[Book] Jin Dadi Sabo Complete by Asma Baffa

Jin Dadi Sabo

Title: Jin Dadi Sabo

Author: Asma Baffa

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Love Story

Doc Size: 501KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuciya Asma Baffa mai suna "Jin Dadi Sabo" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu complete dinsa.

Book Teaser: Birnin tarayya Abuja cikin wani katafaren makeken gida na gani na nunawa a Tv, gidane Wanda ya amsa sunansa babu abinda babu cikinsa,ga motoci maka maka iya shan kallonka babu ta kasa da million Goma, Cikin wakeken palon me dauke da kujeru yan gaske ko a gidan shugaban kasa sai haka, wata dattijuwa ce kyakyawa chocolate  color amma mai duhu da ganinta kasan hutu, Naira da Jin dadi ya samu gindin zama a jikinta,Kwalliya da iya shiga ta zauna a jikinta hannunta rike da kafceciyar waya tana latsawa tana Jan tsaki kadan tare da karawa a kunnenta,ba sai an fada ba kasan wannan matar gogaggiyar yar boko ce,Cikin murya me dauke da fada tace Alklsm yaushe zaka dawo ne AHLEEF ? Ya kamata kazo ka karbi aikinka kasan na gaji ka bar min komai a hannuna daga cewa zaka je Saudiya da Paris hutawa har yanzu kaki dawowa,Abbanku baya kasar ka Sani, su Suhail kasan basa nan suna US Schl dinsu ba ayi hutu ba, ni kadai ce aikin yayi min yawa ya kamata ka dawo kaci Gaba da rike dukiyarka tafi karfina.

   Dariya Ahleef yayi kadan a waya yace Momee zan dawo soon kiyi hakuri,Better cewar Momee gashi Niima ta gama University yanzu kaga sai mu fara shirin bikinku Ko ? Jin an ambaci matar daya fi so a duniya Niima yaji wani farin ciki a ransa ya kusa mallakar Niimarsa wacce yake ganin tafi ko wacce mace a duniya,duk mata mazaje ne a wajensa Sabo da Niima wacce kullum sai sunyi waya yaji muryarta yake iya bacci,Momee ko dan shirin biki ai dole na dawo am sorry Mum,Murmushi ta saki a rayuwarta babu Wanda take kauna sama da Ahleef ko yayanta da ta haifa Bata sonsu kamar yanda take son Ahleef a duniya.

   Bayan sun gama waya da Ahleef cewar Next wk zai dawo gida.

    Wata yar kyakyawace Chocolate me kyan diri zata kai 25yrs ta  shigo Palon Momee tana faman yatsina fuska,sanye take Cikin wasu Arabian  wears dark blue riga da skert masu tsada da kyau jakarta ta ajiye gefe tare da zama kusa da Momee,Momee na gaji yau nasha aiki a Office ga Meeting da mukayi sun kai kala uku,Cike da tausayi Momee tace sannu Niima ai haka aikin yake ba sauki,je kiyi wanka kici abinci sai ki samu ki huta Ko, Da sauri ta Mike ta nufi sama abinta,Yar karamar yarinyace ta shigo sanye cikin Uniform na Islamiyya Zata kai 15yrs tun daga waje take cewa Momee na dawo,yar fara ce yarinyar amma ba kar ba tana da dan Duhu kadan amma ba baka bace, Last Born Latifa kenan cewar Momee wuce ki cire Uniform ki kaiwa me muku wanki a wanke,Yess Momee ta wuce da gudu.

    Bayan sati guda da zancen Ahleef zai dawo daga Paris Sabo da dokin auren Niima bai canja Date ba,yau Saturday yaune kuma suka tashi da girke girken tarbar babban bakonsu,Niima dai tana Murna itama sosai dan tayi missing kyakyawan saurayinta.

     2pm jirginsu ya sauka a Abuja,Momee ce kawai taje tarboshi tace ita kadai zata je, Tare da escort suka jera motoci guda Takwas.

