[Book] Yar Aiki Zan Aura Complete by Sulaiman Lawan

Yar Aiki Zan Aura

Title: Yar Aiki Zan Aura

Author: Sulaiman Lawan

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Love Story

Doc Size: 67KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuci Sulaiman Lawan mai suna "Yar Aiki Zan Aura" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu complete dinsa.

Book Teaser: Haba Naseer wannan Qanwarkace fa meyasa kake mata haka''?

'''Momy kiduba fa kullum saita dameni da surutu wai nakawo mata Auntyn ta ''

 ''to ai gaskiya take fad'a muma nan munzura idanu ne kawai nida abban ka mugani idan bakaza'ba ba muzamu za'ba ma ''

...tunda duk 'yen warinka sunyi aure kai kad'ai karage ''walhi momy harda za'bi nayi mai cikin classmate d'inaa ga k'awata nan Fiddausytana sonshi kullum saita yimin maganarshi '''tabani sak'o amma ya watsar''

''..keyimin shiru kemeyasa bakyayin auren ''?

ai yaya don kasan ban isa aure bane dakaga soyayya ''''dukansu dariya sukasa shiyafice waje yana shafakan shi motor parking space yanufa ....

......moter mai k'irar jeep bak'a mai bakin glass yashiga nanda nan maigadi yawangale mai gate tarda mika gaisuwa naira dari biyar yamikomai ta glass sannan ya ba motar shi wuta yayi gaba ''

..driven yake cikin natsuwa hankali kwance yana sauraren kidan dake tashi ''wayarshi ce fara ringing yad'aga tareda kai dubanshi ga sunan dake yawo akan screen '''SugerDadyyagani hakan yasa yad'aga ciki hanzari tareda karawa akunne ''

....hello dad ka'isone ..??

.'A'a son kawai kashirya kamin lokaci yayi zuwa 3:30 may be jirginmu zai sauka '''daga d'ayan 'bangaren ake maganar '''

'ok dady Allah yasauke ku lapiya ''

''Amenn son ''

''Amma dady dafatan baka manta da alk'awarin ba''

ya fad'a yana 'yer dariya ''

''Dady ya katseshi...

Ai ba kaitsaye zan cikama alkawarinka ba''daman ya mukai dakai sai ka nuna min surika ta ko "

'..ehh dady amma ai...

Bai karasa abinda zai fad'aba ya katse shi''

..kai yanxudai saina iso''ok dad Allah yakawo lapiya ''

''Ameen 

Katse wayar yayi yana murmushi tareda fad'in wai aure bayanzuba dady saboda banga wacce zata zama abokiyar rayuwa taba''

''cigaba da driven yayi harya iso daidai wani k'aramin gida'' gidan zamani mai d'auke da kayan alatu babu kaiwaice babu ciki komai akwai na more rayuwa''

Horn yayi maigadi yabud'e masa gate yagaidahi saboda yasanshi kusan kullum saiya zo gidan ''parng yayi yafito''oyo''oyoyooyo wata karamar yarinya ce wacce bazata wuce shekara hud'u 4 ba ta taso aguje daga wajenda na hangi wani babban mutun maijiki babba dashi

Yana sanye da medical glass a fuskarshi yana karatun jarida TodayNewsdake hannunshi..

    ..

''Oyo ''Yaya Naseer ''Durkusawa yayi tareda rungumota akafad'ar shi yana fad'in weldon my sweetsistr kintashi lapiya ''??""

Ehh yaya ur welcome 

''thnks yace mata tareda shado gashi kanta ''yayan ki yana ciki ''??

ehh'

''Bara nagaida Abba mushiga ciki ''tashi yayi daga durkushen da yake''yanufi wajen Abba ''Sallama ya isa wajen Abba ya amsa cikin fara'a  da murna '

Yau Naseer ne agidan ''?

ehh Abba aiko jiya nashigo baka nan ''ok toya gidan ku ya mamarku ''lapiya qalau suke Abba ''

Alhjinku bai sauka ba ko ''??

ehh amman yanzu munyi waya dashi inda yake gayamin zaishigo zuwa maraice ''

ok Allah yakawoshi lapiya ''

Ameen

'''Mikewa yayi tareda fad'in Abba zanshiga ciki nagaida su mama nafito ''ok Naseer afito lapiya ''

 .......Zaune suke a paluor mama da ''Tagwayen 'yen matan ta biyu Ummu Salma da Ummul kheiri  Wad'anda shekarunsu baza su wuce sha'akwas ba '' a kewaye da ita sun kurawa makeken T.vn dake mak'ale a jigin bango idanu suna kallo...

