[Book] Alqalami Complete by Yar Mutan Kankia

Alqalami

Title: Alqalami

Author: Yar Mutan Kankia

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: True Life Story

Doc Size: 317KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Littafi abin karatu, shi ko Alkalami abin rubutu. Ku sauke littafin marubuciya "Yar Mutan Kankia" mai suna "Alqalami" complete hausa novel a text document daga shafin nan namu yanzu haka.

Book Teaser: ********"Ita rayuwa duk abinda kaga ya sameka daga Allah ne,sannan ba wani abu dake faruwa saida ƙudurar ubangiji,dan haka akan me zan saka wannan matsalar a cikin zuciya ta!bayan nasan shi Allah yana tare dani a kowane hali nike ciki kuma duk rintsi duk wuya bayan nasan shi kadai zai mani gata!yakike so inyi da wannan matsalar data zame mani abin shana ba dare ba rana?tunanin ki daukar mataki shine mafita ko kuwa in biyema yan uwana,makota da sauran jama'ar gari ina maida masu raddi akan kananun maganganun su da sukeyi akaina wadda ba abinda zata sauya daga cikin *Qaddarata* wadda ta dade da tabbatuwa a wajen ubangijina karfa ki manta Allah SWT da kanshi yace rubuta! sai *ALQALAMI* yace ya ubangijina me zan rubuta?sai Allah maɗaukakin Sarki yace duk abinda zaifaru na rayuwa daga samu rashi mutuwa arziƙi yawan mutanen da za'a halitta,na daga mutun ko aljan komai da kika gani Asma'u bai wanzuba saida Allah maɗaukakin Sarki ya kaddara shi tahanyar sa *ALQALAMI* ya rubutashi a Alon Lauhil Mahafus wanda ke cikin gidan Aljanna,inko har kema kinsan hakan mi zaisa in tadama kaina hankali akan rayuwa bayan nasan *Haka Allah Yaso* ya ganni tunda komai ya gama wanzuwa ta hanyar *ALQALAMI* ,saidai kisani hausawa nacewa bakin alqalami ya rigadata ya bushe amman ni nasan nawa bai bushe tunda bawa bai fidda rai daga rahamar ubangijin sa,addu'a na sauya kaddara cikin yardar Allah,wadda ita na maida ibadata a kowane lokaci Asma'u dan Allah kiyi hakuri kuma ki toshe kunnuwan ki,akan duk abinda zakiji kigani a cikin gari ba kanmu farauba kuma ba kanmu karauba,saukin ma ke Danginki da Yan uwanki basu saka maki idoba da har suke ganin son zuciya da ruwan ido su suka hanaki fidda miji wanda nawa Dangin ke ganin hakan akaina saidai abinda nasani koma minene Allah ya kaddara mani mijin da zan aura da ya'yan da zasuzo ta tsatsona harda jikokina duk yasa alqalami ya rubuta wannan tunkan asan za'a halicci ɗan Adam akan mi zan zauna intadama kaina hankali bayan nasan su masu yimani wannan surutun basu isa sukawo lokacin Aurena ba har sai Allah ya kaddara faruwar hakan sannan zanyi dan haka kawata kisa aranki komai  *Lokacine* kuma yana nan zuwa kanmu tunda Allah yagama hukunta komai a cikin lauhil mahafus ta hanyar *ALQALAMI* .!"

zazzafan numfashi wadda na ambata da Asma'u ta furzar tana mai goge kwallan idanunta cikin kulawa ta kalleni tace.

"Hakane kawata kin kara mani hope da kika tunatar dani abun dana mance tabbas Allah yana taredamu duk runtsi duk wuya kuma shi zai mana gata a rayuwar mu,sannan komai lokacine Aure da haihuwa da mutuwa duk bawa bai gaggawar su,kuma bai jinkirin su da lokacin su yazo tabbas za'ayi dan haka nima nasama raina irin wannan hukuncin da kika yanke a cikin zuciyar ki Amina Allah yaimana jagorancin rayuwa.!"

Haka Asma'u ta ida maganarta cikin kunar rai dan lamarin yana tabama kawar tawa rai wanda ni awajena tun ina damuwa haryakai dana daina damuwa kwata kwata a cikin zuciya duk da bazance ban damuwaba saidai na rage kaso hamsin cikin ɗari,kama hannayen kawar tawa nayi nace.