Also Download: Duniya Ta Complete by Asma Baffa

    Janye da Trolley dinsa ya fito,Gaba daya kallo ya koma kansa mata da maza Sabo da tsananin kyawunsa hade da iya shiga,ya  tsaru iya tsaruwa,Sumarsa kadai abin kallo ce da birgewa,dan gemun nan tare da dan saje kadan sai sheki sukeyi suna walwali,Fatarsa kadai abin birgewa ce sai ka rantse yanzu aka fito dashi daga cikin engine,ba sai an fadama ba kasan Naira da Hutu tare da Jin dadi Sun ratsashi,sanye yake Cikin kana nan kaya White and Grey color kamshin dadinsa gaba daya ya mamaye Airport din, Dogo ne Amma ba can ba, shi ba me kiba ba sannan ba siriri ba, idonsa dara dara suna lumshewa, fuskarsa tana da dan tsayi kuma tana da dan fadi normal, hancinsa dogo dan lcib baiyi tsini da yawa ba,bakinsa dan karami jajir dashi yana shining,Fatarsa fara ce amma ba irin kal kal ba,wata iri ce ta birgewa shi ba farin dan Africa ba, ba na larabawa ba kuma na bature ba,haka sumarsa ma take Unique ce kamar ruwa biyu haka yake,babu Wanda zai ganshi bai kara kallonshi ba ko maza ne bare mata,tafiyarsa kamar basarake ta maza masu ji da kansu sai shegen Iyayi a cikinsa da gani ba sai an fada ma ba, bazai wuce 31yrs ba yana ji da kuruciya a cikin lokacinsa yake,tun Kafin ya karasa Momee take zuba murmushin Jin dadi danta da tafi so fiye da yayanta na cikinta ya dawo kusa da ita,da sauri ya karaso tare da rungume Momee yana murna itama haka,Cike da ladabi ya gaisheta sai shagwaba yake mata yana narke mata gwanin sha'awa itama tana lallabashi.Momee tace Son lets go nafi so kaci abinci ka huta,cikin muryarsa me dadin gaske me tafiya da zuciyar yan mata cike da iyayi yace Sorry Mum muje,da kansa ya bude mata ta shiga shi kuma Escort suka bude masa ya zauna gefen Momee,suna gaishe shi yana amsa musu da sakin fuska ba wulakanci,Direct gida suka wuce,Latifa da Niima kawai fadawa sukayi jikinsa suna ta tsalle da murna,da kyar momee ta koresu daga jikinsa,shima da yake Shu'umi ne sai ya jawo budurwa r tasa Niima ya rungume kam a jikinsa,ba karamin kyau tayi masa ba,ga wani kamshi da takeyi,Yaji Albarkatun kirjinta male male bisa kirjinsa lokacin Momee ta shiga kitchen,ya wani lumshe ido yace uhmmmmm wannan mene haka kamar jinjirin mage Sabo da laushi,itama Niima tace dashen Allah kenan ni kaina ina ji dasu,dariya yayi ba karamin kyau dariyar tayi masa ba kamar kar ya daina,hakoransa kanana jere suka bayya,yace to maza San min kafin Momee ta fito yana wani shagwaba,Zatayi magana kenan sai Ji sukayi Momee tace ku kuma mene haka? Ban son iskanci ku kiyayeni fa, da sauri Niima ta gudu Bedroom dinta,shi kuma yace Momee Bari nayi wanka nazo naci me dadi kinsan I missed ur food.

    Asalin Ahleef

ALHAJI AHMAD SALEES(ALHJ AMADU) Dan asalin kasar Niger ne,tun asalinsu kaf danginsu talakawa futuk, Amadu shi kadai iyayensa suka haifa a duniya, Bayan Amadu ya cika 25yrs iyayensa suka rasu Gaba daya sakamakon hatsarin mota sai yan uwa dangi,sanadin talauci yasa kusan zumuncin ma ba ayi da juna kowa yana bige bigen neman kudi,Amadu duk yafi su zumunci da hakuri tare da tawakali gashi da addini,hakan noma kawai yake danyi dashi yake ci yake sha,watarana yana gona ya hadu da SAUDAT wacce a yanzu take Hajiya Saudatu, yar asalin larabawan libiyace kyakyawa ce ta gasken gaske,fada ne na yan taadda ya barke a kasar tasu sukayi gudun Hijira zuwa Niger,Saudat kaf danginta an kashesu a yakin da akayi a kasarsu ita kadai ce ta tsira ta shige cikin Yan Hijira zuwa Niger,tunda tazo Niger take cikin gari a titi sai wanke wanke da shara da takeyi a wani gida ana biyanta,da haka take rufawa kanta asiri tana wannan gantalin Allah ya hada ta da Amadu a Gona,nan yaji sonta ya kamashi har ya kai ga yi mata magana,tas ta bashi  labarinta na rayuwa kuma ya tausaya mata,tun daga ranar suka fara soyayya kullum suna haduwa a gona.

    watansu biyu da haduwa ya sanarwa danginsa ya samu mata,sune suka tallafa akayi masa komai cikin talauci sosai akayi bikin,yan unguwar haka suka dinga surutu Amadu ya auri balarabiya yar gudun hijira ba a San asalinta ba etc,cikin bakin talauci na karshe suke Zaune lfy sai uwar soyayya da suke zubawa.

   Sun kwashe kimanin shekaru goma sha biyar tare amma basu samu haihuwa ba, tun suna sa rai har suka hakura gashi basu da kudin zuwa asibiti ko maganin gargajiya haka suke ta addua. 

