[Book] Jininmu Daya Complete by Sadiya Ibrahim Khali

Jininmu Daya

Title: Jininmu Daya

Author: Sadiya Ibrahim Khali

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Love Story

Doc Size: 500KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuciya Sadiya Ibrahim Khali mai suna "Jininmu Daya" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu complete dinsa.

Book Teaser: A nutse ta iso falon ta tsaya bayan kujerar da matashin da zai haura shekaru 33 da yake zaune wani yaro a cinyarsa yana shafa kanshi matashiyar bazata haura shekaru 22 zuwa da 23 ba sai da yaji numfashi a bayansa yasa ya maida dubensa kacokam ga bayan kujerar a tsaye ya sameta ta harde hannayenta tana murmushi ya dan sauke ajiyar zuciya yace Rufaida na lura dai sam yau tsokanata kike ji Rufaida tace bahaka bane Yaya Wahid ya dan juyar dakai yace to ya akai tace dama naga yau kurum ta Yasir kake ni ko kulani ma bakayi Wahid yace to meye damuwar Yasir dai dan kine banasan rigima dawo nan kizauna ya nunamata kujerar da suke ta zauna kusa da yasir tana mai ambatar Bismillah Yasir Ya dan dubi fuskar Rufaida yace Mami kinji Dad sai je Zaria kuma ba zashi daniba Rufaida ta Kalli Ahad tace kaji Dad kurum ka bari wani satin sai mutafi mu duka ya dan marairaice yace Mami kinsan kiran Umma ne gwara na naje wani satin saina kaiku tunda ba kwana zanyi ba tace haba Yaya yaza'ai ka  tafi yau ka dawo yau yaushema harkabar Abujar yace ai bawai a motar haya zaniba zan iya kaiwa har na juyo ni narasa Kiranma Umma takemin Rufaida tace ni fatana ma dai har kullum Allah yasa lafiya kalau nima kiran na kasa gano dalilinshi yace to Allah yasa lafiya Rufaida sam bazata iya furtawa mijinta tasan dalilin kiranba da mahaifiyarshi ke masaba don batun yau ba tasan komai tunma kafin aurensu shima Wahid bayajin zai iya furtawa Rufaida dalilin kiran dukda ya tabbatar Rufaida mai hakuri ce sai dai bayasan wani abu yasa zuciyar kuncin da bazata iya furta komai akaiba amma shi bayasan ace daga aurensu ya kara wani auren dukda suna da daya amma duka Yasir nawa yake baikai uku ba har yau to kuma suna zaune lafiya da matarshi meye dalilin kara auren Ruqayya da Umma takeso tayi don baya tunanin zasu zauna lafiya yaji ma da matsalolin  aiki kuma yadawo gida ya tarar da wani shiyasa bai fadawa Abba zuwan ba dan yasan ba zai amincemasa yazoba shikuma yanason mahaifiyarsa yaje gareta ya mata magana yadda zata fahimcesa kota samu ta barsa da wannan zancen shi dai har ga Allah baya yiwa Rukayya irin son aure ta kasance abokiyar rayuwarsa sai dai sona zumunci tunda yasan Rufaida tasan komai shiyasa bayason jagwalgwala maganar danshi mutum ne da bayason a dinga tada abin bacin rai.

