[Book] Burin Raina Complete Hausa Novel by Serheeberh

Burin Raina

Title: Burin Raina

Author: Serheeberh

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Love Story

Doc Size: 254KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuciya Serheeberh mai suna "Burin Raina" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu cikin sauki.

Book Teaser: Zaune nake akan dan karamin turmin dake girke a tsakar gidan mu ina yiwa Mamanmu tsifar kai, ina gamawa na hau yarfa mata kananan kitso daya kwashemu fiye da awa daya kasantuwar Mama mai yawan gashi ce da kuma tsawo ma. Ina gamawa ta mike ta shiga wanka, ni kuma na dauki tsintsiya na shiga sharar tsakar gida. Kafin ta fito daga wanka dai har na share mata daki tare da kunna turaren wuta na kuma fesa air freshener. Na sallaci la'asar data riskeni ina shara, wanka nayi a gurguje na suri jaka na tafi islamiyah.

Wajen karfe shida na yamma na dawo na tarda girkin dare na jirana, duk da a tsakar gidan na tadda yayata Iftihal ita da Mamar suna hira amma ko wuta ba wanda ya hada min. Dama dai nayi zaton haka, na dae san da Mama Amina tana nan da zata dora min ko ruwan zafi ne. Allah ya taimakeni itacen busasshe ne dan haka nan da nan na dauko twist macaroni na hau dahuwa, ina saukewa na juye a cikin kula babba na kai dakin Mama.

Karan da waya ta tayi ne da misalin takwas da rabi na daren ranar ya sanar dani zuwan Gwarzon zuciyata Yaya Mujahid, dan gidan kanin babanmu ne. Daki na shiga na dauko hijabi na dake bisa abin sallah na fito na durkusa a gaban mama na ce "Mama zan fita, Yah Mujahid ke kira na..." Bata tanka ba sai wani tsaki daya subuce a fatar bakinta, jiki a sanyaye na mike, ina jiyota tana mitar "....aikin banza! Mutum baya tsinana maka tsiyar komi amma kai kullum ckn rawar jiki a kansa? Shi ko en kudin hirar nan baya bayarwa amma shegiyar yarinya ta like mashi, tsuutttt!!" Taja tsaki. Na danyi murmushi kawai, na rasa duk da na saba jin fiye ma da irin wadannan maganganun amma zuciyana kanyi kuna a duk sanda naji furutan Mama ga Yah Mujahid.

Ni ban ga aibun Yah Mujahid ba, matashi ne mai jini a jika, kyakkywan gaye dashi fari tass ga kwarjini son kowa dai kin wanda ya rasa. Ga sana'ar shi ta kanikanci kuma yana samu dai dai gwargwado, yana kuma min hidima bakin iyawarsa amma Mama da er uwata ba sa ga ni. Hakan kuma bai hana idan ya kawo min kayan bukata irinsu kayan kwalliya, na makulashe ko na sakawa su amshe su rigani amfana dasu ba, sau tari ma sai sun zabe kayan sannan su bani sauran, haka kuma zan amsa don bani da yadda zanyi dasu, kunji fa keta da halin dan adam!.

Mahaifina Malam Ibraheem Dauda mai kayan miya, sana'arshi kenan sayar da kayan miya tun yana matashi. Allah yayi mai nasibi da ita, da ita ya dogara kuma da ita ya auri mahaifiyata Zainaba wadda auren hadi ne aka musu, sai dai har suka samu fiye da shekara uku Zainabu ko batan wata bata taba yi ba. Malam Ibrahim ya sake auro wata Zawara Badiyya, ita din ma sai da ta shekara sannan Allah ya bata ciki. Mahaifi na da Mahaifiyata sunyi farin ciki sosai da samun cikin Badiyya, musamman daya kasance zama suke na lumana da zaman lafiya duk da wasu halaye da Badiyar take dashi na rainuwa. Su ukun suka dinga rainon cikin har Badiya ta haifo danta yaci suna Labaran, bayan shekara biyu ta sake haifo Iftihal.

Kwatsam! Sai ga Zaynaba da ciki, kada kaso kaga yadda bayin Allahn nan suka nuna farin cikinsu, musamman ita Zaynaba da take ganin wannan cikin shi kadai ne danginta, iyayenta kadai ta sani tun tasowarta, suma kuma Allah yayi musu rasuwa tun bata jima da yin aure ba, don haka take ta dokin haihuwarta. Gashi cikin ba karamin wahala yake bata ba, a haka dai take rainon cikin. Ranar nan ta tashi da matsananciyar nakudar data dauketa fiye da kwana uku har asibiti suka yanke shawarar yi mata tiyata. Cikin ikon Allah kafin a gama hada kayan aiki ta sullubo kyakkyawar yarinyarta, sai dai jini ne ya tsinke mata bayan nan, kafin a shawo kan matsalar tace ga garinku nan! Kwatanta halin da mijinta ya shiga dalilin mutuwarta abin baya faduwa, yayi kukan rashin mace ta gari wadda bata taba saba umarnin shi ba. Badiya kam har da suma, dmn ta dauki Zaynaba ne kamar er uwa ba wai kishiya ba. Bayan ta farfado take tasa aka nemo mata kaikayi ta sha tayi wanka, ruwan nono na kawo mata ta dauki jaririyar nan ta fara shayar da ita. 

Sanda Mal. Ibrahim ya ga wannan karramawa ta Badiya har sai da yayi kukan farin ciki, yayi ta shi mata albarka.

Shekara daya ta wata uku ta dauka tana shayar da jaririyar da taci sunan Ummul-Khairi, kafin ta kara samun wani cikin ta yaye ni. Nan ta sake haifo danta yaci sunan Mubarak.

A haka rayuwarmu ta taso, ckn tattali da kulawar iyayenmu har muka yi wayo aka saka su Yaya Labaran da anti Iftihal makaranta, sai dai sam basu son makarantar kuma basu cika zuwa ba, idan kuma Abba yana yi masu fada game da hakan sai Mama ta bi bayansu kasancewarta mace mai son yaya wadda bata so a ga laifinsu, sbd haka ne suke yin duk abnd suka ga dama babu wanda ya isa ya tanka musu.

A ckn haka ne Abba ya sake auro wata bazawara anan bayan layinmu, Mama ta tayar da hankalinta sosai a farkon abin, amma daga baya da ta fahimci halin amaryar sai ta kwantar da hankalinta suke zaman lafiya. Sunanta Amina, macece mai hakuri, kawaici, da kauda kai a harkar da babu ruwanta, ta tare da er karamar diyarta mai kimanin shekara guda, Saudatu. Ta dai sha hakuri da mama da 'ya'yanta musamman Yaya Labaran da Iftihal sbd yara ne marasa kunya da girmama na gaba dasu don shi kanshi Abba ba kasafai suka cika tsoronshi ba. Ita kuma Mama macece mai shegen Wa ido, ga kin ganin laifin 'ya'ya komi suka yi dai dai ne a wajenta, gata da shegen rainuwa da son abin duniya. Abba ya sha kawo cefane na ji tana mitar sunyi kadan ita ya zata yi ta kacaccala su? Haka idan ya kawo sutura tayi ta mitan kananan atamfofi ne waye da waye har sai ka gaji da sauraro.

DOWNLOAD BOOK

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post