   Saudat sarkin hakuri, watarana tana zaune makociyarsu ta shigo tare da kawo mata Maganin sanyi Infection na gargajiya, tace Saudatu ga maganin sanyi ba a son mace ta zauna Bata shan maganin sanyi lokaci zuwa lokaci,Godiya tayi tare da karba,wata uku tayi tana amfani da maganin cikin ikon Allah sai ga Saudat da ciki murna ba a magana,har cikin ya cika wata tara ta haifi danta namiji kato kyakyawan gaske ajin karshe,ko ina zuwa akeyi kallon jaririn Sabo da kyansa,ranar suna yaro yaci suna Ahleef,Ko hakikar suna ba a yanka masa ba Sabo da talauci,bayan wata uku da haihuwa talauci ya kara zurfafa musu sai kawai sukayi shawara cewar gwara su koma Nigeria da zama garin kasuwanci ko Allah zai sa su samu aikin yi,basu tsaya ko ina ba sai Nigeria Cikin Kaduna state.

    Cikin ikon Allah wani hamshakin me kudi ya dauki Amadu gadi a bakin gate tare da bashi daki da toilet a gidan yace ya kawo iyalinsa su zauna tare,Zama yayi zama Sun kusa shekara lokacin watan Ahleef bakwai Me kudin ya biyawa Saudatu da Amadu aikin hajji tare da jaririnsu,sannan ya siya musu katon rago aka yankawa jariri Ahleef na Hakika, bayan sun Dawo da wata biyu lokacin Ahleef ya cika 1yrs Allah yayiwa me gidan da suke aiki rasuwa,bayan rabon gado gidan ya tarwatse Gaba daya yaran Alhaji suka koresu gida ya zama na gado, Shine silar barin gidan gaba daya basu San inda suka nufa ba,ruwa,iska,rana sanyi duk ya kare a kansu har Allah yasa wani mutumi ya gansu ya tausaya ya basu wani dan karamin daki dake a kofar gida kamar na maza,anan suka raba suna zama, Ahj Amadu ya koma dako a kasuwa ita kuma tana wanki da guga.

    watarana ta bar Ahleef a Daki ta shiga wani gida karbo ashana zata hura wuta a waje ma suke girki kowa a titi yana kallonsu,kuma bandaki daya suke shiga da wasu kartin maza samari hakan ma tausaya musu sukayi ganin basu da inda zasu shiga idan shiga bayi ya kamasu,Allah yasa Saudat me tsananin tsafta ce kullum toilet din samarin a wanke kal ita take wanke musu kuma suna jin dadi.

   Tana shiga karbo ashana ashe wasu samari masu satar yara suna siyarwa matsafa suna fakonta a unguwar su biyu,jira dama suke su samu dama, Ranar ba kowa a layin kawai suka fada dakin tare da fesawa yaron Powder ta bacci suka sakashi cikin towel tare da fita da gudu suka fada motarsu sai birnin tarayya Abuja dama abinda ya kawosu Unguwar kenan.

   Saudat tana fitowa neman duniya Bata ga Ahleef ba haka ta haukace Ko ina tana tambaya mutane Sun tausaya mata,Shi kanshi Amadu Kuka wiwi ya dinga yi da yaji cewar dansa da suka fi so a duniya an sace shi, Kullum cikin kunci suke gashi Saudat ta nace ita tasan danta yana raye,kuma idan an sace yara Kudu ake kaisu dan haka ita wai dole sai Sun bar arewa,haka ya lallabata ta hakura har suka kara samun wani ya dauki Amadu yake kula da flowers na gidansa,part guda ya basu suke zama lfy, har suka kwashe shekaru ashirin da biyar a gidan,Sai me gidan ya fara neman Saudatu yana so yayi lalata da ita ganinta kyakyawar gaske tafi matarsa,Amadu yana Jin labari ba yanda Amadu ya iya haka ya kwashi matarsa har zuwa Abuja City, Cikin sa'a kwanansu uku da zuwa suka samu wani attajiri Alhaji Dauda ya daukesu aikin gadi a gidansa, ita kuma Saudat zata dinga yiwa yaransu wanki, kaf iyalan Alhaji Dauda basu da tarbiya bare mutunci,shi kadai ne me dama dama, boysquaters ya basu a nan suke zaune,cin mutunci iri iri ake musu a gidan haka suke hakuri,ganin haka yasa Saudat ta fara Soya doya da kwai  a bakin wata yar kasuwa kusa da wani katon mall na kece raini,Idan tayi wankin da takeyi da yamma sai ta tafi wajen sana'ar soya  doyarta,dake ta iya sai take samun kudi sosai har masu kudi suna tsayawa su siya Sabo da tayi mugun iyawa kalarta daban ce kowa yaci sai ya kara,ta tsare mutuncinta normal.

DOWNLOAD BOOK{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post