[Book] Canjin Rayuwa 1, 2, 3 & 4 Complete by Halima K/mashi

Canjin Rayuwa

Title: Canjin Rayuwa 1, 2, 3 & 4

Author: Halima K/Mashi

Category: Fiction

Doc Size: 1MB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2018

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya Halima K/mashi mai suna "Canjij Rayuwa Book 1, 2, 3 & 4" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: Hajiya saudat tana zaune kan sallayarta ta idar da sallar azahar tana istigfari, 'yar kimanin shekaru arba'in da bakwai zuwa da takwas,amma ba ta yi kama da shekarunta ba saboda kyan jikinta da kuma hutu.

In an ce ka fadi shekarunta za ka iya cewa talatin da doriya,kyakyawa ce mai cikar mutunci. wayarta da ke gefe samfurin nokia tayi ruri, cikin natsuwa ta kai hannu ta dauka tare da kallon fuskar wayar.

Kamar yadda ta za ta, maigidan ne domin duk yinin yau ba ta samu kiransa ba.sallama ya yi,ta amsa cikin ladabi, sunanta ya kira ya ce,hajiya ki karbi bakuncin mu anjima. 

Cikin taushin murya tace,shine ba ka fada mini ba tun safe? cikin lallashi ya ce,na yi ta neman layin ki bai samu ba, ta ce,da ka nemi ta su usaina,kila network ne domin waya ta kunne ta ke,ya dan murmusa,ba mamaki zan iso da yunwa fa,don haka a tarbe ni,ta yi 'yar dariya,wace irin yunwa?shi ma yayi 'yar dariyarsu ta manya,duk wata yunwa ta,da ita zan zo,ta ce, kar ka damu allah ya kawo ka lafiya,ya ce,amin.                                    

Ki sa a yi wa uwata farfesun kifi tare za mu zo,take ta hade fuska, tamkar yana kallon ta,ta ce alhaji don allah kar ka zo min da mimi.

Ya ce,saboda me?ta ce,ka san komai, alhaji MIMI in ta zo gidan ba,ba maaikatan gidan ba.ta sani,na fada mata kar in sake ganinta a gidana matsawar ba ta canza halin ta ba,ba na bukatar ta.yayi shiru domin ranshi ya baci,kusan minti daya duk sun yi shiru.  

Sannan ya ce,sauda, ba zan gaji da fada miki cewa ban jin dadin abinda kike yi wa MIMI ba gaskiya, zai fi kyau ki fito fili ki zage ni sai ya fi min sauki maimakon aibanta MIMI. 

Allah! in ji hajiya saudatu,ta sake tausasa muryarta,ban san lokacin da za ka fahimce ni ba alhaji,amma kayi hakuri in dai don mu zaka zo,to ka zo kai daya zan fi so haka.cikin dan zafi ya ce,sauda muna hanya kar ki manta da abincin ta na yau da kullum,ki fada ma duk 'yan gidan wanda bai son ganin ta zai iya barin gida har sai ta tafi.

Sannan ya kashe wayarsa, ta dan ciji lebe tare da lumshe ido cikin takaici,ba ta da zabin da ya wuce yin abinda mijin ta ke so a fili ta ce ni kan bana son zaman MIMI garin nan,na tsani halin ta,a ce yarinya karama a bar ta tana yin yadda ta ke so.ta mike tana nunke sallaya.         

Abdulkarim ya yi sallama, ta amsa fuskar ta daure,sannan ta yi tsaki, abdulkarim ya ce,lafiya hajiya?alhaji ne ya kira ni wai suna tafe shi da MIMI. abdulkarim ya ja tsaki,don jin ambaci sunan MIMI, sannan yace,ashe yanzu zan juya a kan sawuna mu gaisa kawai hajiya in sabi jaka ta,ai a wannan sati bani da darasi kamar yau,sai na sake dawo wa. 