"Naji dadin haka kawata insha Allahu,sai munji dadin zabin da Allah zai mana arayuwar mu,dan haka mukara mikama Allah kukan mu shine zai mana gata."

na ida maganar ina mata murmushi,itama kirkiro murmushin tayi a saman fuskar ta,da haka mukaci gaba da firarmu ta kawaye wanda mukeyi duk da kasancewar Asma'u kawatace kuma ta wani fanni yar uwatace ta bangaren mahaifiya ta,kamar yanda nagaya maki Yar Mutan Kankia nidai sunana Amina Yusuf kuma ni haifaffiyar Yar Jahar Katsina ce a garin da akafi sani da Caranci mahaifina ya kasance aikin Lawyer yakeyi mu shidda ya haifa a duniya mata huɗu maza biyu mu dukan mu da kike gani uwar mu ɗaya uban mu ɗaya,kamar yanda kikaji sunana da sunan mahaifina,sai mahaifiyata Khadija dukkan su haifaffun yan Caranci dake cikin jihar Katsina,abinda yasa na zabi da inbaki wannan tarihin na rayuwata duk da akwai shi da tsayi dan inajin dadin yanda kike ilimantar da al'umma ta hanyoyi daban daban cikin ruwan sanyi da taushin zuciya shiyasa nakawo maki wannan tarihin rayuwar tawa mai dauke da kalubale na rayuwa iri² banda al'ajabi wanda ni awajena ba abin al'ajabi bane,wannan dalilin yasa nace kibada labarina nasan zai zama wa'azi kuma ishara ga yan matan da suka kasance cikin hali makamancin nawa koma fiye da nawa naji dadin yanda kika karbi wannan labarin nawa da kuma yanda kika jajirce wajen isar da wannan sakon ta hanyar ALQALAMIN ki wanda ya zarce takobi Allah yabiya bukata Anty Jameey."

Murmushi nayima Amina wadda ke zaune a ɗakina nace mata.

"Bakomai Amina aimu marubuta da kike gani aikin mu kenan isar da saƙo ga al'umma kuma dukkan mu kowa na kokari ka'in da na'in wajen ganin sun ilimantar da al'ummar su,dan haka ki daina damuwa kamar yanda kika bani wannan labari haka zan zauna in rubutama al'umma shi akyauta duk da kuwa yanada yawa ni wannan ba damuwata bane kaunar da masoyana ke nuna mani kadai itace tukuicin Yar Mutan Kankia dan haka cikin kankanin lokaci zakijini da wannan labari naki kamar yanda kika bada shi,saidai karin da zanyi kadan ne saboda kinsan marubuci dole ya tsara labari yanda zaijema mai karatu cikin nishadi da farin ciki,sannan in zan fara posting zan maki magana sannan zan adding dinki a cikin group din ALQALAMI da yardar Allah,nagode da kika zabi Yar Mutan Kankia domin rubuta wannan labarin mai ban mamaki,dinbin darasi na rayuwa tabbas saidai ince ina maki fatan alkhairi Anty Amina kuma Allah yakawo maki mafita a cikin al'amuran ki."

"Ameen ya rabbi,saidai kece Anty na Yar Mutan Kankia."

Murmushi nayi sosai dan dagani Amina bata da girman kai macece mai saukin hali,ce mata nayi.

"Aaa ai a girme kin girmeni dole in girmamaki dan haka nidai kinzama yar uwata kuma Anty na fata Allah yasama rayuwar mu albarka."

"Ameen ya hayyu ya qayyum."

Cewar Amina Caranci.

da haka mukayita fira akan case din sannan mukayi lunch bayan ta gaisa da iyayena,nan narakata tahau mota ta tafi gida cikin aminci,kunji yanda mukayi da Amina Caranci wadda duk wannan labarin da zan rubuta maku akanta komai yafaru kudai ku kasance da ALQALAMIN Yar Mutan Kankia domin jin yanda takasance a cikin wannan labarin mai dibin darasi,son so nike maku son fisabilillahi,muje zuwa masoyana😘

