[Book] Amir Da Amira Complete Hausa Novel by Maman Nusibah

Amir Da Amira

Title: Amir Da Amira

Author: Maman Nusaibah

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Love Story

Doc Size: 684KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Tab, masu suna bai daya akwaisu da rikici. Ku dauka tare da sauke littafin Maman Nusaibah mai suna "Amir Da Amira" cpmplete hausa novel a text document. Ku saukeshi yanzu-yanzu.

Book Teaser: Gida ne babba wanda yake dauke da bangare uku ga yara nan suna wasa wata yarinya nagani an bigeta tana kuka  yaran  kowa yasoma guduwa suna shiga cikin gidan wanda ba yan gidan ba sun fita sunkoma gidan su

 dayan yarinya ce ta tsaya akan mai kukan tana cewa yarinya kadan ma kika gani indai nice dama nace miki duk uban daya hadani da yaya Safiyan ya dakeni saina rama kanshi ko ance miki namanta ne to ina sani nace dama sai munfito wasa na rama

 yarinyar  na kuka tace saina hadaki da mama na

wata mata ce ta  fito daga dayan bangaren tana fadin  ke  rashida wani dan iska ne ya tabaki agidan  nan mu fidda reni nida uwarshi

 wadda aka kira da rashida tana ganin mamanta tayo  wajan ta tana cewa mama ba ameera bace ta ke dukana wai dan jiya munje gonar mlm bukar mun ciro  mango shine yabiyomu  kuma itace tace muje mu ciro idan bamu ciroba zata mana wankan qaiqayi duk wanda baije ba

 mama ta banka wa ameera harara wadda ita kuwa ko ajikin ta mama tace yanzu ameera bazaki dena halin azzalumai ba na daukar maganar da kuke dauko mana kullin ana kawo mana karar ku musamman ma ke mai kunnen kashi

Ameera tace eh  din baza adena ba kuma ai hadda diyarki muke zuwa wllh ko gobe tayimin gami da yaya safiyan saina jibgi banza ehee tana jijjiga jiki ita ala dole wai an bata mata rai sai masifa takeyi kamar ba gobe

 Mama kuwa kama hannu Rashida tayi sukayi  sashen mama ameer   tana cigaba  da  masifa  

Ameer kuwa  nasashen  innar ta  ta  nufa  tana  zuwa  tayi  sallama 

 sai wata tsohuwa ta amsa tana cewa ke kuwa kedawa naji kina daga murya tace nida rashida da mamanta"  Inna tace to mai kika musu 

 ameera  tace inna wallahi saina ci aban rashida wai jiyane munje gonar bukar shesuka shiga suna cire mango shine daya biyomu sukace wai ni na sakasu kuma ni ko gonar ma banshiga ba tana matso kwallar karya tace shine suka hadani da yaya safiyan yayi  min duka da safe naje wajan umma gaisheta kawai yake dukana 

Inna ta saka salati tana cewa shi dan banzan yaron nan shine ya dakeki to wllh bai bigi banza ba saina rama miki dan iska mugu,   ita kuwa ameera tana murmushi tace kuma bakiga yadda yake dukana ba kamar wata yarshi 

Inna tace zaizo yasameni anan badai ke ya dakaba zonaga wajan ta matsa kusan inna tana cewa wllh jikina ciwo yake yi tana kukan karya,   Inna kuwa sai zuba masifa takeyi kamar ta aro baki.  (nace ashedai su ameera gado akayo)

 mama na shiga gida da isa wajan wata mata tace sadiya kiduba kiga yadda ameera ta yiwa Rashida gaskiya abin nan ya isheni haka dan tafi karfinta saitake zaneta kullin

 wadda aka kira da sadiya ta dago kai ta dubesu tace kiyi hakuri nana wllh kinsan ameera inna ce ke daure mata gindi agidan ko abbansu idan yayi magana inna ke rufeshi da fada nima kaina abun damuna yakeyi kullin addu'a nake mata Allah yashirye ta yarinya bata tsoron kowa kisan da cewa mutum daya take tsoro safiyan shima wani lokacin saita mishi mugunta

Maman rashida tace to shikenan amma kija mata kunne gaskiya tace to insha Allah,  suka juya suka fita

 Umma tayi tagumi tana tunani rashi ji irin na ameera yarinya kamar aljana babu wanda take ragamawa ita batasan ya zatayi da yarinya nan ba kodayake ai lefin inna ne ita ce bata ganin lefinta

 Tana nan abba yashigo da sallama amma yaji shuru ya sake wata nan ma shuru kawai saiya sayo kai ciki umma yagani zaune tayi tagumi da alama ta nisa cikin dogon tunani yazo yazauna akusa da ita duk batasan yazoba saida ya shafo fuskarta