Jin shirun da Wahid yayi yasa Rufaida cewa Yaya koka FASA tafiyar ne lokaci fa baya jira cikin sauri ya dawo daga tunaninsa,yace ai kema kinsan sai an amsa kiran Umma yau Insha Allah,fitowa sukayi shida Rufaida da Yasir har bakin motarsa suka kaishi yace har zai tadane Rufaida tace Yaya Wahid namanta fa zuwanmu gidan Luba yace au nashafa'a jeki ki shirya tace ai Yaya na shirya bara na rufo ciki murmushi yayi yace to suna tsaye da Yasir ta karaso ta shige gidan gaba Yasir yana baya Wahid yana zolayar Rufaida da cewa da ya tafi sai dai tahau taxi murmushi tayi tace ai kudinka ne zai kuka a bakin gate ya tsaya masu gadin Barrack din ya tsaida motar suka gaisa suna yallabai sai ina yace Zariya zanje amma su a gidan abokina Kabir zan saukesu addu'ah suka yimusu kana ya fice daga barrack din 'yan sandan na cikin garin abuja Area1 a Gwarinfa ya saukesu Rufaida har gidan Kabir ya shiga suka gaggaisa da Luba tana baya shigowa sai dai taji firarsu a sitroom yace kusan bana zuwan banzane kinsan shine dalili Rufaida tace ayimasa hakuri zai gyara Yusuf dan Luba yana ganin Yasir suka fice harabar gidan sunata fara wasa,Yace Luba ina abokin nawane yace wallahi ya fita shida Nazir amma bazasu jima ba yace ai ki kyalesa kawai ni tafiya zanyi zanje Zariya zamuyi waya idan naje.

Bai jira komai ba ya mike Luba tamasa addu'a Allah ya kiyaye hanya yace Amin ya fice daga Falon Rufaida ce tabisa tana masa addu'a sannan tace  ya gaida kowa da kowa harda su Gwaggo da Malam da Abba yace aiko  da wuya naje gidansu Gwaggo cikin bata fuska tace maiyasa  yace saboda kinsan ba kwana zanyi ba tace shikenan amma dai ka daure kaje yace to ranki ya Dade abinda kikace shi za'ayi murmushi tayi tace ko kaifa Yasir ya karaso gurin Babannasa shida Yusuf suna cewa Dad Allah ya tsare Rufaida ma cewa tayi Allah ya tsare Allah ya dawo dakai lafiya a gaida kowa da kowa Wahid ya amsa da amin yana murmushi yaja motar ya fice daga gidan sai da yafita da motar Yasir ya dawo gun Rufaida yana kuka babansa ya ki tafiya dashi Rufaida ce ta shiga lallashin yasir din tana cewa idan baka daina ba Yusuf zai yima dariya ka ganshi can yana kallonka Yusuf can gurin wasa Yasir din ne ya tafi gurin Yusuf din Rufaida murmushi tayi tace kawai ta shige ciki.

Luba ta kalli Rufaida tace sai yanzu kika barshi ya tafi kenan,Rufaida murmushi tayi tace kai Luba banda sharri yaushe ma muka fita,ni cikina ya fara kiran ciroma goma ta wuce na safe bikinsan mai zaki dafa ba kin daka ta wannan chat din gaskiya Yaya Kabir yana hakuri ace mace bazata gama girki ba sai wajen 4 na yamma Luba tace to hadasu kasa rabasu duka sau nawa kika zo gidan nawa kika tarar bangama abinci ba da wuri wannan chat dinma saikisa a hana mutane Rufaida tace dama yafi Luba tace da kema nasa an hanaki baki Rufaida ta ta'be tace ni kinsan baidame ni ba,Luba tacanza zancen da cewa mutumin kifa yau zanyi Rufaida tace alala gaskiya ki tashi mu dora tun yanzu haka suka mike suka shiga kitchen

Bugun Zuciyar Rufaida ne ya karu dole ta bar kitchen din taje falo ta kwanta hakanan yanzu take jin bugun zuciyar batasan daliliba anbatan Allah ta fara yi a cikin zuciyarta,wayarta ta lalubo ta danna tasa a kunne,a daya bangaren murmushi Ahad yayi ganin sunan mai kiran My wife ya daga ya gabatar da sallama ta amsa tana cewa Yaya Ya hanya yace Alhamdulillah nakusa zuwa Kaduna wayar ta ka tse tana masa addu'ar Allah ykiyaye hanya yayi murmushi yana kara jin kaunar matarsa a ransa da haka ya cigaba da tukinsa 

