[Book] Shi Kadai Nake So Complete Hausa Novelby Beely Badaru

Shi Kadai Nake So

Title: Shi Kadai Nake So

Author: Billy Badaru

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Love Story

Doc Size: 192KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuciya Beely Badaru mai suna "Shi Kadai Nake So" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu complete dinsa.

Book Teaser: Bismillahir-rahmanir-rahim_ *Wannan littafin nawa qagaggen labari ne banyi don cin xarafin wani ko wata ba, idan yayi dai dai da labarin rayuwarka ka gafarceni, kuma kar wanda ya juya min labarina ta wata siga, wanda yayi hkn na barsa da Allah...

Kallon juna suke cike da so da qauna,kai da ka gansu xaka tabbatar da cewa su masoyan juna ne na ainihi. Ita ta soma sauke idonta daga kallon da sukema junansu, sannan ta dago tare da cewa "*Habeeby* ina sonka fiye da yanda nake son kaina, bana tunanin xaniya rayuwa ba tare da kai ba, kaine majinginin rayuwata idan ka matsa rayuwata gaba daya rugujewa xatayi".

Dagowa yayi shima ya kalleta cikin so da qaunarta da suke yawo cikin jinin jikinsa sannan yace "*Habeebty* sonki a cikin jinin jikina yake, soyayyarki wani bangarene mai mahimmanci a rayuwata, cireshi a cikin xuciyata abu ne mai wahalar gaske, ta yaya kike tunanin xan iya rayuwa babu jini a jikina? Ta yaya kike tunanin xan iya rayuwa babu xuciya a jikina? Cire sonki a raina ba abune mai yuwuwa ba, don kuwa idan har aka ce xa'a cireshi ai dai a debe duka jinin jikina domin kuwa sonki a cikin jinin jikina yake yawo". Lumshe ido ta tayi cike da jin dadin kalamansa, haqiqa sunyi nisa a soyayyar junansu, rabasu abune mai wahalar gaske. Bude baki tayi da nufin yin magana sai ji tayi an fincikota ta baya, waigawa tayi da sauri don ganin ko waye, gabanta ya fadi ganin Abbantada tayi tsaye a gabanta fuskarsa daure kamar wanda aka aikoma da saqon mutuwa. 

Jikinta ne ya dauki kyarma, durqushewa tayi a gabansa hawaye har sun soma xarya a kumatunta, shima durqushewar yayi cike da jin tsoron abinda Abba xaiyi masu. 

Wani wawan mari Abba ya watsa mata, a gigice ta dafe kuncinta don har wasu taurari ta gani shima da hanxari ya dafe kuncinshi don ji yayi kamar shi aka mara don yaji xafin marin har cikin xuciyarshi.

Cikin bacin rai Abba yace"*KHADEEJAH* ni xaki maida qaramin mutum? Ni xaki kunyata? Ke har kin isa in yanke magana a kanki ki bijiremin? To bari kiji in fada maki ko xaki mutu baxaki auri wannan yaron ba auren xumunci xakiyi kamar yanda kowane dan'uwanki yake yi". 

Ya waiga ya kalli saurayin da har lokacin bai sauke hannunshi daga dafe kuncin da yayi ba, yace " Kai kuma ban gargadeka ba akankar na sake ganinka da diyata ba? Karka kuskura na sake ganinka da ita idan ka bari hakan ta faru......" Yayi kwafa, sannan ya juya ya fara tafiya canya waigo kuma ya kallesu sannan yace"Ki tabbatar da kin shigo gida cikin secon biyu".

Da sauri ta miqe ta qarasa gabanshi ta durqusa tare da hade hannayenta biyu guri guda sannan cikin muryar kuka tace " Abbana na roqeka da Allah kayi hkr kayi min rai karka rabani da *AHMAD* wllh shine rayuwata baxan iya auren kowa b in bashi ba, *SHI KADAI NAKE SO* zuciyata tarwatsewa xatayi Abba idan har ka rabani dashi". 

Wani dogon tsaki yaja ya tare da yin ball da ita yace "Ah lallai dole xakizo ki tasani ki ri qa gayamin magana n ranki, to bari kiji in gaya miki dolenki ki amshi auren xumunci kamar ynd yan uwanki suka amsa, daga rana irin ta yau bake ba Ahmad kinji na fada miki". 

Jin hakan yasa Ahmad yayi saurin qarasowa wajen Abban shima ya durqusa gabanshi tare da cewa " Abba don Allahkarka rabani da Khadeejah wllh *ITA KADAI NAKE SO* Abba meyasa kake neman ruguxa mana rayuwarmu, Abba don Allah kayi hkr ka barmu mu auri junanmu".

Banxan kallo ya watsa mashisannan ya shige cikin gida. Ahmad har ya fara xubar da hawaye, da sauri Khadeejah tace "Ka daina xubar da Hawayenka Habeeby, xuciyata quna take a duk sanda naga hawayenka na xuba".

DOWNLOAD BOOK

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post