[Book] Bongel Complete Hausa Novel by Zee Yabour

Bongel

Title: Bongel

Author: Zee Yabour

Category: Love Story

Doc Size: 196KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2019

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya Zee Yabour mai suna "Bongel" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: GGC KABOMO

Yara ne mata manya da k'anana duka sanye da uniform na makaranta, kowa da abunda yake yi, wasu na wasanni, wasu na cin abinci wanda ke nuni da lokaci ne na break, Yanayin yaran zai tabbatar maka iyayen su ba masu hali bane, makaranta ce ta gwamnati wacce ana jeka ka dawo kuma akwai b'angaren yan' kwana.

   Budurwa ce yar' kimanin shekaru 17 da haihuwa zaune a aji ita kad'ai, littafi a gabanta tana bitar karatu, "Bongel sarkin boko, wai bakya gajiya da karatu" Cewar Asiya da shigowar ta kenan, itama ba zata gaza shekaru 17 da haihuwa ba, Ta d'ago kai ta kalle ta tace "Hmm Asiya kenan, wannan shine matakin k'arshe na sakandire wanda ya kamata nayi k'ok'arin ganin na fita da sakamako mai kyau, haka karatun nan shine gatana, shi zanyi na taimaki iyayena, basu da buri da ya wuce ganin na samu ilimi mai zurfi, saboda shi na baro ahalina" Asiya ta jinjina kai da cewa "Allah ya bada nasara", "Amin" Ta amsa, ta juya ta cigaba da karatun, Asiya ta zauna kusa da ita, itama tana d'auko nata littafin.

   "Sannu Baffa, Allah ya tashi kafad'un ka" Dattijuwar mata wacce ba zata gaza shekaru arba'in ba ta fad'a da k'arasawa da hawaye, Wanda aka kira da Bappa kansa ya girgiza yace "Ko bayan raina kada a cire Bongel makaranta ita kad'ai Allah ya bani ikon sawa makaranta, Dan Allah ku cika mun burin nan nawa na ganin tayi ilimi mai zurfi", "Baffa In Shaa Allahu kana tare damu, zaka tashi ka cigaba da rayuwarka", Kansa ya girgiza ba tare da ya sake cewa komai ba,

  Bongel komai yau sukuku take yin sa, duty d'inta na ranar kawai tayi sa ne, ta fito hostel, Tun shigarta aji bata cewa kowa komai ba, dama ita ba gwanar surutu ba ce, sai dai shirun yau yasha bambam dana kallo, Ta rasa dalilin da yasa bata jin dad'in ranta, ga gabanta dake yawan fad'uwa

   "Hafsat Aliyu" Taji muryar Vice principal d'insu na kiranta, Ta amsa da mik'ewa, "Zo" Ya fad'a yana yin gaba, ta biyo bayansa har zuwa admin, Hamma Bala ta tarar a zaune ofishin vice principal, "Hamma ina wuni?" Ta gaishe sa cikin sanyin murya, "Lafiya lau" Ya amsa murya a raunane wanda daga yanayin sa ya tabbatar mata zuwan nasa ba na lafiya bane, Rubutu VC d'in yayi a takardar ya mik'awa Hamma Bala, Ya juya kan Bongel "Idan akwai abunda zaki buk'ata a gida, kije ki d'auko zaku je gida", "Gida" Ta nanata a ranta, yayin da k'irjinta ya doka, ko shakka babu ba lafiya ba, tsawon shekarun da tayi a makaranta tun js1 ba'a tab'a zuwa d'aukarta ba, biki ko suna Bappa baya bari saboda yadda ya d'auki karatun ta da muhimmanci, "Bana buk'atar komai" Ta fad'a dan a halin yanzu burinta ta ganta a gida dan sanin meke faruwa,

   Babur na Hamma Bala ta hau, yaja su zuwa malumfashi kasancewar babu nisa, Taron mutanen data gani a k'ofar gidansu, yasa jikinta tsinkewa, ko shakka babu mutuwa ce, wani daga cikin yan' gidansu ya rasu, Tana dosar k'ofar shiga ta fara jiyo koke koke, jikinta ya soma rawa da k'yar ta rab'a mutane ta shiga ciki, idonta ne ya sauka kan mahaifiyarta wacce ke faman zubar da hawaye, da gudu ta k'arasa kusa da ita ta fad'a jikinta, 

  "Mun rasa Bappa Bongel Allah ya k..." Bata k'arasa ba sakamakon sumar Bongel, mutane sukayo kanta ana yayyafa mata ruwa, A hankali ta bud'e idonta tace "Nene Dan Allah kice mun mafarki nake bamu rasa Bappa ba", Hawayen data gani shimfid'e kan fuskar Nene ya k'ara tabbatar mata gaskiya ne,

  "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Take nanatawa idonta a runtse, hawaye na ambaliya saman fuskarta, mutanen da ke wurin ta basu tausayi matuk'a sanin irin shak'uwar dake tsakanin ta da Bappa.