Also Download: Gaba Gadi Complete by Jamila Umar Tanko

********na kasance nice babba a gidan mu daga wajen mahaifina har wajen mahaifiyata inda kannena guda biyar,tunda natashi gidan mu a cikin gata natashi a wajen iyayena saidai mahaifina ba wani shahararren mai kudi bane amman yana da rufun asiri domin duk wata dawainiyar mu yana mana ita dai dai karfin shi,sannan mahaifina yana sona kasancewar inada sunan mahaifiyar shi,tunda natashi Babana baitaba buguna ba ko ƙwaƙwaran faɗa mai tsayi saidai duk sanda zanyi laifi saidai yai mani nasiha dayake Babana mutunne marassan yawan hayaniya,ya kasance ma'abocin addinine,sannan yana cikin dattawan kirki a garinmu wanda duk wani abu da za'ayi na addini inbaizo na biyu yana cikin na ukku komai tareda shi akeyi,Babana su  shidda Mahaifin su ya haifa mace ɗaya maza biyu, dakin su ɗaya sai sauran ukkun matane suma ɗakin su ɗaya, dangin mahaifina basu kasance masu saka ido ba akan abinda bai shafe suba,kuma basu fiye yan ubanci ba sunada hadin kai kwarai da gaske saidai abinda ba arasaba amman muna respect  din junan mu,wannan shine kadan daga cikin tarihin yan uwan mahaifina.

Mahaifiya ta Khadija sunada yawa a cikin gidan su babban family ne mai zaman kanshi sunkai su arba'in a gidan su saidai masu rai su talatin ne dakai mahaifin su ya haifa,a dakin su Mamar mu tanada Yaya Anty Rukayya sai sauran kannen ta guda goma duk da ita da yayarta ya kama su goma sha biyu kenan,sunan kakata Sa'adatu macece mai hakuri juriya da kauda kai ga dukkan al'amura,sunan kakana Adam ya kasance mai yawan faɗa ne baida wasa ga ya'yan sa harda jikokin sa shiyasa kowa ke shakkar shi,dan duk girman ka ida kai mashi zai iya zuwa har gidan ka ya zaneka agaban ya'yan ka koda kuwa namiji ne wannan dalilin yasa kowa ke shayin haye masa saidai abin mamaki duk zafin kakan nawa wanda muke cema Baba bai hana yan ubanci da hassada ya wanzu a tsakanin tarin ya'yan nashi ba wanda ko kadan basu da hadin kai a tsakanin su kowa ɗan ɗakin su ya sani duk da ko a cikin yan dakin ma akwai wa'anda zakiga sunajin haushin junan su, da hassada ga yan uwan su wannan shine kadan daga cikin tarihin yan uwan mahaifiya wanda duk wannan labarin yanada tushe a cikin wannan family din duk abinda ke faruwa akwai gudunmuwar su.

******tunda Allah yasa nata shi agaban mahaifana nakai minzalin sawa a makaranta aka kaini Primary School a 1997 to 2003 nagama primary School dina na zana common and interest bayan wani lokaci jarabawar mu ta fito na samu addimission a G.G.P.S.S Kankia.

Akwai watarana da bazan taba mantawa da itaba lokacin bani lafiya ranar wata litinin ina kwance a tsakar gidan mu mahaifiyata nata hada mani kayan provision cikin akwaitin karfe wanda yake shake da kaya iri² nadaga Complex Sardine Gesher Carbin Madara Bomvita Sweet Chewgam Gari Kuli busassar shinkafa taliya kanzo Manga Mangyaɗa ƙuli dai dai sauran kayan ɗan makaranta duk mamata tana tayi mani shiri,haka ake hada mani provision dina,ba yaban kaiba ban tunanin a set dinmu ban tunanin akwai wadda takaini kayan abinci koma akwai saidai muzo tangan saboda iyayena suna hada mani provision nagani na faɗa,haka mamata ta kammala a hada mani komai a cikin akwatina sai murna nike zanje makarantar kwana duk da kuwa ba wani cikakkar lafiya ne dani ba ina fama da matsanancin zazzabi mahaifina ne ya shigo fuskar shi dauke da annuri ya dubi mahaifiyata dake kammala hada mani kayana yace........

"Maman Amina ya jikin Aminar da sauki ko yanzun naga malan Huzaifa zaikai yarsa makaranta harta shirya saidai ni mama na,bata lafiya Allah dai yabaki lfy,kema kitafi makaranta ."

"Ameen ya rabbi."

Cewar mahaifiya ta,niko tunda naima mahaifin nawa sannu da zuwa ban kuma cewa komai ba,cigaba da cewa yayi.

