani da 'karin ruwan da akayima Laraba ba.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*_BAYAN SATI BIYU_*

Zaune take kan guntuwar tabarmar da aka shimfid'a kan shararren gidansu na 'kasa, ta tasa kwanon abinci gabanta, ita bata ciba kuma bata maida ta rufe ba, ta zubama abincin ido tana kallo, wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta, tasa hannu ta goge.

"Yanzu Laraba bazaki cire damuwarnan daga cikin ranki ba, kiyi ha'kuri ki d'auki kaddara, kin riga kinsan dukkan me rai mamacine, muma nan mutuwa jiranta muke ko yau ko gobe ko jibi koma yanzu, 

Dan Allah kisama ranki ruwan sanyi.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post