[Book] Meke Faruwa Complete Hausa Novel by Aisha Isah

Meke Faruwa

Title: Meke Faruwa

Author: Aisha Isah

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Love Story

Doc Size: 432KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2016

Description: Sauke littafin marubuciya Aisha Isah mai suna "Meke Faruwa" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu daga shafin nan.

Book Teaser: Yana kwance cikin tafkeken bahon wankan da ke cikin tsfkeken bayin, Sam bai yi kama da bayi ba, domin yana da girma kwarai. Bahon kato ne haka nan daga inda bahon kana iya kallon TV manne jikin bango can daga nesa kadan ga gurin da zaka zauna don yin bahaya (toilet) tsararre ne mai tsafta. 

Kwance cikin baho Modibbo ne, daga in da yake cikin bahon da ya cika da ruwan dumi da kuma ruwan sabulu mai shegen kamshi yake canza tashar da yake kallo zuwa (CNN) daga inda yake yana jiyo karan kawankawasa  kofar bayin. Shin wanene? Ya tambayi kanshi amma ci gaba yayi da kallonshi. Da ya tuna duk Wanda ya matsu ya jira shi kusan rabin sa'a sannan ya soma cuda jikinshi, ya cire abin da ya toshe rariyar da ruwan ya tsiyaye sannan ya kunna wani dake zubowa daga inda aka rataye su ya rufa a jikinshi sannan ya dauki karami yana goge sumar kanshi. Bayan yazura lallausan silifas a kafarshi zama yayi kan wata kujera duk dai nan cikin bayin ya shafe jikinshi da mai mai kamashi tare da turaruka ya gyara sumarshi tare da shafa mata nata kalolin.

 Modibbo yana kashe ma kanshi kudi fiye da zaton mai tunani,mikewa yayi cikin tafiyarshi ta kasaita ya nufi dakin barcinshi don saka tufafi ya kalli kofar da zata kaishi falo sai ya tuna ana jiranshi, din taski yaja sannan ya rufe kofar (bedroom) din shi bayan ya shige tare da fadin ko ma waye zai tafi ne don yanzun lokacinan na kar2 ne. Shirayawa yayi cikin wandon {jeans blue} da rigarsahi mai dogon hannu ya isa kan durowa ya kwashi takardu tare da wayoyinshi ya zuba su cikin aljihu, takalmanshi sawu ciki ne ya saka sannan ya fita.

  Vicky ce zaune a falon tana jiranshi,ji yayi tamkar bai ganta ba duk da tsananin son da yake yi mata. Ya nufi hanyar fita, ta taso da sauri tana kiran shi. 

Darling prince D P

Ci gaba yayi da tafiya, ta soma gudun sassarfa ta cinma shi ta dafa kafadarshi tana cewa cikin turanci. 

Duban ta yayi tamkar ba zai magana ba sannan yace amma kin yi saurin hucowa. Ya taba baki" ina zaton kin manta ni wanene shi yasa kike yi min fushi, bani da lokacin lallashin ya mace duk da son da nake musu. Ki gane bani Yarima Modibbo ke bin mata ba, ni suke bi. Je ki ci gaba da fushi dan kin ganni da wata. " yaci gaba da tafiya yana sake fadin Yanzu lokacin kar2 ne ba na surutu ba. 

Ta tsaya ranta a bace,hawaye ya soma zubo mata tana tunanin yaushe ne zata daina kuka saboda prince? Yaron da take matukar so, yaron da mata suke rububinshi, yaron da yake ma mata jan-aji, yaro mai kyau da kwarjini, ta zube ta soma kuka. 

 Kafin ke dubin ki sun yi Vicky . 

Yarima Al-amin kenan. Kenan dan sarki Ismail jikan Abdullahi mai mulkin yankin Bauchi. Matashin yaro dan shekara ashirin da biyu  Wanda aka fi sani da YARIMA MODIBBO A malesiya gurin kar2 ake CE mi shi prince

A ZARIA FA? 

Katon gida ne ginin kasa mai dauke da sassa kusan goma sha biyu, gida ne ginin kasa tun na da wato ginin gargajiya. Kafatanin 'yan gidan dangin juna ne in ka dauke Fatima'yar mutanen Bauchi da aure ya kawo ta gidan. Yanzun da haka fatimar ce zaune tana tuka tuwon dawa, Bilkisu ta yi sallama ta shigo jikinta sanye da atamfa java, ta rataya jaka kana ganinta kasan daga makaranta take. Bilkisu kyakkyawa ce ta bugawa a Mujalla, domin idan har za'a zuba gasar kyau ta shiga ciki babu abin da zai hana ta lashe gasar 'yar kimanin shekara ashirin da biyu CE. Ta isa gurin mahaifyarta Fatima tana fadin.