Wahid bayan barinsa cikin Kaduna yana gaf da shiga Zariya,duk yadda yaso kaucewa motar sai da tazo ta bugi da motarsa nan motar tasa ta dinga mirginawa yanata salati motar man da tayi gefe ta kama da wuta abinka da cikin jama'a yasa dan dan nan gurin ya cika AbdulWahid ake kokarin ceto aka tsaida motar da ta fara shigewa rami kuma mai zurfi dakyar aka fiddoshi daga cikin motar jini yayi kaca kaca da jikinsa bazaka taba shaida cewa wannan fuskar AbdulWahid ne matashi mai kuruciya kyakkyawa lallai duniya ba abakin komai take ba,wayar dake cikin motar da duk ta ragargace police suka dauko suka aka saka sim din a wayar wani daga cikin yan sandan bayan anyi kokarin sasa a motar police din aka bar wasu suna bincika motar tasa nan aka fara kokarin kiran danginsa amma yawanci duk bata shiga ta Rufaida ce kawai ba'a kira ba

 A abuja

Rufaida lafiyarki kalau kuwa kin kasa cin alalan nan kuma bayan nasan kinasan alala Luba ta fada tana dafata damai da fuskarta ga Rufaidan Rufaida tace wallahi Luba wayar Yaya Wahid nake takira naji ko yaje zariyan to da tana shiga baya dagawa yanzu kuma taki shiga gaba daya kuma nasan yaya Ahad baya kin daga wayar Luba tace ki sake kira kiji to yanzu,wayar Rufaidan ta dauka tasake kiran sa anan tayi sa'ata shiga daya daga cikin dan sandan da yake a farfajiyar General hospital na Zaria din ya dubi abokin aikinsa yace yallabai ana kira wancen mai hatsarin naga an rubuta My wife yace,daga kila matarsa ce tunda an kira iyayennasa basu daga ba da ya rubuta hakan da sallama dan sandan ya amsa wayar  jin bashine ya amsa wayarba nan Rufaida bugun zuciyarta ya karu dan sandan yace wacece ke a gurinsa tace matarsa dan danan dan sandan ya katse wayar zuciyarsa a raunane domin bazai iya fadama Rufaidan halin da mijinta yake cikiba nan Luba ta kalli Rufaida tace ya akeyi Rufaida tace cikin karayar zuciya tace Luba bana tunanin Yaya lafiyarsa kalau kuwa nan ta labartawa Luba abinda ya faru a wayar da sukayi Luba tace bara na kira baba yusuf nafadamasa ki kwantar da hankalinki ita dai to tace kawai kira daya Luba tayiwa Kabir ya daga yace yana kofar shigowa falon bata aje wayarba ya shigo falon yana riqe da hannunsu Yusuf da Yasir gurin mamarsa ya nufa ya kwanta a cinyarta Rufaida batasan sanda hawaye ya zubo mata ba ta fashe da kuka tana shafa kan Yasir Kabir ya kalli Luba yace Wife mai aka yima Rufaidan ta dan dubesa tace Wallahi abokin nakane Baban Yasir ake ta kiransa yaqi dagawa karshe ma wanine ya daga Kabir yace haba to shine abin kukan bari na kirasa naji yanzu namaga missed call dinsa badamar na daga ina tuki wayar tasa yasa a kunne maganar da yaji anfadamasa a wayar ita ta girgizasa ya dan saki murmushi bayan gama wayar yace,to meye abin damuwar ki shirya yanzu m tafi gidanku ashe aprilfun ya miki ko zariyanma baije ba ita dai Rufaida cikin kasala ta mike tana tunani kala kala to ita tunda take da AbdulWahid baitaba mata wani April fun ba bare kuma yau yayi mata yanzu asalima shi bayasan wannan April fun din tunda ba shi a musulunci shiru tayi ta mike tasa hijibinta tace ta shirya Kabir yace kema wife kije ki dauko hijabinki tace Abban Yusuf kaje kaci abinci mana kafin mu tafi yace kibarshi ni na koshi munje shoprite da Nazir,Luba dai ba tace komai ba dan tasan mijinta baya cin abinci ako ina ba sai gida

Hanyar Zaria ya nufa dasu ya hada rai domin karsu tanbayesa ma Rufaida kuwa kukan zuci kawai takeyi dan tariga data yanke tsammani.

DOWNLOAD BOOK{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post