[Book] Mijina Sirrina Complete Hausa Novel by Ummi A'isha

Mijina Sirrina

Title: Mijina Sirrina

Author: Ummi A'isha

Category: True Life Story

Doc Size: 504KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2020

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya Ummi A'isha mai suna "Mijina Sirrina" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: ~~~ "Oyoyo yaya kabeer...,oyoyo yaya kabeer.."

Wannan shine ihun da yaran dake zaune cikin tsakar gida suna wasa suketa faman yi daidai lokacin da suka ga shigowar matashin saurayin wanda ke sanye cikin farar shadda kansa babu hula sai yar kyakkyawar suma da ya dan ajiye,

Fuskarshi dauke da murmushi ya rungume yaran wadanda akalla zasu kai su kimanin guda hudu.

Daga inda take acikin kitchen ta sake lab'ewa saboda bata son ya ganta duk da sanin cewar dominta yazo gidan, sadadawa tayi ta buya a bayan fridge gamida leka kanta ta window ta yadda tasan bazai iya hangota ba.

Ganinshi tayi rike da hannun Amira da waleeda kannenta sannan ga amir da husna atsaye sai faman jajja masa riga suke suna tsalle,manyan chocolate samfarin coconut chocolate ya debo daga cikin aljihunsa ya mimmikawa yaran.

Sunkuyawa yayi wurin Amira saboda itace babba tafi su husna wayo.

"Amira ina mama?"

"Tana falon abba?"

"Yaya NADIYA fa?"

"Tana kitchen mama tasata aiki.."

Murmushi yayi ya mike saboda yasan aduk inda take taji shigowarsa shiyasa ta gudu ta buya.

Yana rikeda hannun su Amira ya bi hanyar da zata sadashi da falon Abba.

Sai da ya tsaya yayi sallama mama ta amsa ta bashi izini sannan yasaka kai ya shiga cikin falon.

Mama yasamu zaune kusa da abba suna yin hira gefe daya kuma kwanukan abincine da abban yaci kasancewar bai jima da dawowa daga wurin aiki ba.

Su walida da amira na biye dashi har cikin falon sai da suka rakashi ciki sannan suka ruga da gudu suka fita,wuri yasamu ya zauna kanshi a kasa saboda kunya da kuma girmamawa.

Ganinsa yasa abba sakin fara,a tareda mikewa daga kishingiden da yake ya gyara zamansa yana murmushi.

"Kabeeru yanzu kake tafe? Barka da zuwa.."

Cikin jin kunya da sose sosen keya kabeer ya daga ido ya kalli Abba.

"Ehh wallahi abba, shigowata kenan dama nazo ne in gaisheku saboda kwana biyu ban samu damar shigowa ba.."

Murmushi Abba yasake yi ya kalli kabeer din.

"Haba kabeer har yaushene rabonka da gidan, nazaci ai jiyane kawai baka zoba amma ai shekaran jiya ma kazo kodai ka manta ne?"

Maganar da abba ya fadice tasa mama tsoma bakinta tana dan murmushi amma fuskarta babu yabo babu fallasa.

"To ai Alhaji tunda yasaba zuwa kullum jiya kuma baizo ba ai dole yaji kamar yafi sati daya rabonsa damu"

Dariya abba yayi yakoma ya kishingida yana kallon kabeer wanda ya gyara zama yafara gaisar da mama

Shiru falon ya danyi nawani lokaci saboda shi kabeer nauyin mama da abba yakeji yanzu sam baya iya sakewa yayi hira dasu yanzu kamar da.

Ganin yanata zaune shiru sai dai dan lokaci zuwa lokaci abba yana sakoshi cikin zancen da suke yi da mama yasashi mikewa.

"Abba bari naje waje.."

"To kabeer tafiya zakayi?" Abba yafada yana gyara zamanshi.

"A'a ba tafiya zanyi ba waje zanje"

Fita yayi daga cikin falon cikeda kunya, yana fita abba ya dubi mama yana fara,a.

"Nasan dama ba tafiya zaiyi ba wurin mutuniyar tasa zaije.."

Shiru mama tayi batace komai ba saboda ita kwata kwata bata son wannan maganar saboda wani dalili wanda ta barwa zuciyarta ita daya amma idan hali yayi zata bayyanar dashi ga abban shima yaji, ganin taki zancen yasa abba barin maganar ta hanyar shigo da wani zancen daban domin ya fahimci duk lokacin da zaiyi magana makamanciyar wannan wadda ta shafi kabeer da nadiya mama bata bada goyon baya.

 Yana fitowa daga falon abba cikin kitchen yawuce, a bakin kofar kitchen din ya tsaya saboda ganinta da yayi tsaye tana mopping bayan ta kammala share cikin kitchen din.

Yarinyace yar budurwa wacce bazata wuce shekaru goma sha biyar aduniya ba, tanada hasken fata amma ba farace can ba, tana sanye da atamfa kalar koriya dinkin riga da zani, daga inda yake yana iya hango gashinta dake nannade cikin dan kwalin dake daure akanta.

 "Sannu da aiki.." Yafadi yana murmushi har lokacin yana tsaye akofar kitchen din.

"Sannu da zuwa yaya kabeer" tafada ahankali sannan maganar ma tayi tane cike da kunya.

"Yawwa sannu sarki aiki.."

Tunowa da tayi cewar bata gaidashi ba yasata saurin dan rissinawa.

"Yaya kabeer ina wuni?"

"Bazan amsa ba har sai kin jiyo kin kalleni ido da ido.."

Murmushi yasaki bayan ya furta mata hakan saboda yasan ba karamin aiki ya hadata dashi ba domin kunyarshi da takeji bazai taba barinta ta iya hada ido dashi ba.

Jin abinda ya fada ya sata sake sinne kanta kasa tana kallon tiles din dake malale a kitchen din,

"Bazaki gaida ni ba kenan in tafi ko?" Kabeer ya fada har lokacin fuskarshi tana dauke da murmushi.

"To ba na gaisheka ba kaki amsawa" nadiya tabashi amsa tana mai sake juya masa baya dan kar yaga fuskarta.

"Nadiya kenan wai wannan kunyar yaushe zaki dainata ne? Kullum idan nazo sai ki gudu ki buya alhalin nikuma saboda ke nake son zuwa gidan nan, duk ranar da ban gankiba idanuwana radadi da zugi suke yimin, kuma nazo sai ki hanawa idanuwa tozali da kyakkyawar fuskarki? Uhm nadiya? Dan jiyo mana.."

Badan taso ba ta dan jiyo dakyar tana kallon kasa.

"Kinga kyankyaso nan a bayanki.."

Tun kafin ya karasa maganar ta dako tsalle tabar wurin sai gata a bakin kofar kitchen din kusa dashi, dariya ya fara yimata domin dama yasan tana mutukar jin tsoron kyankyaso shiyasa lokuta da dama yake tsoratata dashi.

Ganin yanata dariya yasata gane cewar ba dagaske yake ba.

Fuska ta bata, "yaya kabeer ashe dama tsokanata kake?"

Dariya ya sakeyi ya daga mata gira.

"Wasane matar yaya kabeer.."

Hannuwa tasa ta rufe fuskarta cikeda kunya domin kowa adangi da haka yake kiranta tun tana yar jaririya har ta girma, kowa matar kabeer yake cemata.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post