Mamarmu sannu da gida Ta dube tace da kulawa duk da kasancewarta'yar fari ta ce "yauwa sannu maigado. { shi ne sunan da ake kiranta da shi } ma'ana mai gadon zinar. Kirarin maisuna Bilkisu. 

   Yau kin dawo da wuri. Ta ce " Eh, Mamarmu wata kawar mu muka je dubawa da tuni na dawo. Ta ce Allah sarki, bata da lafiya ne? 

 Zazzabin cizon sauro ne, nan sabon gari suke. 

 Allah ya bata lafiya. In ji mamar. Amin . Bilkisu ta amsa. Sannan ta nufi dakin mamansu duk da gajiyar dake tattare da ita sai da ta share dakin fes tare da gyara shi. Sannan ta fito ta share tsakar gidan duk da cewa ba'a siminte yake ba, yakan ba da sha'awa in an share . 

Asma'u Auta ta shigo da sallama, ta dawo daga Islamiyya tace, Sannu Mamarmu, sannu Aunty Maigado. Bilkisu ta harare ta da sauri ta gano laifinta ta ce, Na manta ne, yi hakuri. Tana yar dariya . Bilkisu ta ce ban son Aunty ki ce min Bilkisu kawai don bana son maigado . Ranar da ki ka kara fada sai na fasa miki baki. Mama ma ta ce. To ai sai a hankali zata saba, mu dai ai ba yanda za ai damu.

Ta dubi Asma'u. 

Auta amso min kwanukan mutanan gidannan in kwashe tuwon nan. Dakuna uku duk da na su hudu sashen Babansu malam mamman kenan matanshi hudu ya'aya ashirin da takwas, don haka kwanukan da Asma'u ta baje gaban Maman mu sai ke ce za'a kaima gidajan layin gaba daya ne, yawancin kwanukan duk sunyi tsatsa da kuma lamba, haka Mamanmu ta ci gaba da kwashe tuwon nan tana zuba ma kowane. Bilkisu ta fito daga daki tana cewa, Mamanmu bari in debo ruwa in kin gama sai na dora ina son na yi wanka. 

Tace, ai fa ke kam ko kwado ya San da zamanki gurin wanks. Dariya tayi sannan ta dauki bokiti zuwa gurin rijiya. Kananan yara sun kai hudu suna wasa da kasa a bakin rijiyar, maza uku mace daya macen mai suna Safiya tana zaune tsakiyar tabon da suka kwaba, rigarta duk koko haka nan fuskarta, kanta rabi a tsefe rabi da kitso. Tsaki Bilkisu taja sannan ta ce da su. Kai Ku ta shi a nan kazaman yara kawai."  Bala dan babba a cikin su ya kalle ta. 

To ina ruwanki dama za ki ce mu ta shi? 

Ta samu kanshi ta dan buga dai dai da shigowar mahaifinsu Malam Mamman. Yace ke ke ke kar ki sake ki duke shi, ki shafa mishi bakin jininki

  Ta dakata. Me yayi miki? Ko zalinci da mugun Abu za ki nakasa min da namiji gashi ke uwarki bata iya haihuwar ya'ya maza ba. Ya ja tsaki kai Bala. { hahahah wai bala dama bala sunane?} Idi, kuzo muje ciki domin zata iya jefa Ku cikin rijiyar nan yan ubanci ba karya ba ne.  Allah ya kyau ta. 

Bilkisu hawaye suka zubo mata, ita dai tana matukar mamakin irin tasanar da dukkan dangin mahaifinta 'yan dai-dai-ku suke yi mata ta dibo ruwan ta dawo, yanda taga fuskar Mamanmu tasan cewa ta ji duk me baba yace mata, don haka ta ce kiyi hakuri Mai gado wata rana sai labari .

Da daddare kwance take kan gadonta, gefenta Asma'u ce tana ta shara barcinta, ita kam ta zurfafa cikin tunanin cukurdaddan al'amarinta, kullum tana tambayar kanta shin me ke faruwa da ita ne? Tana da kyau na gani afada, tana da hankali ta sani domin mutane suna fada, tana da ilimi duka biyu wato islama da na boko. Natsuwa da kamun kai kuwa ba a magana, amma me ya hana ta burge maza? Me yasa ba ta da saurayi?me ya hana wani yace yana son ta? Kuka ya kufce mata Wanda ya zama dan kullum. A fili tace. Meke faruwa ne da nine? Wa zai bani amasar tambayata?  Shin ko Ubangiji bai kaddaro ni cikin wadanda zasu yi aure ba ne? Allah kai kadai ne mafi sani......... Ta daga hannuwanta  Ya Allah Ya Ubangiji halitta kai ne majibancin al'amurana, kafi ni sanin halin da nake ciki, Allah ka zaba min mafi alkairi. Ta maida kai ta kwanta ta soma tuno ita wacece? 

 Uhm sai an jima.

DOWNLOAD BOOK

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post