[Book] A Daren Farko Complete Hausa Novel by Rabi'atu Nasidi Abubakar

A Daren Farko

Title: A Daren Farko

Author: Rabi'atu Nasidi Abubakar

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Fiction

Doc Size: 440KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuciya Rabi'atu Nasidi Abubakar mai suna "A Daren Farko" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu complete dinsa.

Book Teaser: kotun ta yi tsit, kowa ya yi jigum, ana sauraran abinda xai fito daga bakin alkalin wanda yasunkuyar da kansa yana rubuce-rubuce.

Lauyoyi dasauran ma,'aikata wadanda suke da alhakin zama a kotun sbda sauraron shari'ah, kowanne yana xaune a mazauninsa daya dace dashi,haka yan kallo da iyayen yarinyar da ake gudanar da shari'ar a kanta al'amarin yan ba kowa tausayi shiyasa indai mutum yakalli fuskokin kaso tara cikin goma na mahalarta kotun sai kaga kowa cikin matsananciyar damuwa musamman wadanda abin yashafa, iyayenta da yan uwanta knan.

Mai shari'ah usman muhammad yadaga kansa a hankali yadubi wacce ake ka ra tana tsaye inda ake tsaida wadanda ake tuhuma hannayenta biyu sanye da ankwa.

Bakar rigace a jikinta da bakin hijjabi sanye akanta, ba dankwali idanuwanta sunyi wani irin ja saboda tsabar kuka, ba ta son dago kai tadubi kowa saboda tsanar kanta datayi don

haka ma da alkalin yakira sunanta bata dago kanta ba ta dai amsa cikin dashashiyar murya wadda da kyar ake iya jin abinda ake fada.

Alkalin yakuma cewa "Fatima Musa"

Ta amsa "Na'am"

"Ke kika kashe doctr Abubakar saddik wanda akafi sani da doctr khalifa???

Fatima tayi shiru alkali yana maimaita tambayar har sau uku batayi magan ba, yadda kasan kotun ba kowa saboda tsabar shiru, koda fatima da mai shari'a yake kallo ana sauraron

abinda fatin xa tace amma taja bakinta tayi shiru kamar dam chan yadda Llah yahalicce ta ba ta da bakin magana.

Mai shari,'a Muhammad Bamaina yana magana cikin yanayi na tausasa harshe yace "Fatima kotu tana tuhumarki da laifin kashe mijinki Dr. Khalifa kamar yadda ka kamaki da gawarsa shiyasa muke son ki bayyanawa kotu gasjiyar al'amari da bakinki tunda ke ba bebiya bace kuma ba kurma bace kina jin abinda muka fada kuma kina iya magana.

Idan ke kika kashe shi kifadawa kotun sannan kifadi dalilin dayasa kika kashe shi, idan ba ke bce ba to kidanyi magana kiyi bayani.

Fatima tadago kanta a karo nafarko tadubi duk jama'ar kotun suka hada ido da mahaifiyarta wadda tazuba tagumi dukda nisan dake tsakaninsu da Fati, Fati ta san kuka take wiwi tana girgiza kai, Fati tadubi mai shari'a sai kawai taj kanta yana juyawa kafafunta suka shiga rawa, hakan yasa suka gaza cigaba da daukar gangar jikinta tazube a gun, nan take mai shari'a Usman M Baina yadaga shari'a zuwa uku ga watan gobe idan Allah ya kaimu.

Kotu tarude da hayaniya, koke koken iyayan fati da yan uwanta ya cika kotun ga uar uwarsu a matsananciyar hali amma ba yadda xa ayi su taimaketa, sunaji suna gani wasu yan sanda mata suka daga fati aka fice da ita da gaggawa sbda numfashinta ne yake sama saa kamar zai dauke.

Yammaci ne akalla za mu iya kiran lokacin karfe biyar na yamma dawasu mintuna, ummi na zaune gefen tabarma ta hada kai da guiwatana kuka kamar ranta xai fita, goggo Abu ne gefenta itama tana goge hawaye cikin yanayi na tsananin damuwa kobaka sansu ba kaga halin dasuke ciki sai ka tayasu wnnan kuka dasuke, ko ba a maka bayani ba ka san damuwar daxata sa a yi irin wannan kuka ya isa a tayashi kuka.

