[Book] A Sanadin Abayar Sallah Complete by Ummu Maher

A Sanadin Abayar Sallah

Title: A Sanadin Abayar Sallah

Author: Ummu Maher

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Love Story

Doc Size: 74KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuciya Ummu Maher mai suna "A Sanadin Abayar Sallah" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu complete dinsa.

Book Teaser: *Gidan Malam Tahir*

Salma yarinya ce mai hankali kowa a unguwarsu ya santa da hankali da hangen nesa, sai dai a gefe d'aya kuma Salma na da wata gur b'atacciyar k'awa mai suna Zuly wato Zulaihat, ta tura mata wata gur b'atacciyar a k'ida na cewa matuk'ar saurayin ta bai yi mata a bayar Sallah ta kece raini ba to ta rabu dashi tayi mai wulak'ancin da wani saurayi ba zai k'ara zuwa wajenta ba.

*GIDAN HAMISU*

Hamisu yana da mata kwaya d'aya mai suna Zeenat, Zeenatu dai bata tab'a haihuwa ba shekarar ta takwas, Amman hamisu bai tab'a yi mata gorin rashin haihuwa ba yana kula da i'ta dai dai k'arfinshi, Amman ita a b'angaren Zeenat ba haka yake ba domin i'ta Zeenatu gidan ta gidane na tara jama'ah ko wani kare da kiyashi kullum yana gidan, A saboda haka ne kullum Zeenat da Hamisu suke fad'a Saboda yayi_yayi tara mishi mutane tak'i a cewar ta wai i'ta ta Al'umma ce kuma ta jama'ah ce,  don haka tare ya gansu i'ta ba za ta daina tara jama'ah ba.

Also Download: Silar Fyade Complete by Ummu Maher

Kwatsam wata rana ta tara y'an mata da matan Aure, da  zawara , kawai sai wata mai suna Hauwa"tace Hmm kai ku tsaya kuji wani labari🤔 daya shigo mana kwana nan  wai wannan Sallar yayin a baya za'ayi ta kece raini, nidai har mai gidana ya siyomun don ni kun san bana wasa da duk abunda ake yayi idan ba haka ba sai kaji a layi da cikin dangin ka ana gulmar ka ana cewa kai kullum kayan da kake saka wa baka saka na yayi, shiyyasa na dage akan saiya siyamun don nima in kece raini don ance baka yi bani waje.

Salma ba tana jin haka i'tama ta d'orawa kanta dole dole saita saka abayar nan da akace sai anyi yayin ta da Sallah, don haka Hamisu yana dawowa ta saka mishi kuka akan cewa dole i'tama saiya siya mata abayar Sallah, Hamisu yace indai baifi k'arfinshi ba zai siya mata, Hamisu yace wa Zeenat ta tambayo kud'in.

Nanfa Zeenat ta kama murna, ta saka azuciyarta sai da safe zata tambayi Hauwa nawa aka siyo mata abayar Sallar ta don itama a siyo mata.

*Sai a shafi na gaba zaku ji yadda abun zai kaya don gane da gidan Malam tahir da Gidan Hamisu*

DOWNLOAD BOOK{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post