"Yanzun Asma'u zata tafi naga an fiddo da kayan ta za'ai mata rakiya kum.....

ai ban bari mahaifin nawa ya idasa maganar shi ba natashi tsaye kamar wadda aka tsikara duk wannan zazzabin da nikeji yatafi kamar bani ba dan naji ance yanzun aminiya ta Asma'u za'aikata boarding dayake duk makaranta ɗaya muka samu daman tun muna Primary ajinmu ɗaya nida Asma'u click dinmu mu shiddane sanda muke Primary School ni Asma'u,Maryam,FiddausiAisha sai Hauwa'u Mannir, shiyasa muka shaku da junan mu.

da kallan mamaki Baba yake bina kafin yai magana nace.

Aaa Baba na warke nima yau zanje boarding Allah na samu sauki.

Murmushi Babana yayi yana mamakin kalar kuruciya tawa cewa yayi.

"Haba Hajia ta kibari ki warke sosai sai inkaiki kinji."

Fafa naki amincewa saboda munyi alqawali nida Amina rana ɗaya zamuje boarding daman kuma makobciyar muce kusan gidan mu a hade yake,ba yanda mahaifina ya iya dole ya kyaleni shidaman ba mutun bane mai yawan magana ba haka halin shi yake,tashi nayi nashiga daki na saka uniform dina blue color coutin kasancewar ranar monday ne dayake mu uniform dinmu blue ne sai house ware dinmu na zaman hostel dayake mu haka muke cewa su kuma Pink color ne haka aka nagama shirina tsaf na dauki school bag dina  haka naita tsalle ina murna huɗuba sosai mama tai mani sannan muka tafi haka Babana yakaina G.G Kankia kusan atare akai kaini da Asma'u haka aka aje mana kaya bakin gate mukaje wajen Principal Hajia Rabi Bello,itace PC dinmu ta wannan lokacin koda mukaje anata yima New Entrance interview har aka zo kaina aka bani sentance na English Language na karanta sai 1234 zuwa hundred and ABCD  complete duk na karanta haka akakaini B Class nan Babana yai mani sallama amman ban damuba dan zai tafi yabarni lokacin ɗauki da zumudi na boarding ya sakani gaba ko zazzabin dake jikina banjin shi ko alama,Class mukatafi nan mukaita haduwa da kawayen mu wasu tun Primary mukasan junan mu,saidai nida Amina ba Class ɗaya aka ajemuba ita C class aka kaita,haka malamin mu ya shigo Class dinmu wanda ake kira AA Sadiq yazo yai mana wakar turanci saidai bazan iya kawota  a halin yanzun ba,sannan ya dinga tsokanar mu wai sanda zamuyi Candy anyi tashin alqiyama haka zamuyita kuka muna cewa mudai insha Allah sai mun gama baza'ayi tashin kiyama ba,haka rayuwa ta kasance mana a boarding school munata zumudinta a cikin zukatan mu,koda na kwana biyu haka na nemi wata Anty na mamata tabani wasika inkai mata,koda naje lokacin tana SS2 haka Anty Salma tayi murna da zuwana dayake da Maman ta da Mamata iyayen su maza uwarsu ɗaya uban su ɗaya,haka ta rikeni amana duk da kasancewar ina zaune a dakin mu *Hassun Yan Katsina* shine sunan ɗakin da akabani,amman hakan bai hanata yimani wanki ba harta bani ruwan wanka,tunda nike da Anty Salma bata taba zalinta taba kota cimani abincina ta rikeni kamar kanwarta wadda suka kwanta ciki ɗaya,haka ta daukeni.

Akwai wata ranar laraba tunda muka tashi da asuba mukayi sallar Asuba bamu koma ba daman haka mukeyi zamu shirya musaka uniform dinmu sanda gari zai fara haske haka kowa zai dauki tsintsiyar shi yaje yayi potion din da aka bashi dayake lokacin munada muguwar house captain mai suna Zainab Kabir  ta kasance azzaluma kuma macuciya batada tausayin na ƙasa da ita ko kadan musamman muda muke JSS1 amman bata raga manaba,ba wadda muke samun sauki a wajen sai gun Aisha Salisu ita kuma Prefect ce tana son mu tana kyautata mana lokacin har koya mana addu'oi takeyi da yake lokacin zafi waje muke fiddo katifun mu,muna kwanciya haka zata samu agaba tana mana fira da tatsuniya kowa ya shaku da Anty Aisha a cikin mu.

