[Book] Motar Kwadayi Complete by Rash Kardam & Khadija Candy

Motar Kwadayi

Title: Motar Kwadayi

Author: Rash Kardam & Khadija Candy

Category: Love Story

Doc Size: 69KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2016

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya Lubna Sufyan mai suna "AbdulKadir" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: Dukkan yabo, godia da tsarki, Mulki, sun tabbata ga ubangijin Al’arshi maigirma. Sauri2take tafiya, duk da saurin da takeyi, hakan ba zai hana ka gane, cikin nutsuwa ta ke tafiyar ba, sanye take da hijab dinta har kasa, kalo daya zaka mata ka gane yarinyar yar mutumci ne, kuma tana da hankali. 

Kalo na kai duba zuwa ga fuskan ta ba laifi, tana da dogon hanci, gata da yalwan gashin gira, wanda ko da batai ja gira ba, hakan ba zai boye kyan da Allah ya mata ba, tana da yar kamar baki, sai manyan idonta masu fisgan mutum, tana da haske dai2 gwargwado, ko dana kara kalonta, tana da dan zayi san’nan ba za’a kirata da guntuwa ba, ba kuma za’ace mata doguwa can ba, tana da jikin ta dan dai2, abun sai wanda ya gani. 

A hankali ta rinka tafiya, har ta iso gurin masu sai da icce, sallama ta musu, tace baba mai ice aban dami daya, nan ta mika masa naira hamsin, ta zabi mai kyau, wanda tasan zai yi ci, daukowa tayi, ta nufo gida, sauri takeyi don yau basu daura girki da wuri ba, kasan cewan yau Umman ta ke da girki, sauri take har ta iso dan ma dai2cin kofar gidansu, sam bata lura da addah Safiya tana zuwa ba, sai ji tayi sun karo da mutum, ga iccen ya bugeta soaai wani uwar ashar ta narko, Ayshat tuni ta san kame agurin, cikinta ya soma dura ruwa, don ta san yau ta jaza musu kwandon balaâi, bakin ta na bari, tafara Adda dan Allah kiyi hakuri bada sani naaaa.

Ai bata karasa ba ta ji saukar dun’du, a bayarta, Inna safiya ce, tace wato bakin halin ki da na uwarki da kika gado, ya sauko kan tilon yata, yar gwal ko don kunga ku bakin jini ya muku yawa, kin rasa mai tayawa shiyasa za’a sauke akan diyata, to ahirr… Bazaku iya ba, tayi muku nisa, nan takama hannun safiya suka nufi cikin gd, safiya sai wani karai raya takeyi, ita ala dole mai kyau, kallo na tsaya kare mata, ba laifi tana da kyau dai2 gwargwado kuma farace ainun amma ta hada da man bleaching, san nan ga duk wanda yasan kyau, Aisha tafi Safiya kyau ita dai safiya farinta yayi yawa, gashi ta hada da man bleaching. 

Aisha ta dau iccenta, jiki ba kwari ta nufi cikin gd, da sallamarta, tashiga dakunsu, nan ta tarar da ummanta, ta zabga uban ta gumi da sauri tayi gunta idonta fal da hawaye, tace ummah banson kina wan’nan yawan tunanin zai iya jawo miki matsala, wataran sai lbr, kuma duk abunda yayi farko zaiyi karshe, sai da ta tabbatar hankalin umma ya kwanta, ta nufi kitchen don ta musu aikinsu, Aysha kenan yarinya mai hankali da nutsuwa. 

Bayan sallar i’sha aysha na zaune tsakar gida ita da qawarta karima suna fira, Safiya ta fito sanye da wani material riga da saker kayan sunyi mugun kama jikinta ga wani shegen Show ur back daya fitar mata da rabin waya waje sai wani munafikin gyale data dora a kafada ringing wayarta tayi da sauri ta dannan receive ta kara a kunne gani zuwa yanzu.

Ido aysha da karima suka bita dasu tana kashe wayar ta watso musu harara  to kashedi dai wlh nan gani nan bari nafi karfin mutum tsaye da kyau zaune da kyau son kowa kin wadda ya rasa ta karasa maganar tana ya mutsar fuskar Ta nufi kofa tana wani yauki wai ita ala dole ga mai farin jini Ajiyar zuciya aysha ta sauke karima ta kalle tace  tayi abunta banga laifinta ba tana da daraja dan shiyasa a samarukanta baba talaka a kallon tsoro aysha ta mata haba karima ai darajar macce kyau tarbiyarta da kula da kare mutuncinta ba wai tara samari masu kudiba ko saka suturar banza ba dan kinsan duk namijin kirki bazai zo yace yana sonki ba kuma duk wadda ya ganki cikin wannan shigar bazai ga mutuncin kiba karima tace kuma fa hakane dan wani lokacin zakiga yan iskan ma matar kwarai suke nema in suka tashi aure Allah dai ya shirya mu aysha tace amin wannan ai zubarda kimane ( hmmm ina ma yan matanmu zasu gane wannan ba wayeba bane ) Karima ta tashi tana fadin maganar kifa haka take amman fa gamai hankali nikan na tafi aysha saida safe to saida safe karima na gode sai mun hadi school.

Safiya ko tana fita, na hango wata katuwar mota dan nesa da gidansu, wanda garun gidan ya tsufa wani gun ma har ya zube, sai wani yauki takeyi tana karairaya kamar bazata taka kasa ba, bakin nan yaci wani uban janbaki 24hrs, gsky ba laifi safiya tana da kyau, shi yasa yake rudinta take wan’nan rayuwan,( yan mata ina kira gareku da babban murya, kar kuga Allah ya hore muku kyau, ya rudeku ya kaiku ga wata rayuwan da bata da amfani, rayuwa mai cike da nadama acikinta, kusani duk wanda ya hau MOTAR KWADAYI zai sauka, tashar wulakanci, Allah ya kyauta, ya Allah kabamu ikon tsare mutuncin mu da kimar mu, dana iyayenmu, Ameen). 

Ta isa gurin motar nan ta bude kofar ta shiga, ko da na kali na cikin motar matashine baki ne sosai, yana da dan kauri, baya da tsayi sosai, bai wani haduba, in ka kalle shi ka ganta kasan kudinsa tabi, don basu dace ba, Safsey yau kin so ki bata lokaci, cikin yanga da karairaya tace, sorry Mubson na dan tsaya wani abune, yace, kai ya kada don ya san halinta yana cewa zai nuna fushi zata fita a motar, motar ya ja suka bar unguwan. 

Malam Muhammadu da ke nesa yana kallon yarsan, kai ya kada zuciyarsa cike da bakinciki amma bai isa ya tanka ba uwarta zata mishi ba dadi, kwalla ne ya cika idonsa, “mun tausaya masa.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post