[Book] Yar Gidan Tsohuwa (Deejamah) Complete by Ummu Safwan

Yar Gidan Tsohuwa

Title: Yar Gidan Tsohuwa

Author: Ummu Safwan

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Love Story

Doc Size: 251KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuciya Ummu Safwan mai suna "Yar Gidan Tsohuwa" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu complete dinsa.

Book Teaser: Cikin sand'a tashigo cikin zauren gidansu, tana wasar b'uya, ita da k'awayenta

Lab'ewa tayi tasha jinin jinkinta kamar wacce tayi k'arya, tana tafiya a hankali yanda baxaka iyajin sautin takun k'afartaba."

Gafda zata shiga cikin gidan ne

Saiji tayi   taci karo da wani abun,a gabanta."

 turus tayi,

Taja ta tsaya gefe d'aya tana turo baki  kasan cewar zauren gidan duhu ke gareshi,

Ta d'auka *Kaka* ne, kaka Kwaishi da fitinar tsuha,

Tashiga gunguni tana magana k'asa k'asa, " kai wannan tsohun kacika rigima yazaka taka min k'afa, idan kuma akace da kai ka kusan mutuwa, ka d'ora hannu a kai kace kai  ba yanzun zaka mutuba."

Shuru taji anyi  Bataji antanka mata ba."

Dogon tsaki taja harda d'an murgud'a baki taci gaba da tafiya

zata shiga cikin gidan kenan taji ta kuma taka k'afar mutum a karo na biyu."

Jikinta ya soma rawa fitsari ya fara d'iga a wandonta, saka makon marin da taji an kwad'a mata a fuska."

Wata irin k'ara tasaki ta fad'i k'asa tana birgima, "Wayyo idona na shiga uku tsohuwa kizo ki ceceni." 

Mahmud dake tsaye cike da takaicinta, yace "Ke wace irin yarinya ce,wadda bata kallon gabanta, tunda kika shigo soron gidan nan naketa k'ok'arin naga na kauce mki amma duk da hakan saida kika taka min k'afa."

Oh kin d'auka *kaka* ne da kike fad'awa magana yanda kikaga dama?"

 to bashi bane  ni kika tak'ewa k'afa, wawuya kawai marar hankali wadda bata kallon gabanta bare bayanta,

 Ni maganin rashin kunyarki zanyi  kafin na bar  gidan nan."

Tsohuwa dake sallah, 

 Sallamewarta kenan taji sautin kukan Dije a zaure."

Da sauri ta mik'e tsaye tafito daga d'akin tana fad'in "deejama wani mugunne  ya dakeki?"

Ai kuwa deejama najin muryar tsuhuwa ta kuma bud'e baki had'ida sanya hannu d'aya ta dafe b idonta d'aya, "wayyo idona nashiga uku tsuhuwa idona ya tsiyaye."   

Mahmud tsaye yayi ya  tsura mata ido yana kallon ikon Allah, k'azafi takeso tayi mashi yanaji yana gani."

Ta mik'e tsaye dafe da ido sai kuwa takeyi tana tsalle tana fad'uwa, sai da tazo dafdashi ta kuma taka masa k'afa da k'arfi 

 ta xuba a guje tanufi wurin tsohuwa dake tsaye a k'ofar d'aki tana ruwan masifa."

Tanufi wurin tsohuwa tana fad'in "wayyo idona tsohuwa ki taimakeni yaya muhmud ya tsiyayar min da ido d'aya."

"Tsohuwa tace "burinka ya cika mamuda ka tsiyaye mata ido d'aya saika zuba ruwa k'asa kasha,

  Ni wlh bnsan irin k'iyayyar da kakeyiwa deejama ba, 

kwata kwata baka k'aunar ka bud"e ido ka ganta tana walwala a gida ko a waje."

Tunda burinka ya cika ka makantar da ita, saikazo ka kwashe kayanka ka koma gidanku. Mungode da ziyarar Allah amfana."

Muhmud da zaifita, jin k'azafinda dijana tayi masa yasashi dawowa ya fasa fitar.

Yace "Allah tsohuwa ki daina biyewa wannan yarinya, kwata kwata batajin magana kuma batada kunya. Tun da nazo garin nan kullum sai ankawo maki k'arar dijama, amma kullum sai d'aure mata kikeyi bata laifi."

"Saboda kana jin zafinta shiyasa ka tsiyayar mata da ido d'aya?"

   Tafad'i hakan had'ida kamo dijama dake gefenta tsaye  kamar ta shige mata a ciki dafe da ido d'aya."

Ta janye hannun deejama daga kan idon nata tana fad'in naga idon naki dije, idan ta kama mutafi asibity sai na kira ubanshi duk inda yake yazo ya d'aukemu ya kaimu asibitin."

Ganin babu abunda idon nata yayi, tsohuwa ta kuma kallon muhmud dake tsaye gefe d'aya yana kallon ikon Allah.   

"To burinka bai cikaba baka makantar da itaba."

 tarik'a hannunta "mutafi deejamar tsohuwa kisha hura ki nemi wuri ki kwanta kirabu da wancan Azzalumin."

