[Book] Dan Mace Complete Hausa Novel by Hawwa Muhd Usman

Dan Mace

Title: Dan Mace

Author: Hawwa Muhd Usman

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Fiction

Doc Size: 1.2MB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2020

Description: Sauke littafin marubuciya Hawwa Muhd Usman mai suna "Dan Mace" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu cikin sauki.

Book Teaser: Tunda ta zauna a gurin ta yi wani irin shiru mai shiga zuciya,bata sake k'ok'arin motsawa ba bare ayi tunanin tana raye.? Ta suma.? Ko kuwa mutuwa tayi.? Duka dai ga tanan ne sunkuye da kanta dake kife a tsakanin cinyoyinta,,yanayin yadda tayi she looks so restless and disturbed,wanda da kyakykyawan kallon tsanaki guda zai yi saurin sawa mutum ya fahimci yanayinta yafi kama da na mutumin dake cikin tsanani,kamar yadda both hannaye da k'afafunta dake d'aure cikin sasarin k'arfen suka yi indication,,and kuma yanayi da tsarin gurin da take ko kad'an bai yi kama da torture room ba,bare a kira shi da prison ko guardrooms.

   Tsarin gurin ya kasance babu wani hayaniya,d'aki ne guda yalwatacce da bai had'a ko wane irin tarkace ba,,ita kad'ai ce zaune cikin d'akin da girmansa ak'alla zai tasamma kaiwa 30 square meters,daya kasance yana d'auke da wani irin tsohon traditional iron bed wanda hausawa kewa lak'abi da mahadi ka ture (wato dai irin hausar nan da ake nufin kafin aga bayan abu za'a d'auki tsayin zamani),then midi wooden table da kujera da suke gefe and long cutains masu sauk'in haske da suka zagaye duka windows da entrance na d'akin,,,ta d'auki tsayin lokaci a sunkuyen ba tare data d'ago ba,sannan kuma bata koma ta kwanta ba,gashin kanta daya baje ya sauka jikinta ya sake taimakawa wajen rufe ilahirin halittar fuskarta,da duk iya nacin mai naci da son bin kwakwaf akanta,zai yi wahala ya iya gano wace irin halitta ce farat d'aya,yarinya.?,Budurwa.?,Tsohuwa.?,Matar aure.? Ko kuma bazawara..?

***

      Tafe yake cikin wani irin taku mai tattare da nutsuwa,tun da ya shigo cikin gidan fuskarsa ke sunkuye tana kallon k'asa,,sai dai a yanayin tsarin yadda yake tafiyar zai yi saurin sawa a kirashi da kamilalle,bcos yadda yake yi d'in tuni ya fallasa asalin nutsuwarsa  da zata sa ayi saurin kiransa nutsatstse da yake bin komai na rayuwarsa a sannu,,a zahiri shekarunsa duka baza su haura 24 ba,sai dai da yake ya kasance ma'abocin ginannen jiki da duk wani siffar k'arfi na kasantuwarsa d'a namiji mai ji da shekarun yarintarsa suka bayyana kansu ta cikin fasion summer with hooded sleeveless d'in da yake sanye da ita,ta sake fallasa asirin girman jikin nasa da ka iya sawa a kirashi da mutumin da ya tasamma shekaru talatin a duniya,,tun daya shigo bai yi k'ok'arin d'agowa ba,hasalima sai sake janyo hooded d'in dake rufe da sumar kansa yake,wisely and time2time sai ya d'an lek'o ta side yana sake monitoring hanyarsa,sannu a hankali har ya wuce harabar gidan ya iso cikin d'akin da take,,y'an kalle² yayi lokacin da ya shigo,ko da ya tabbatar babu kowa direct ya nufi inda matar take zaune ya k'araso kusa da ita,slowly ya d'ora hannunsa a saman shoulder d'inta,muryarsa na wani irin trembling bayan ya janye hood d'in yana kallonta da fuskar damuwa yace

     *"LOLLY..!* Kiyi hak'uri ki fad'a min yanzun.. Please..!?"

   Shiru tayi bata d'ago ba har sannan,da wani irin muryar tausayi ya sake dafata yace

   "Please lolly..! U have to take a look at me,always fa am growing older,why ne ba zaki sanar da ni ba..?? Why.?"

      Shiru ta sake yi bata d'ago ba still kuma bata amsa tambayar da yake mata ba,shima d'in still ya sake yi mata duk muryarsa ya koma kamar zai yi kuka saboda k'in kulawa da maganarsa da tayi,a hankali ya janye hannunsa a jikinta ya juya mata baya,yana kallon wani side d'in yace.

   "Lolly..! U know ko wane lokaci saina tambayeki inda Daddy na yake,waye shi? Ina zan ganshi.? But always sai dai kiyi min shiru al'halin nasan kina jina,i know kin san abunda nake nufi,kuma kin san abunda nake buk'atar ji kenan daga gare ki,why don't u informed..!? Kin fi so ko wane lokaci naci gaba da rayuwa da bak'in cikin kira na *MARA ASALI..??* Ina son sanin inda mahaifina yake,na nemo shi,na rungume shi,a karon farko,a lokaci guda naji nima na zama d'aya daga cikin y'ay'a masu asali da gata,,tabbas zanyi alfahari da hakan,a duk ranar da nasan wane ne mahaifina zan kasance mai farin ciki..!"

