[Book] Taimiyyah Complete by Ayshat Dansabo Lemu

Taimiyyah

Title: Taimiyyah

Author: Ayshat Dansabo Lemu

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Fiction

Doc Size: 228KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuta Ayshat Dansabo Lemu mai suna "Taimiyyah" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu cikin sauki.

Book Teaser: Matashiyan budurwace kwance ƙudundune cikin bargo,jikinta na faman kakkarwa alamun zazzaɓi ne yai mata kamun me kyau,daga gefenta wata dattijuwa ce wacce shekarunta ya fara nisa sosai,don a ƙalla zatai shekaru sittin da biyar zuwa sama,farace tas dattijuwan me tsagen kalangu a fuskanta hagu da dama,kyakykyawace wanda a kallo ɗaya zaka zaci cewa bafulatana ce,sai dai ba hakan bane bahaushiyace ziryan,wanda ubangiji ne kawai yai mata baiwan kyau da farin fata,hannu takai tana janye bargon da budurwan ta ƙudundune aciki,cikin muryan da ke nuni da tsananin kulawa take faɗin "Tashi TAIMIYYAH ki ƙoƙarta kiyi wanka ko zaki daina wannan rawan sanyin,idan kin karya yanzu sai Sani yazo ku koma asibitin watakila waɗannan magungunan kaɗai bazasu wadatar da ke ba sai an haɗa da alluran dai da ba'a so."

Ta ƙare maganan tana ƙarisa yaye bargon da budurwan ta rufa dashi,nan take kyakykyawan fuskan budurwan da aka kira da TAIMIYYAH ya bayyana,tare da jikinta baki ɗaya wanda take sanye da rigan bacci Ash colour me kauri sosai,kamanninta da tsohuwan daya bayyana sosai zai baka tabbacin idan ba ƴarta bace to akwai alaƙa ta jini me ƙarfin gaske dake tsakaninta da dattijiyan matan,abinda kawai dattiyan zata nuna mata shine fuskan manyance ,amma hatta farin fatan nata irin na Dattijiyan ne,TAIMIYYAH ta yamutse kyakykyawa fuskanta tana sake lumshe manyan idanunta,muryanta can ƙasa dake ɗauke da ƴar shagwaɓa take faɗin "Wash! Allah Iya baki ji kaina ba kaman zai cire wallahi."

Iya ta dube ta cike da tausayi da kulawa tana faɗin "Sannu kiyi haƙury zai bari,yanzu tashi ki shiga wankan na haɗa miki ruwan ɗumi sosai da zakiji daɗinsa,Allah ya baki lafiya TAIMI na."

Budurwan ta amsa da "Ameen." Tana miƙewa tsaye da ƙyar sai lokacin na kula da cewa tana da tsayi dai-dai misali wanda bai cika yawaba,sam bata da jikin ƙiba sai dai jikin a murje yake cike da tsoka da cikan halitta me ɗaukan hankali,ta sake lumshe manyan idanunta sabida ciwan da kanta keyi,kafin a hankali takai hannunta na hagu ta dafa guiwan ƙafanta na hagun tana me fara takawa zuwa toilet ɗin dake manne cikin ɗakin,Dattijiya Iya tabi bayanta da kallo ƙaunar budurwan da tausayinta na sake ratsa ilahirin jinin jikinta,tana matuƙar tausayin TAIMIYYAH sai dai ko kaɗan ba ta nuna mata cewa nakasan da ta samu na ƙafa yana damunta domin ita kaɗaice a kullum take ba TAIMIYYAN tabbacin haka ubangiji yaso ganinta,tashi tayi tana me ficewa daga ɗakin mintoci kaɗan ta dawo ɗakin hannunta ɗauke da Mug da ta ciko da zazzafan Kunun gyaɗa da yaji madara sabida sanin TAIMIYYAH na matuƙar son sa,dai-dai lokacin da TAIMIYYAH ta fito daga toilet,tana ɗaure da ƙaton towel da tsayinsa ya sauka har zuwa guiwanta,ƙafafunta nabi da kallo wanda na lura ɗaya ya sirance ɗaya kuma lafiyayye,ta yadda ruwa ke gangara a jikinta kaɗai zai baka tabbacin Allah yai mata baiwa da sulɓin fata,taiwa Hajiya Iya kallo ɗaya tana sakin murmushi,a hankali ta ciga da dafa ƙafanta na hagu tana takowa zuwa cikin ɗakin,da alamu wankan da tayo yasa ta fara jin daɗin jikinta,Iya ta ɗaga kai ta dubeta tana faɗin "Sannu kinji daɗin jikin  ko? ga kununki nan saiki daure ki farasha kafin Ladi ta gama soya miki dankalin."

TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta masu haske ta dubi Iya,cikin sanyin muryanta me daɗi take faɗin "Naji daɗi Iya nagode da kulawa,amma ina ga abar dankalin wannan ɗin kaɗai ya isa,amma zuwa anjima don Allah ki min faten tsaki da kanki irin wanda kikeyi yayi ɗan tsamin yakuwannan shi kawai nake son sha." Ta ƙare maganan da shagwaɓa sosai a muryanta."

Hajiya Iya tayi murmushi me faɗi tana faɗin "To shikenan baki da damuwa za'ayi insha Allah,yanzu dai sha kunun ki sha magungunan,sai a sake kiran Sanin ku koma asibitin,ki tafi da duka magungunan sabida su gani ki kuma buɗe baki kiyi magana agaban likitan bana son wannan miskilancin naki idan kina ciwo ki ƙi magana."

Hajiya Iya ta ƙare maganan da mita,wanda hakan yasa murmushi me faɗi suɓucewa daga face ɗin TAIMIYYAH wacce ta kammala shafa mai tana ƙoƙarin saka rigan da ta ciro,ba tare da tayi magana ba har Iya ta fice ta sanya doguwan rigan atamfa Red wanda akaiwa adon zanen manyan Flawer da milk and black,yayi mata kyau sosai tare da haska kalan skin ɗinta,bata shafa komi a face ɗinta ba sai lip balm me taushi,qamshin Body mist datai anfani dashi ne ya cika ɗakin baki ɗaya domin ita ɗin ma'abociya son qamshi ce na ajin ƙarshe,zama tayi tana ɗaukan Mug ɗin da Iya ta aje tana fara shan kunun ahankali cike da nutsuwa,magungunan ta sha bayan ta shanye kunun,wani zufa ta fara ji na keto mata hakan yasa ta miƙe tana ƙara ƙarfin gudun Fan ɗin dake aiki a ɗakin,tsaye tayi gaban dogon mirrow ɗin ɗakin tana kallon fuskanta da ya rame sosai a kwanaki biyu kacal da fara ciwan nata,sai fararen manyan idanunta ma'abota haske da ɗaukan hankalin mai kallonta,domin wasu irin idanu Allah yai mata baiwansu masu ɗaukan hankali,ƙirjinta ta kalla tana me waro ido waje ganin cewa ta manta bata sanya Bra ba,gashi fita zasuyi sam bazata iya fita babu shi ba,sabida Allah yai mata baiwan cikar ƙirji,sai dai bawai irin sunyi girman da har suka rankwafa bane,kawai dai bata iya fita haka babu Bra dake tare su ajikinta,wannan sabo ne dataiwa kanta tunda ta isa sanya Bra ɗin,don haka kai tsaye wajen da take aje su ta nufa ta ɗakko tana sauke zip ɗin riganta zuwa ƙasa ta sanya,wayanta dake aje bisa gado ya fara ringing,sai ta nufa wajen don ganin me kiran,ganin sunan Sani ya bata tabbacin yazo kenan,ta ɗaga wayan tana gaida shi tare da bashi tabbacin fitowanta yanzu.

"Iya ga Sanin can ya iso zamu wuce."

TAIMIYYAH ta faɗi hakan tana kallon Hajiya Iya dake zaune saman ɗaya daga cikin kujerun da suke qawataccen falon nata,Iya ta ɗaga kai tana sauke ganinta akan TAIMIYYAH da ke sanye da dogon Hijab kalan Red da yai mata kyau sosai,ta saki murmushi tana faɗin "To sai kun dawo ki kula ki kuma buɗi baki agaban likitan bana son wannan miskilancin naki,kice ma Sanin idan kun dawo ya shigo ina son ganin sa."