Malam musa yashigo da carbi a hannunsa yayi sallama yatsaya chan daga bakin kofa yana kallonsu tsawon mituna biyar sanan ykaraso inda suke ,Allah sarki bawan Allah mai saukin kai wanda bai dauki duniya a bakin komi ba, fuskarsa cike da tausayi da karaya yake kallonsu ya ka sa magana, xuwa chan goggo Abu tagoge hawayenta cikin karfin hali tace

"Malam ka dawo?? sannu daxuwa.

Ya daga mata hannu yace ba na son gaisuwar ta kui tunda idanuwanku baxasu daina xubda hawaye ba akan abinda ba xai yi mana amfani ba. kokuwa wannan kukan xaiyi mana magani

akan damuwar damuka samu kanmu aciki??

Goggo Abu tace "Mala to yaya xanyi tunda abinnan yfaru ummi bata daina kuka ba. na yi lallashin duniyar nan yarinyar nan ta ki daina kuka har na rasa wacce kalma xan gaya mata wanda xa yasa tayi hakuri.

Malam yace "Ummi kiyi hakuri ko mu damuka haifi fatima babu abinda xa mu iya akan wannan lamarin sai dai addu'a.

Cikin matsananciyar damuwa Ummi tace "Shin baba shikenan daga hakuri babu abinda xa ku iya gaya min wanda xan samu sassauci a xuciyata game da halin da fatima take ciki???

Wyyo Allah kaicon rayuwata ni ummi in har xan xauna ina rayuwa a cikin tunannin fatima na kulle a kurkuku ana tuhumarta da laifin dani daku daduk duniya sun san baxata taba iya aikata shi ba.

Ya ya xa ayi ace fatima xa takashe rai, kisan ma ace tarasa wanda xa takashe si mijinta? kadubi wannnan al'amari ayi wani abu akai har yaushe muna zaune fatima na cikin mummunan zargi irin wannan".

Malam. musa yai xaman dirshan a wurin yace "Ummi toh yaya xamuyi? Saboda girman Allah me kike ganin xa mu iya yi kinsan indai ace muna da bakin yi din da yanxu ba wannan

xancen akeyi ba.

Kinsan mudai ba kudi garemu ba, kuma ko idan mutum na da kudi idan akace case din me xafi ne da tsanani irin wannan ba ka da tacewa, kudinka ba xa suyi amfani ba dan ba xa su sayi

ran da aka kashe ba balletana kasiya domin ko da ke biyan diyya idan wani yakshe wani ba a irin wnnan yanayin ake biyan diyya ba kinsan ita shari'a sabanin hankali ce, duk yadda kaje

tunaninta ta wuce nan.

Kuma idan ma muna da abin yin a yanxu ba xa mu iya ba idan Fatima ba ita takashe docta Khalifa ba tai magana man a kotu, kinaji kina gani daxu a kotu ka sa magana tayi ,tayi shiru

tabude bakinta tace ba ita takashe shi ba tafdi yadda abu yafaru akalla idan ma akwai abinda za a yi ai a yi tunda tayishiru me za ace??

Yagirgiza kai cikin dan zuciya yace "Allah kadai yasan yadda wannan abu yakasance sai kuma fatima.

Ummi taciji yatsa har yanxu kuka take mai ciwo a rai tace "Shi kenan baba shikenan goggo tunda kuma kun yarda fatee ita takashe doctor sai kusa ido itama a kasheta ba tare da hakkinta ba, amma dai inaso kusani ko ku kuka haifi mutum to ba kune kuka halicceshi ba yadda kake da hakkin yayi ma biyayya haka shima yanada hakinsa akanka idan kadanne Alah subhanahu wata'ala xai tuhumeka baba.

Nikam ba xan bar maganar fatee tawuce haka ba ,ba xan bari acigaba da xalintarta akan abinda bata aikata ba, zan shiga infita ko xan rasa zanin daurawa sai na taimaki Fati Insha

Allahu. 

Malam yace ummi ba na shakku akan abinda kika fada mun tabbatar xa ki aikata fiye da abinda kik fada akan fatima kaunar dake tsakananin ku ya wuce a fadadeta da baki, Allahbkadai yasan iyakacinta, sai dai inason kisani ba wai mun yardabcewa fati itace ta aikata kisan ba, kifahimci wani abu day

ummi ba mu da kudin daxamu iya daukan lauya daxai kare fati, ba ki da bukatar mugaya miki halin damuke ciki na kaka ni ka yin rayuwa a gidannan kinsan kome da ina mukaga halin daukar lauya sannan idan ma mun dauka dawacce hujja xa.

DOWNLOAD BOOK

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post