 Ta zabura da sauri yayi saurin riketa yana cewa haba sadiya menene yasaka kike wannan tunani ? Umma taja numfashi tace abban safiyan wllh lamarin yarinyar nan ne yayi yawa kaduba kaga yadda take dauko mana magana a garin nan amma inna bata gani duk wanda ma yazo sai dai suyita fada dashi

Also Download: Mutum Da Duniyarsa Complete by Maman Nusibah

Abba yace kiyi hakuri umman yara mucigaba da mata addu'a insha Allah wata rana zata dena umma tace amin nan ta dauko mishi ruwa da abinci takawo mishi tace na hada maka ruwan wanka yana bayi

Abba yace to matata farin ciki na yana murmushi,  Umma dinma murmushin  tayi yazo ya rungumeta yamata  kissing  a kumatu tayi dariya tace oga ruwan fa zai huce 

 Ya saketa yana dariya yace ki fiddo min kayan dazan saka tace ai tuni na fiddo maka yana kan gado

 Ya fice bayi ita kuma ta zauna tana jiransa, 

 Safiyan ne yashigo gidan bangaren inna ya nufa yana shiga  banka mishi harara tayi  dariya   yayi  zuciyar sa yace to inna gidan masifa kennan yau kuma komai nayi ake min wannan harara haka yana maganar zuci,   yaji inna tace wato azzalumi ko uban me ameera tayimaka ka daketa inata magana ka wani ziramin ido kamar na uwarka da hanci kamar karass

 dariya yayi dan ya saba da wannan ba'ar ta inna yace hajiya inna ikon Allah kaka ta ni kadai , Ameera na kan cinyarta tace tab wllh bazan yadda ba ta soma tirje tirje a kasa tana cewa itafa kakar tace ita kadai bada kowa ba 

Inna tace butar uwaka safiyanu nace tashi kabar min gida ai nan ba gidan ahmadu bane da sadiya to tafiyar ka nace kazo kasaka min yarinya kuka

 Safiyan ya kama baki yace Allah yabaki hakuri masifatu,   Inna kuwa ta dauko wani filo akusanta ta jefa miki tace fice tin kafin na karya maka kafa

 yace kai kaji karfin hali irin na inna ni har zaki iya karyani sabon jini ne nifa kekuwa duk kin tsufa

 Inna tace uwarka sadiya ce ta tsufa baniba

 Ameera tace inna kyaleshi ai yasan kinfi karfinshi,   harara yamata ta koma bayan inna tana boyewa fita yayi  daga gidan yayi bangaren umma yashiga da sallama

 Suka amsa ya karaso yana cewa umma abba sunun ku da gida atare suka amma da yauwa ,, Umma tace har kadawo daga makarantar yace eh umma na amma Hajara fa da Ibrahim

 Umma tace basu zoba tukun nan daiko mai suka tsaya yi ne, Abba yace ai zasu dawo

 aikuwa basu rufe bakiba sai gasu sun shigo Ibrahim ne agaba yana kuka hajara na rike da jakar makarantar su umma tace a a lafiya kukashigo Ibrahim yana kuka

 hajara tace umma wllh kamal ne da Hanifa suka dakemu wai mufadama ubanda zai rama mana

 Umma tace to kuyi hakuri kunji wata rana sai labari, Abba yace kuje kucire kayan naku kizo kukai wa inna abincin su tace to

umma

 sukashige cikin daki suna fitowa saiga ameera tashigo da sallama tana cewa abba sannu dazuwa

 yace yauwa yar inna ya innar take tace lfy lau abinci mu nazo karba tana fada

 Su ibrahim suka fito daga dakin nan yawo wajan ta yana cewa anty ameera yau aka dakemu nida hajara

 Ameera ta janyo shi jikinta tana bubbuga bayansa tace wai wani dan iska ne ya tabamin kune wllh ko waye babansa saina yi masa b'alle b'alle

 Ibrahim yace kamal ne da haneefa  

Ameera tace  kai kai kai aikuwa basu daki banza ba dani suke zancen

 Umma da abba  da yaya safiyan sukayi kuri da ido suna kallon yadda  ameera take masifa

 Abba yace haba yar inna kiyi musu hakuri kila suma tsokanar su sukayi shiyasa suka dakesu

 Ameera tace haba  abba  ya za'ayi  a dakesu kuma kace wai na hakura gaskiya bazai yiyuba saina rama musu 

Umma tabige mata baki tace kiyima mutane shuru uwar neman rigima to karna ganki a hanyar gidansu ma

 aikuwa ta saki kuka tana ihu waiyo Allah bakina inna umma ta kasheni

 Abba yayi dariya yace kai wannan yarinya da neman rigima kike. yace mamana kiyi shuru mana ki dauki abincin ki tafi