TAIMIYYAH ta amsawa Iya tana miƙewa hannunta ɗaya riƙe da ƙaramin hand bag da ta sanya magungunan da aka ɗaurata akai,ɗaya hannun na dafe da guiwan ƙafanta na hagu,wanda ke bada tabbacin sai da taimakon dafa guiwan shanyayyen ƙafan take iya takawa tana tafiya,a dukkanin cikar halittan ta babu inda ke da naƙasu sai wannan ƙafan na hagu daya shanye ya silance,kyakykyawace da ta mallaki duk wani cikan halitta me ɗaukan hankali,ahaka ta dinga takawa har ta fice daga falon Hajiya tayo waje,idanunta suka shiga ƙarewa haraban sasan Iya kallo kaman me son gano wani abu,kafin ta cigaba da takawa bisa tsarin yadda ubangiji yaso tafiyan nata ya zamo ahaka har ta fito daga sashin Iya baki ɗaya,ta iso ainihin haraban gidan me ɗauke da part guda biyu duk da na Hajiya Iya ne cikon na ukun,tafiya ta cigaba dayi zuciyanta na karyewa a lokacin da idanunta ke hango mata matar da ta fito daga ɗaya part ɗin,bayan matan wani matashi ne ke biye da ita riƙeda da wata ƙatuwar leda a hannunsa,TAIMIYYAH tayi saurin yin ƙasa da kanta tana cigaba da tafiya har ta iso dai-dai inda Hajiya Shuwa suke tahowa,hakan yasa TAIMIYYAH dakatawa daga tafiyan tana jiran ƙarisowan Hajiya Shuwan wacce suke kira da Umma,matar wan mahaifinta ne wacce taiwa TAIMIYYAN wata irin muguwan tsana.

"Ina kwana Umma."

Sune kalmomin da suka fito daga bakin TAIMIYYAH a lokacin da su Umman suka iso suna shirin gitta ta su wuce,sai dai gaisuwan da ta aikawa Umman yasa Umman dakatawa tana zubawa TAIMIYYAH ƙananun idanunta,fuskanta babu ɗigon fara'a ko kaɗan,tai mata wani malalacin kallo memakon ta amsa gaisuwan TAIMIYYAN sai cewa tayi "Ikon Allah su gurguwa kenan ance baki da lafiya,ke kuma haka Allah ya yoki irin jaraba ga nakasa ga yawan ciwo da wanne za'aji? kuma a hakan ake so wani yazo yace zai kwashi jaraba,ga gurgunta ga yawan cuta kaman sikila,to mu dai kurwan mu kur kada arasa me so ace wataran za'a cinnama lafiyayyun ƴaƴan mu gurguwa raguwan cuta."

Ta ƙare maganan da jan tsaki tana yin gaba abinta bayan ta kalli ɗan lelen ɗan nata ta maka masa harara tare da yi masa sign da ido alamun ya shige gabanta,ba tare da ta kuma kallon TAIMIYYAH da tai ƙasa da kai zuciyanta na shiga wani irin ƙunci mara misaltuwa ba,manyan idanunta tuni sun fara tara hawaye, ciwan kan da take riritawa taji ya dawo sabo,cikin ɗan hanzari ta dafa ƙafanta me laluran ta fara cigaba da tafiya,sai dai taku biyu tayi taji sassanyan qamshin turaren BENTLEY na isowa hancinta,kaman yadda kafin tayi wani yinƙuri yayi saurin tare gabanta,manyan idanunsa masu kama da nata ya sauke akanta,wani abu na yawatawa cikin maƙoshinsa,cak! TAIMIYYAH ta tsaya still bata ɗago face ɗinta ba don qamshinsa ya gama bata tabbacin ko waye domin kaf gidan shi kaɗai ne mamallakin irin wannan turaren me qamshin da ke kashe jikinta, amon muryansa me cike da ginshira taji cikin kunnuwanta yana faɗin "Kiyi haƙury Sis da halin Umma please! watarana sai labari ko kaɗan bana so kisa wani damuwa a zuciyanki haka Allah ya halicceki kuma yaso ya ganki, mu da ita babu me halitta haka kuma babu wanda isa ya sauya halittan wani face wanda yayisa,ya jikin naki?"