Haka rayuwa ta kasance kullin cikin wahala har mukazo duk wani zumudin boarding ya fita a cikin zukatan mu yanzun mun koma zaman hakuri mukeyi da yawa daga cikin mu haka zamuita kuka,muna kewar gida.

Yau takama Monday lokacin satin mu Ukku a cikin G.G tunda safe mukayi komai kamar yanda muka saba,sannan muka tafi Class sanda bakwai zatayi har munje aji,da yake mu duk safiya kafin muje Assembly sai munyi morning pref,haka Malan Bala Wada ke zuwa yana round Class by Class yana ganin yanda muke karatun mu,takwas dai dai muka tafi Assembly haka Pc dinmu Rabi Bello tazo mukayi prayers da national attem haka tagama yimana bayani akan maranta da kuma karatunmu muna gamawa mukayi national pledge sannan muka tafi Class haka aka gama mana lesson har zuwa lokacin da akayi Close na  School karfe 2pm akayi ringing muke wuce masallaci haka Baba mai jam'i malan Magaji yazo bisa keken shi yai mana sallar azuhur daganan muka dauki robobin mu irin na almajirai muka tafi dining muna ansowa da gudu muka wuto kanya wadda ke kusa da house din yan 2005 lokacin suna SS2 su ake ganama azaba kullin,haka mukaci abincin dining ko hadi babu sannan aka koramu potion Labour din lokacin   Hafsat Moh'd ake cemata kowa tsoronta yake tun daga SS2 har zuwa mu kananun kwari JS1 haka taita dukan SS2 dan bata da lokacin mu,haka suka bugu har sai sun baka tausayi wannan lokacin, rayuwar makaranta ba dadi sai kuka shine aikin mu kullin dan dai saukin mu,bamuda matsalar ruwa ko kadan Allah ya tsare mana,amman Malan Bala Wada shike kula da ruwan shanmu har zuwa karatun mu na Morning,Evening and Night shiyasa Malan Bala Wada ya zama favorite Teacher ga daliban G.G Kankia tun daga Yan iskan makaranta har zuwa ga salihai kowa na kaunar malan Bala Wada.

Yau ta kasance Lahadi ranar ce ake Visiting kuma watan mu ɗaya cir a cikin boarding murna da farin ciki bai boyuwa a fuskokin dalibai kowa na murna zaiga yan gidan su,haka muka gama gyara makaranta tas kwal sadda tara zatayi duty prefect sunyi kora kowa yayi fes dashi haka mukayi Visiting ground dan jiran tsammani na ganin yan gida.

Dayake mu akusa muke ba nisa shiyasa yan gidan mu sukazo mani visting karfe hudu na yamma tundaga bakin gatena hango kanwata Nusaiba da gudu nayi kanta natareta ina kukan dadi ban kaida sakin taba na hango mamata tashigo aiko nasaketa na rungume mama inata murna haka sauran kannena su Ahmad ba kadan naji dadi ba haka na dauki Hafsat itace autar mu,samu waje nayi  muka shinfida tabarma muka zauna haka kawayena su Asma'u Isma'il da Hassana Musa suka tayani kwaso kayana inda naima su mama shimfida haka akaita zuwa kawayena ana gaida mama sannan muka zuba abinci na Visting mukaci da fans dina kowa na murna,sai zuwa Visting akeyi haka student sukaita murnar ganin iyayen su musamman JS1 da ke kukan murna dan sun zata boarding dadi gareta ashe ba haka bane hakuri kawai ke cikin ta, tambayar Mamata nayi Babana cemani tayi yana gaidani basu sukabar makarantar muba sai wajen 6pm bada jimawa aka gama shigowa Visting lokacin dutyn mai gadin mune waishi Baiti,baida ragi balle ragowa ya tsare aikin shi bilhakki da gaskia muddin akasa doka bai yarda akaryata da haka aka gama Visting cikin aminci Yaya Salma ta daukar mani kayana bayan Mama ta bata nata kayan da kudi ba kadanba Mama taima ta godiya ba da haka muka wuce hostel wannan kenan.

{getButton} $icon={download} $text={Download Mp3}{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post