 Ai kafin ya karasa inna tashigo tana cewa iyee lalle sadiya ai dama nasan kece zaki daketa ba kowa ba to Allah idan kika sake dukanta yanzu zanyi tsukiya muci danbe nidake dan baki isaba kike dukarmin yarinya tafada tana huci 

ita kuwa ameera tana ganin inna aikuwa ta kara sakin kuka tana rungume inna tace inna babu abinda na mata wai dan nace zan ramawa su Ibrahim dukansu da akayi shine ta dakeni

 Inna tace wai sadiya nace uwarki ta haifeta ne kokuwa a kasuwa aka siyota ne da kullin saikin daketa to bari kiji duka dai  saita rama musu dan basu isa ba suci bulus  ta kama hannun ta suka fita

 Washe gari tinda sassafe ameera ke shirin makaranta dan yau zata daukama kannanta fansar dukan da aka musu

 Inna tace ameera fito mana  ameera tace ganinan inna dan kwali dan daura ta fito 

Inna ta kama hab'a tace a a kinga kuwa yadda kikayi kyau

 Aikuwa ameera ta washe hakora tana dariya taji an yabeta tace inna ta to na tafi

Inna  tace nadawo lfy tana fitowa bangaren umma ta nufa nan suma su Ibrahim anshiryasu ta gaishe da umma da abba  da yaya safiyan nan suma suka gaishe da ita, ta kama hannu su suka fita 

Sauran  yaran bangaren suma suka fito da shirin makaranta nan suka fita daga gidan yaran suka isa makarantar su

 tukun Rashida da ameera da nafeesa suka isa nan malaminsu yazo suka gaishe shi nan aka fara koyarwa 

Ameera ce taga wani yaro yana kallon ta yana dariya dankuwa tasha kwalliya kamar aljana kuma kowa yasan halinta dan idan aka kama fada da ita bata barin bashi

 aikuwa ta aika mishi harara  mai nuni da zamu hadu anjima

 Ana  tashi ameera da kawarta khadija suna tafe suna hira 

Ameera tace kawata ki rakani yau mu casa wasu yara 

Khadija tace yauwa dama kwana biyu ban yi fada ba hannu na  har  kaikayi yakeyi mutafi amma suwaye

Ameera tace kamal da haneefa mana jiya suka kama min kannan suka zanesu nikuwa nace saina rama musu dan babu wanda ya isa ya dakar min yan uwa

 Khadija tace aikuwa sun taba bala'i dan bazamu raga musu ba

 can suka hangosu ita da kaninta sun tafiya aikuwa da sanda su ameera ke tafiya har suka  zo wajan su

 Carab sukaji an rikesu haneefa tace uban waye ameera tace ubankine nan suka bude musu idon aikuwa sukayi arba da ameera 

Haneefa da yake itama mafadaciya ce cikin fada tace lfy kuka taremu a hanya muna tafiyar.  Ameera tace maiyasa kuka dukar min yan uwa

 Haneefa tace su suka zagemu ,  aikuwa bata idar ba ameera ta bade mata ido da  kasa nan suka kama dukan ta kamar Allah ya aikota tana ihu tana cewa kiyi hakuri wllh bazan sake dukansu ba

 Aikuwa ameera tace batasan hakuri ba saida suka nada musu duka sosai dan har an fasama haneefa baki da hanci  kamal  kuwa marin da khadija ta wanke  masa   har hudu

 Shine ya gigitasa ya rasa inda zai nufa ya rike yar uwarsa suka tafi suna kuka 

wani dan  saurayine ya karaso wajan su ameera yace to iyayen fada

 Ameera tamai harara tace ina ruwanka sarkin iyayi

 yace ke wllh yanzu zan zaneki ,   Ameera da khadija suka tafa suna dariya    ameera tace kama isa saidai muzaneka wllh , khadija tace kai yanzu lado in banda abinka ina ruwanka damu banza jaki alade

 Aikuwa lado ya shaka yace nine jakin ?  tace eh din anfada jaki bata ida ba ya wanke ta da mari 

Aikuwa ameera ta dauko wani dutse tasamu bayansa ta buga mishi yasaki kara ya juya kan ameera

 Itama khadija ta dauki dutsen ta buga mishi a kugunsa aikuwa yaji zafi cikin fushi yace wllh saina karya ku yanzu nan yafada yana huci

 Da gudu  suka bar  wajan yana binsu dayake dukkansu basuda jiki aikuwa sukamishi nisa 

duk inda suka fuce suna ihu suna wai mahaukaci gashi nan zai kashemu taimako jama'a 

aikuwa duk inda sukabi indai akwai mutane  suma  mutanen rufa musu baya sukeyi kafin kace me tuni sun yaye mutanen layin kowa gudu yake yi nan suka yako kofar gidan mai gari.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post