[Book] Barauniyar Amarya Complete by Sadnaf

Barauniyar Amarya

Title: Barauniyar Amarya

Author: Sadnaf

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Fiction

Doc Size: 74KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuciya Sadnafmai suna "Barauniyar Amarya" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu complete dinsa.

Book Teaser: 'Yan mata ne a zaune a wani k'aton tsakar gida, sun sha k'unshi hannu da k'afa a k'alla za suyi goma sha, wata tsalleliya ce a tsakiyar su kyakyyawan gaske ko ba a fad'a ba da alama itace Amaryar, sakamakon k'unshinta ya fita daban da sauran 'yan matan sai tsokanar ta, suke tana murmushi, wasu dake zaune a can gefe da suma suke jiran layi yazo kansu ne suka fara gulma "Binta gaskia Amarya nan kyakyawa ce da alama bafullatana ce" cewar Amina "kijiki, ni kuma kallon 'yar shuwa Arab nake mata, baki ga gashin ta bane har gadon baya ba?"  "uhum kuma fa haka ne, dama su gayyace mu bikin ni ko photo ne muyi da ita".

    "rufa mana asiri a ina zasu gayyacemu kina ganinsu ma kin san hatimin nassara ya zauna," sallama da suka jiyo daga bakin k'ofa ne ya katse musu hirar da suke suka maida kallonsu bakin k'ofa, ciki kuwa harda Amarya da k'awayenta,wasu yanmata biyu ne suka shigo su biyu sanye suke da wani arnen less da kud'in su zai yi dubu sittin, kunensu sanye da tapka-tapkan d'an kunnen gold, haka ma hannunsu.

    Taku suke d'ai-d'ai har suka k'araso wajensu,tunda suka shigo Amarya kausar ta saki baki tana kallonsu, bawai kyaunsu ne ya tafi da imanin ta ba a'a k'iyasta irin dukiyar dake sanye a jikinsu takeyi, zama da d'aya daga cikinsu tayi a kusa da ita da daddad'an k'amshin daya ziyarci hancinta ne ya dawo da ita daga tunanin data tafi,yan matan hannun suka mimmik'awa k'awayen kausar sukayi musabiha suka mik'awa kausar hannu suka gaisa Inda suma suka kasa d'auke idansu daga kan kausar sabida ba k'aramin kyaunta suka  gani ba,Hanne mai k'unshi kuwa cikin rawar jiki ta fara gaishe su Dan tasan indai suka zo ko iya hannu tayi musu k'unshi dubu ashirin suke bata, da rawar murya tace "hajiya fareeda da fadeela gani nan zuwa  bari nayi sauri na k'arasa mata  gani nan zuwa" 

     Murmushi wacce aka cewa fareeda tayi tace "karki damu Hanne ki gama yi musu  a hannu kawai zaki mana" 

     "To ranki ya Dad'e bari nayi sauri nagama"

     Juya wa tayi ta kalli Amina da Binta dake zaune a gefe da  suka saki baki suna kallonsu fareeda tace musu "kuyi hak'uri gobe ku dawo sai na muku Dan yanzu Idan na gama yiwa wanan su hajiya zanyiwa kuma daga kansu nagama ta fad'i haka ne Dan tasan ba kud'in kirki suke biya ba Dan sai  ta gama musu k'unshi su had'a ta da D'ari biyar,tsaki Binta tayi tace 

Also Download: Budurwar Mijina Complete by Sadnaf

     "kya ce haka mana tunda kinga  masu kud'i sunzo"

     Amina da sauri ta tashi taja hannun Binta  suka bar wajen,fadeela kuwa wayarta ta Ciro a jakarta k'irar iPhone 7  ta ringa dannawa ko d'agowa ba tayi ba ballantana tasan mai ke faruwa,Amarya kausar kuwa tunda suka zauna ta fara raya abubuwa a ranta, hankalinta bai tashi ba sai  data ga wayar da fadeela ta ciro a jakarta, a ranta  tace turk'ashi mutanen da gani ba k'aramin masu kud'i bane "Allah ka bani sa'a" tace tana mai kallon jakar fareeda dake gefenta a ajiye, maganar Hanne ne yadawo da ita daga tunanin da take 

    "Hajiya  Ku matso na muku nagama" Hanne tace tana gyara inda zasu zauna.

     fadeela ce ta fara mik'ewa taje ta zauna Hanne ta fara mata minti goma da fara mata ta d'ago ta kalli k'awayen kausar tace dukan su zasu iya wankewa tunda ya bushe,mik'ewa suka fara yi d'aya bayan d'aya suna nufar bakin pampo dake tsakar gidan suna wankewa, hakan ne yabawa fareeda dama ta matsa kusa da yar uwarta Dan taga k'unshin da ake mata,hakan da kausar tagani ne yasa ta matsa kusa da jakar fareeda ta bud'e ba tare da kowa ya ganta ba ta zura hannu ta dauko rafar kud'i bata tsaya ganin kalarsu ba ta cusa a skirt d'inta tayi sauri ta matsa daga wajen duk abinda tayi a idon k'awarta Aminiyar ta Jameela tayi,girgiza kai Jameela tayi cikin takaici tana mai k'yamatar halin k'awarta,kausar kuwa mik'ewa tayi tace fitsari take ji ta nufi band'akin gidan da buta a hannu tana shiga band'akin tayi sauri ta zaro kud'in, waro ido tayi cikin mamaki data ga bandir d'in D'ari biyar-biyar ne tace "Alhamdulillah na samu kud'in dazan rage bashi" d'aga vest d'in jikin ta tayi tasa kud'in da yake vest d'in mai roba ne. tana fitowa daga band'akin wayar fareeda ya fara ringing, mik'ewa tayi ta d'auko Jakarta ta zura hannu Dan ta d'auki waya taga wayam dubu hamsin d'in data sa a jaka babu, salati tayi da k'arfi hankalin kowa ya koma kanta,k'arasawa tayi wajen fadeela tace "our money is missing"

waro ido fadeela tayi tace "how?" anan tace "an sace mana kud'i," "what" Fadeela tace tana mik'ewa,salati Hanne tayi tace "tabd'ijan anan d'in aka yi sata? wlh sai na chaje kowace yar iska" da gudu ta nufi k'ofa taje ta sa sakata.

DOWNLOAD BOOK


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post