[Book] Matar Lecturer Complete by Precious Hajja Ce

Matar Lecturer

Title: Matar Lecturer

Author: Hajja Ce

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Short Story

Doc Size: 15KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuciya Precious Hajja Ce mai suna "Matar Lecturer" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu cikin sauki.

Book Teaser: Mace ce kyakyawa dan idan ka ganta sai ka ɗauka ko budurwa ce, zaune suke a parlour suna kallo yayin da mijin ke ta cike cike takaddu da cikin laptop ɗinsa, ya wancin kallon ma duk ita take shi hankalin shi yana ga aikin da yake yi hakan yasa ko wata maganar tayi bayaji sai ta kuma cewa kaji!,

    gajiyar da tayi ne yasa ta fara ɗan gyan gyaɗi kafin ta juya tagan shi zaune ko alamar bacci babu a idon shi, cikin muryar shagwaɓa ta shafo fuskar shi tare da cewa;

 "teacher please muje mu kwanta 12:45am fa kaji"

  ta faɗa tana ɗan shafa kirjin shi fuskarta akan tashi tana kallonsa tanajin wani irin son shi yana kara darkuwa a zuciyarta.

  Ajiye biron yayi sannan ya ɗan tallafota zuwa kan cinyar shi yace ;

 "oya kwanta kiyi baccin ki anan idan na gama saina ɗaukeki mu wuce ɗaki tunda kinga ni aiki nake which is very important to me,so kiyi hakuri yanzu ki kwanta anan"yace hakan ya nuna mata kafar shi tare da cewa ;"

  dana ɗan karasa zamu tafi ko bayan baccin kina bukatar wani abun?" 

  girgiza kai tayi alamar a'a dan ta gano manu farshi, ita kama yanzu bacci kawai take bukata dan haka ta gyara kwanci a kan kafarshi tare da rufe ido bata daɗe ba bacci ya ɗauke ta, shi kuma ya cigaba da aikin shi lokaci lokaci yakan ɗan shafo kanta tare da mata peck a goshi.

around 2:30am ya kashe komai tare da saka su cikin wata katuwar school bag wadda yake zuba duk wasu muhimman abubuwan shi a ciki,ahankali ya zamar da kanta daga kafar shi ya shiga toilet, alwala yayi sannan yazo yayi sallah tare da addu'o'insa karfe 3:00am ya cicciɓi Matar shi suka wuce master  bedroom.

 Cikin bacci taji yana mata wasu abubuwa, hakan yasa tayi saurin buɗe idanuwa kafin ta sauke su a kansa cikin hasken bedside lamp ta hangoshi yana ta wani kashe mata idanuwa tace cikin turo baki....

"my teacher yanzu dan Allah sai yanzu zaka kwanta?"

 Cikin wata irin murya sassanya yace;

  "i'm sorry wifey kinsan aikin da yawa kuma gobe nake son zuwa dasu thats it why nakai wannan time ɗin"

  haushi fal cikin zuciyar ta, full time ɗinta ya barsu gurin cike ciken abubuwa yanzu kuma yazo yana wani bukatar ta, abun haushin kuma 6:45am ya shirya ya bar gida,tana ta sake sake ta biye mai har ya samu biyan bukata sannan bacci ya ɗauke su a take gaba ɗayan su.

    5:58am ya farka, toilet ya wuce sannan ya kuma dawo wa tashin ta yayi ta mike da kyar, suka je wankan tare sannan ya jasu jam'i sukayi tare suna idarwa ta wuce kitchen dan samar mai wani abun, ruwan tea da soyayyan kwai tayi mai dan tasan ba tsayawa zaiyi ayi mai wani lafiyayyan breakfast ba, yana gama wa tayi mai rakiya yashiga mota fatan alkairi tayi mai sannan ya wuce ita kuma ta koma cikin gida.

"hello my teacher how far?"

   "a'm fine wifey, ya gidan hope komai lafiya?"

 "kalau"tace mai cike da so, sallama tajiyo tacikin wayan kuma muryan mace, bataji ya amsa ba suka ci gaba da hirarsu,

  "gud morning", taji an sake cewa nan da nan hankalinta ya tashi ta daure tace mai," my teacher kana ina ne yanzu?"

  "office mana"

"ok wasu ne suka zo?"

ta tambaya, yace "ehh ina zuwa bari na sallame su sai in kiraki"ɓejira cewar taba ya kashe.

a gida hankalin Aisha a tashe, kardai teachern ta 'yan mata gare shi! taɓ kici akwai tashin hankali kuwa ita zai rainawa hankali, sake kiran layin tayi ya ɗauka....

   "hello wifey!"

bata amsa ba sai tambaya data wulla mai, suwaye suka zo maka office?"

  ɓe kawo komai ba yace wasu studant ɗina ne, ɗazu nayi musu test shine su basuyi ba suka zo suna rokana akan na basu koda assigment ne kuma naki yadda.

  wani numfashi ta sauke mai karfi, yana jin tace "Alhamdulillah,please teacher na ka kula min da kanka i love you,"

yayi murmushi kamar tana kallon shi sannan yace

" ok i will insha Allah love you too,"

shima ya faɗa ssannan duk suka ajiye phone ɗin kowa cikin jin daɗi tare da son junan su.

karfe 4:30pm ya baro BUK zuwa bichi kasan cewar irin wannan lukutan go slow yayi yawa a hanyar hakan yasa ɓe karasa gida da wuri ba sai kusan 6:15pm.Da gudu ta fito yi mai oyoyo tare da karɓar kayan shi ta kama hannun shi suka wuce ciki.

   toilet ta fara kaishi tayi mai wanka sannan ta bashi kaya marasa nauyi yasa,masallacin kusa da gidan ya tafi dan gabatar da sallar magriba, yana idarwa ya dawo gida wanda itama time ɗin tayi sallah harta sake makeup tare da bin sassan jikinta da humra mai kamshin daɗi.

  a parlour ya kwanta a kan duguwar kujera,

" my teacher ya da kwanciya bakaci abinci ba?"

"washii" kawai yace mata batare dayayi magana ba,karasawa tayi tasa tattausan hannunra tana mai massaging cikin jikin shi yayin da yake wani lumshe idanuwa.

   karar wayan shi ita tasa Aisha da kadar da abinda take yi, zaro wayan yayi ya duba, ganin ba suna yasa shi ajiyewa ya kuma ɗora mata kafan shi akan tata suna wasa da dariya tana cigaba da matsa mai.

kiran ne yayi ta shigowa, ganin bashida niyar ɗagawa yasa tace ;

"my teacher ka ɗaga mana bakasan ko meye va"

ɗan tsaki yayi tare da cewa;

 "Kika bibiya students ne" yana kaiwa nan ya ɗaga tare da cewa "hello".

"Good evening sir"ɓe amsa ba yace" ya akayi?"

  cikin kashe murya ta cikin wayan tace;

"sir nice ta ɗazu dana zo office ɗinka"

 uhmm ya faɗa ranshi ɓace dan an katse mai jin daɗin shi.

 " dan Allah sir, ka temaka min gashi kace last c.a ɗinka ce pls sir ka bani koda assignment ne," tayi shiru danjin mezai ce dan sun san ɗan wula kanci ne na karshe.

DOWNLOAD BOOK{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post