  Ta jima zaune a wurin tana zubar hawaye, kiran sallar la'asar yasa kowa mik'ewa zuwa gaida ubangiji, Bongel ta d'ago rinannun idonta da suka koma jajir saboda kuka suka sauka kan Dije da Fatsuma wanda suke cin tuwo hankali kwance babu d'igon hawaye a kan fuskar su, Kanta ta kawar gefe cike da takaicin su, bata d'auka rashin imanin su ya kai haka ba, Alwala tayi a famfon dake tsakar gida ta shiga d'akin Nene, ta dad'e tana addu'o'i,

  "Adda! Adda!" Ta d'ago tana kallon k'anwarta Ramla yarinya yar' kimanin shekara 14, hannun ta rik'e da k'aramin k'anensu dan' shekara hud'u, "Adda Bappa ya tafi ya barmu" Ramla ta fad'a tana fashewa da kuka, ta fad'a jikin Bongel, K'aramin k'aninsu Abu shima ya fad'a jikin Bongel, ta k'ank'anme su jikinta, suna kuka mai tsuma zuciya.

  Goggo Hajjo wacce k'anwar Nene ce ta dad'e tsaye a d'akin tana kallonsu cike da tsantsar tausayi, Kafin ta nisa tace "Haba Bongel kece babba cikin su, ke da ya kamata ki lallashe su kin sasu gaba kuna kuka, Bappa addu'ar ku yake buk'ata ba kuka ba, nasan da ciwo amma haka zaku jure, mutuwa na kan kowa",

  Muryarta da k'yar take fita ta dishe tsabar kuka tace "Ashe haka mutuwa take da d'aci da rad'ad'i, mun rasa Bappa Goggo dole muyi kuka", Kusa dasu ta duk'a ta kamo hannun Bongel da Ramla ta soma lallashin su tare da musu nasiha, a hankali sukaji natsuwa na saukar musu sun tsagaita da kukan.

   Da zazzab'i Bongel ta kwanta, ana cewa bacci b'arawo sam bai sace ta ba a daren ranar, Ramla da Abu sun samu yin bacci, Nene itama haka ta kwana lazimi tana rok'arwa Bappa rahamar ubangiji.

   Kwana uku ana zaman makoki, kowacce rana da irin halayyar dasu Dije ke nunawa, har mutane sun fuskanci basu damu da mutuwar ba, haka kowa ke tafiya dasu a baki.

  "Na sha jin labarin facaloli amma ban tab'a ganin kishin matan sauri irin naku ba" Cewar Hajjo, Nene ta numfasa tace "Nasu dai, ni kaina abun yana matuk'ar bani mamaki da d'aure kai, ban k'ara tsinkewa da lamarin su ba sai rasuwar nan", "Ni kaina na k'ara shaida Dije da Fatsuma basa sonki kuma bana jin zasu tab'a sonki", Nene tayi murmushin takaici tana girgiza kai, Bongel shiru tayi tana k'ara nazarin rayuwa irin ta ahalin su, yadda ake gudanar da masifaffan kishi tsakanin matan gidan, su ba kishiyoyi amma har sun fi kishiyoyi kishi.

   Bongel da Ramla suna zaune kan tabarma dake shimfid'e a d'akin, Nene na zaune kan katifa ta jingina da bango, Abu yayi matashi da cinyoyin ta, kowannensu yayi shiru yana sak'ar zuciya, yayin da d'imbin kewar Bappa ta zagaye zukatan su, a irin wannan lokacin sukan zauna suna hira, cike da nishad'i.

   Nene ta dubi Bongel tace "Gobe ya kamata ki koma makaranta", "Gobe Nene ko sadakar bakwai fah ba'a yi ba", "Jiran me zaki tsaya Bongel, kina matakin k'arshe na kammalawa, kada kiyi wasa da karatun ki, Bappa bai bar wasiyyar komai ba sai na karatun ki, yana da burin kiyi ilimi mai zurfi, Dan Allah ki cika masa burin sa", A raunane ta d'aga kai tare da cewa "In Shaa Allah zanyi k'ok'arin cikawa Bappa burin sa, haka zaku yi alfahari dani", "Allah ya yarda" Cewar Nene, Dukkansu suka amsa da "Amin"

   Washegari Hamma Bala ya mayar da ita makaranta, ta koma da k'udurin k'ara zage dantse wurin ganin ta cika burin Bappa, da son ganin ta taimaki mahaifiyarta da k'annen ta, Asiya tayi murna sosai ganin Bongel ta dawo, itace aminiyarta rashin ta kwana biyu yasa tayi kewarta sosai, Ta mata gaisuwar Bappa, kuma tace ana yin hutu ita da yan' gidansu zasu je yi ma Nene gaisuwa.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post