Hajiya sauda ta yi yar dariya tare da fadin haba abdul,ka taho tun daga zariya har katsina sannan ka ce mu gaisa kawai ka wuce saboda MIMI?ta ci gaba da fadin ba zai yiwu ba.dauki jakarka kawai ka wuce sashin ku,ka watsa ruwa.barin in sa mutuniyarka tabawa ta kawo maka abinci na san yanzu sun gama na rana.ya ce,ai ni bana son rainin wayonta ne hajiya,a ce yarinya karama kanwar bayanka ta zo tana kawo maka rainin wayo,ba dama ka yi magana.ni kuma kin sanni da zuciya sai in doke ta. hajiya tace,aa kar ka soma,ka san halin alhaji.ina fatan baka manta da yadda yayanka abbas suka kwashe ba,in ka tuna zungure mata kai kurum yayi,amma ta inda alhaji yake shiga bata nan yake fita ba.

Tsawon wata shida yaki ams gaisuwar abbas sai da biki shi sannan alhaji ya sauko,shima sai da abokan abbas suka taro abokan alhajin aka hadu ana taba shi baki, sannan ya hakura da kyar da dokoki a kan 'yarsa.      

Abdulkarim yayi ajiyar zuciya cikin takaici, sannan ya ce, van manta ba hajiya shi yasa nace, zan koma, tace ka hakura da harkanta.yace, gaskiya alhaji ba yayi mana adalci,a ce cikin 'ya'yansa mu ishirin da biyu,amma ya zabi daya rak yace,ita ce star don kawai tana da sunan mahaifiyarsa.allah hajiya abin yana damu na, kanwarmu ce fa,amma ko shawara da ita sai abinda ta ce a family.                   

Hajiya sauda ta ce,ku yi ta hakuri.

Dadin abin ita dai ta mace ce,duk abinta ai dole ta yi aure ko? abdulkarim ya ce, tabdi, wannan 'yar jin kan?ya zauna a kujera, sannan ya ce,allah ya sa ta saurari wani hajiya ta ce, ayya abdulkarim dole tayi aure. 

Ba dai mace ba ce?shi kanshi zai so a bar masa ita a gabansa?abdul' ya yi 'yar dariya,sannan yace,kila ya ce mijin ya dinga biyo ta nan gidansa.hajiya ta ce, oho mishi su dai suka sani, suka yi 'yar dariya, ta ce ba su lokaci kawai.ni dai ina ta fada ma allah, ku da ma na haifa ciki daya kuna jin takaici da haushinta, bare wadanda ba ni ce na haife su ba.abdul ya mike tare da saba jakarsa, bari ni kan na isa dakinmu, hajiya ta ce, to ni ma bari in je babban kicin.

Hajiya sauda ta tafi gefen babban kicin,ka san cewar gidan babban gida ne mai tsari,tun daga waje za ka san cewa mamallakin gidan ya tara abin duniya ba kadan ba ta isa babban kicin din,mata uku ta samu a ciki suna ta aiki,suka maido da hankalinsu gurinta tare da yin mata sannu da shigowa, ta amsa da sannunku da aiki cikin girmamawa, ta kalli tsohuwar cikinsu ta ce,baba tabawa me aka yi da rana?tsohuwar tace,taliya ce ke kan layi da rana,da dare kuma zamu yi tuwon masara da miyar danye kubewa,ga taliyar nan ma yanzu na sauke.     

Hajiya tace to,a canza na dare a yi mana dan waken gari dawa sannan ayi shi da wuri.baba tabawa tace,maigida yana nan shigowa kenan?hajiya tace eh,suna tafe,suka hada baki guri cewa,allah ya kawo su lafiya.

Hajiya tace amin sannan ta kalli jummai muna da kifin ruwa ko?jummai ta ce eh,hajiya ta ce yawwa ki dafa kadan kar ki cika yaji kuma kar ki sa tafannuwa.

Sannan ki kula kar ya dagargaje na MIMI ne dukkan su suka hada baki gurin tambayar har da MIMI ne za a zo?jummai ta ce, allah ya fishe ni yin kuskure. hajiya tace kar ki damu, sannan abinda kawai zan fada maku in tazo,ku kawar da kai duk abinda za tayi kun ji ko?cikin karyayyar murya suka ce to shikenan,tabawa ta kalli jummai kar ki sa mata tafannuwa.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book 1}

{getButton} $icon={download} $text={Download Book 2}

{getButton} $icon={download} $text={Download Book 3}

{getButton} $icon={download} $text={Download Book 4}


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post