    Dakatawa yayi kad'an yana jan numfashi,idanunsa a d'an kulle amma tsananin damuwa ke sake appearing masa a saman kyakykyawar fuskarsa mai d'auke da matsaikacin haske,madaidaitan idanu,pointed noise,dim beard nd small rounded mouth mai d'auke da wasu irin soft lips masu jan hankali,,still matar tana a yadda take ba tare da tayi ko gezau ba bare yasa ran zata amsa shi,da yaga bazata kula ba cikin fushi² da a ko wane lokaci ya tambayeta tak'i amsa masa suke k'arewa babu dad'i ya juyo yana kallonta idanunsa d'auke da wasu irin hawayen takaici yace

    "It's ok Lolly! Its ok.!! Tunda har bakya so na sani,,,i promised to my self nd u too,as from today till my last breathe i won't ask u,,ever..!"

    A fusace ya juya zai fita a d'akin zuciyarsa da ransa duk a mugun b'ace ya ganta tsaye tana kallonsu ta hard'e hannaye a k'irji fuskarta d'auke da damuwa,haka idanunta banda tsantsar tausayawa mai girma babu abunda suke bayyanarwa,jikinsa yayi mugun sanyi bcos yasan ta hana shi zuwa gurinta shi kad'ai da irin wad'annan tambayoyin,duk da yaji fad'uwar gaba lokacin da ya ganta tsayen,but hakan bai hana shi sunkuyar da kansa k'asa ba,slowly kamar wanda tafiya kewa wahala yaci gaba da takawa har ya k'araso gefenta yana niyyar rab'awa ya fice,,ita kanta ko da take tsayen tana kallonsu tun bayan da taga shigowarsa gidan bata iya ce da shi komai ba still tana kallonsa yana tafe yana matse idanunsa,har lokacin da yayi shirin fita ya bar musu d'akin,sannan tayi k'arfin halin rik'o hannunsa,waiwayowa yayi saurin yi yana kallonta a lokaci guda hawayensa suka samu damar fara sauka saman kyakykyawar fuskarsa,yadda yake jin zuciyarsa damuwar da yake ciki a yanzun na rashin hope ya wuce yace zai iya had'iyeta a cikinsa,dole ya bawa hawayensa damar sauka ko zai samu sassauci

    *"NURAZ..!* Habibiiy.! Kada kayi kuka,kada kayi Yarona..! Idan ina ganin hawayenka suna k'ona ni,,bana iya jurewa ganinka ko wane lokaci kana kuka,,shin har tsayin wane zamani zanyi ta ganinka a haka..? Bazan iya jura ba,,ka kwantar da hankalinka yarona,in sha Allah ni kuma a yau nayi *ALK'AWARI* zan sanar da kai *ASALIN KA!* Labarin ka da mahaifiyarka tare da duk k'alubalen da muka fuskanta,na amince yau zan fad'a maka..!"

     Tun kafin yayi magana suka ji ta fasa wani irin razanannen ihu da dole yasa su duka biyun juyawa suka kalleta fuskokinsu bayyane da damuwa,,Nuraz da jin ihunta da yanayinta daya sauya lokaci guda babu shiri yayi saurin matsawa bayan d'aya matar yana fad'in

   "Annie..! Ki ce ta bari bana so.. Pleasee.. Am scared,,tana min irin kallon nan zan dunga jin tsoro,kuma zan daina zuwa gurinta..!"

    Rik'o shi Annie tayi saurin yi zuwa jikinta,a hankali ta mayar da kanta gefen da take zaune tana kallonta rai a b'ace

      "Haba *HAUWA.!* ke kuwa me yasa zaki dunga tsoratar da da shi..?? Kina son rayuwarsa ta sake shiga garari ne,bayan tarin matsalolin da yake kan fuskanta na rashin sanin goben sa..??"

    A hankali hawaye suka fara gangaro mata,kafin tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa tana girgizawa ba tare da tayi magana ba

    "Mene matsalar ki kike kuka.?" Annie ta tambaya tana sake kallonta,ci gaba tayi da girgiza mata kai kamar wacce dama can abunda tafi iyawa kenan still bata ce komai ba,Annie da take tsaye fuskarta da damuwa tace

   "Ba kya so yasan asalinsa ko..? Kinfi so mu bar rayuwarsa a haka cikin wahala da duhu..?? Mene ne amfanin boy'ewar..? Kina tunanin hakan zaisa jama'ar dake masa gorin rashin mahaifi su daina.? Mene ne laifinsa dan ya kasance a haka..!? shi kenan dan yana amfani da sunan mahaifiya sai a tsangwami rayuwarsa..Haka kike so duniya taci gaba da kiransa *MARA ASALI,,,MARA TUSHE..?* yaci gaba da rayuwa cikin damuwa da bakin ciki all the time aka kira shi *MARA ASALI.. D'AN MACE.?"*

DOWNLOAD BOOK

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post