Ya ƙare maganan da jefa mata tambaya,hakan yasa TAIMIYYAH yin jarumtan maida ƙwallan da suka cika idanunta,sai dai duk yadda ta so ɓoye halin da zuciyanta ke ciki ƙaramar zazzaƙan muryanta dake rawa ya fallasata,cikin sanyin muryan da ke kashe zuciyansa take faɗin "Naji sauƙi Yah Sadeeq zazzaɓin ne yaƙi tafiya shine yanzu zamu koma wajen ganin likita,ina kwana dafatan mun tashi lafiya."

Ta ƙare maganan da gaida shi tana me ɗago manyan idanunta ta sauke akan face ɗinsa,sai dai ganin ita ɗin yake kallo yasa ta sake ƙasa da kanta,tana jin yadda idanunsa ke cigaba da yawo akanta,kafin ya furta "Okey! Allah ƙara lafiya yi maza kije tunda yana jiranki zuwa anjima zan shigo sasan Iya sai muyi magana,take care Angle."

Ya ƙare maganan da wani karyayyen sauti daya motsa zuciyan TAIMIYYAH,hakan yasa ta gyaɗa kanta tana lumshe idanunta da buɗesu lokaci guda ta cigaba da takawa zuwa parking space inda take hango motan Sani,ya bi bayanta da kallo tausayinta da matsananciyan ƙaunarta na sake kassara zuciyansa.

Ko da TAIMIYYAH ta isa wajen motan Sani baya ta buɗe ta shiga don tana buƙatan kwanciyane sabida yadda kanta ke sarawa,sam baiyi ƙorafi ba domin matsayin driver yake bashi da damuwan duk inda zata zauna ɗin,sannu yai mata yana tada motan bayan TAIMIYYAH tayi ƙarfin halin amsa masa,zuciyanta na mata bitan baƙaƙen maganganun Umma wanda inda sabo yaci ace ta saba da yadda Umma ke kyaran halittan ta da kushe nakasanta tamkar itace tayo kanta a hakan,ba haka Allah yaso ganinta ba, hawaye masu ɗumi suka silalo mata ta kai hannu ta share tana son ƙarfafa zuciyanta kaman ko yaushe,don ganin maganganun basuyi tasiri a zuciyanta sosai ba,sai dai har suka isa asibitin ABU da ke zaria zuciyanta babu daɗi,zuciyanta ya sake nauyi tana tambayan kanta wai har sai yaushe ne zata daina fuskanta gorin halitta da cin fuska daga wasu cikin ahalinta akan yadda Allah ya yota? da ƙyar ta lallashi kanta ta samu ƙwarin guiwan shiga cikin asibitin don ganawa da likita.

A ƙalla ta shafe kusan awa guda kafin ta fito tana faman liliya inda akai mata alluran,domin bayan dukkanin bayanai da taiwa likitan sai ya sanar da ita dole ta amshi allura guda uku wanda zaa jera yi kullum guda ɗaya,ba don rai yaso ba ta amince domin allura na daga cikin abinda family ɗinta suka tsana akira za'aiwa ƴaƴansu tun bayan laluran data samu TAIMIYYAN wanda ta sanadin allurance ta samu wannan nakasan na shanyewan ƙafa ɗaya,wanda hausawa ke kira da shan inna wanda kuma take fuskantan ƙalubale me tarin yawa daga ƴan uwanta da wasu baren daban ma,kai kace itace ta janyowa kanta laluran da kanta ba Allah ne ya ɗauro mata ba.......

Hello! my people gani da sabon salo sabon tafiya irin wanda Ɗansabo bata taɓa zuwa dashi ba,labarin TAIMIYYAH labari ne mai cike da ban tausayi, haɗi da darasi me tarin yawa ga zallan ƙauna da soyayya me motsa zukata,kada ki bari abaki labari a wannan karon kowa ta ƙoƙarta ta mallaki nata akan fara shi me sauƙi da zan faɗi nan gaba kaɗan,ku dai ku cigaba da bibiyata a shafukan da zasu biyo baya don jin ya rayuwan TAIMIYYAH zai kasance.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post