'Sallamar dayayi ce tasaka sudukan su suka juya da dubansu wa kofa ake sallama don ganin waye''da gudu salma tatashi zuwa gareshi tareda amsar sallamar itama kheiri oyooyoo oyooyo ya Naseer sannu dazuwa ''yauwa sannuku dai ''

Waje yasamu yazauna yadurkusa har kasa yagaida mama kowa sai murna yake kamar yaune farkon zuwanshi gidaan '...

Naseer yasu Hajia da k'anwarka  ..?

kowa lapiya mama '''momy yace tana gaidaku kuduka baki d'aya 

sannu dazua lafiya mama '''

..ciki suka shiga suka barshi nan zaune'' ba afi minti 3uku ba ''kheiri ce tafito da plate a hannun ta d'auke da cup biyu da freshmilk da sam water ''

A hannunta yaya ga wannan nasan kana bukata ta aje saman karamin robber centre dinning table dake tsakiyar palourn murmushi kawai yayi mata itama tamaidamai ....

Saurin d'auke kanshi yayi saboda baya iya juree wannan murmushi aduk lokacin da tayimai wannan  murmushin sai yaji  kamar kada ta daina harma zai iya fita daga hayyacinshi ''

Durkusawa tayi agabanshi tareda 'balle gorar freshmilk tazuba mai a d'aya cup ta mikamai ahannu yakar'ba yafara sha ''''saiga Salma tafito daga cikin kitchin da nata plate a hannu ..

''Da foodplast karami ta girke aganshi ''abin dariya yabawa Naseer 'waiku koso kuke kukashe nine da abinci saida na koshifa sannan nafito daga gida 

Dariya sukayi sudu ka harda mama da bata damu da lamuran suba saima yanzu tayi dariya hankalinta na kan T.v ..

Ai ya Naseer  bahaka bane yazakazo nan gidan ka koma bakaci komai ba ''cewar salma tana 'yer dariya da har yanzu ke abakinta

'''Ya Naseer gaskiya saikaci kakoshi bamu yarda ba ai nan gidan kune ''

kedai sweetsis. barshi kawai ''kojiya haka yayi mana ''cewar salma 

'Naseer dariya kawai yake yau za'a mai d'uren abinci ''

Mama ce tatashi zata shiga ciki ''to Naseer zanshiga ciki ''cewar mama to mama bazaki tsaya ba kirabani da wad'anna yaran ..?

dariya kawai tayi tana fad'in gaka gasu ai kunsaba tahaye sama ''.

'''to kudakata zanci amman da sharad'i baduka zanci ba cokali biyu kawai zanyi nabari hakanan ''A'a gaskiya Ya Naseer kaci ko rabine ''cewar kheiri

   ..

a'a kicedai naci har yafito min..

haka dai suka tusashi gaba saida yayi cokali goma shabiyar15 dakyer suna dariya ''

To naci na sha saime kuwa kubari naje wajen wanda nazo gunshi ''ina yayanku ''??

......yana ciki may be ma bacci yake ''cewar salma 

  A'a ya tashi yanzunnan najishi yana waya '' cewar kheiri''

  Tashi yayi yanufi sama sukuma suka kwashi kaya zuwa kitchen''

''tsaye yake sanye da riga da wando bakin wando da farar t.shirt yana shace kanshi da waya makale tsakanin kafad'ar shi da wuyanshi yana magana daidai shigowar Naseer d'akin yake cewa sai anjima nagode saina sake kira ''thks

    .....Naseer ya hango tacikin madubin dake gabanshi yana tsaye abakin kofa yagame hannu biyu a kirjinshi sai murmushi yake ''yajuyo yakalleshi tareda cewa kagama soyayyar ko''cewar Ya Isma'eel

''''Soyayya dawa kuma 'Naseer yatambaya tareda 'bata fuska amalur rashin fahimta

Soyayya da 'yen matanka mana tunda ka kasa za'ba Salma ko Kheiri'' uhm kaida dazenka ''aikai kake soyayya dawa naji kana waya yanzunnan ''??Naseer ya tambaya yana 'yer dariya 

DOWNLOAD BOOK{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post