Kallon mahmud deejama tayi ta fakaici idon tsohuwa tayi masa gwalo had'ida murgud'a mashi baki."

Nuni yayi mata da hannu a lamar zanrik'eki."

Bai d'aga daga inda yakeba. Sai sallama yaji anayi, 

wata mata ce tashigo da yaronta janye a hannunta wanda bai wuce shekara goma ba da bokitin markad'e a hannunta duk ya b'aci da k'asa alamar b'ari yayi."

Tana fad'in "ina tsohuwa take?"

  Fito fito dan yau na rantse da Allah bazanyi asaraba. Kullum na aiki yarona wurin markad'e sai dijama ta tareshi a hanya tayi mashi dukan tsiya sannan daga k'arshe ta zubar min da markad'e to yau hak'urina ya k'are Dan bazanyi asaraba  sai anbiyani ehe "

Mahmud yadubi matar yace "d'aga murya kwarai yanda zasujiki suna ciki yanzun suka shiga."

Tsohuwa tafito deejama ta biyo bayanta,

  Tsohuwa tace Abu mai waina mekike fad'i?"

Me kuma deejama tayi?"

Abu mai waina tarik'e k'ugu, ta maimaita mata b'arnar da deejama tayi mata."

Tsuhuwa itama ta hau masifa tana fad'in Sam ba Deejama ta aikata hakan ba." 

"Na lura a garin nan babu wanda aka sanyawa ido irin deejama, yarinyar da na aika tasayomin sikari. Tayaya zatabi ta k'ofar  gidanku?"

to Wani irin sokon yaro ne gareki da har zai saki baki,

Deejama tayi masa duka kuma har ta zubar mashi da markad'e." dan Allah Abu mai waina kifita a gidan nan tun cikin muna mu biyu, dan babu wani ranko da zan maki ehe."

Ai kuwa Abu mai waina tashiga ruwan bala'i, 

"Ayi maka asara kuma baxa'a baka hak'uriba, to yau duk yanda za'ayi sai dai ayi amma sai anbiyani markad'ena."

Mahmud da yaji fad'an ba mai k'arewa bane, ransa ya b'aci yaciro d'ari biyar ya mik'awa Abu mai waina had'ida bata hak'uri."

Baki ta bud'e ta fara dariya takarb'i kud'in tana godiya,

  Sai  ta koma yin magana cikin lalama da taushin murya, "aisu yaran ne basajin magana, amma ya kamata a k'ara jawa deejama kunne saboda kaf a cikin k'auyen nan ta hana yara walwala idan ta fito kowa tsoronta yakeji."

   Babu Wanda ya kuma  tanka mata, sai Deejama da tace "kedai ki wuce kiba mutane wuri, tunda anbiyaki kud'in markad'anki, karki damemu da suruto."

Ta dubi Sale yaron Abu mai waina, ta harareshi tace "kai kuma sale duk na rik'aka saina karye maka k'afa d'aya."

Abu mai waina najin hakan kuma tasan halin dijama zata iya, zata fara wata sabuwar masifar mahmud ya bata hak'uri. SnnTa tafi, 

a hasale yanufi wurin dijama zai daketa tsohuwa ta turata d'aki tana fad'in wlh karka daketa. Meye ruwanka, to muddun ka daketa saina sab'a maka a gidan nan."

Mahmud ya dawo baya, yana hararar dijama yana fad'in zan rik'akine saina d'ebi d'arina biyar a jikinki. Dan bazan biya mki kud'i a banzaba."

Yanajin tsohuwa ta fara ruwan masifa ya fito ya baro masu gidan."

 Bayan sallar isha'i kamar yanda suka saba kowace yarinya zataci ado tanufi dandali,

   Haka dijama tayi kwalliya tasanya atamfa riga daban Zane da d'ankwali daban, tazane fuskarta da kwalliya kasan cewar dijama kyakkyawace kuma bafulatana ce, domin ba sosai hausarta ke fitowaba."

 An d'aure k'ugu da gyale."

Da gudu tafito gidansu tana rera wak'a, k'awayenta najin sautin wak'arta kowa ya fito daga gidansu suka tareta 

Suna fad'in ga 'yar gidan tsohuwa nan ta fito, aikuwa da murna suka tareta suka jera suka nufi dandali."

Dijama ce gaba k'awayenta suwaiba da lantana da ladidi, da luba a bayanta suntake mata baya domin itace boos duk Wanda yaja magana ita ke tare mashi."

Gefe d'aya suka samu suka zauna a kusa da wani mai kifi,

Mai kifin yana ganinsu , Sai da ya kuma dallara fitila ya duba da kyau ya tabbatar da sune,

 Ya sauke wani numfashi a ransa yace "Ashe yau zanyi kwantai bazan samu cinikiba. Saboda wad'an nan hatsibiban yaran."

'Dijama ta turo ido had'ida turo baki cikin tsiwa ta dubi mai kifi tace "lafiya meya faru kake haske mana ido da fitila?"

Mai kifi da saida gabanshi ya fad'i dajin maganar dijama, dan ba k'aramin aikinta bane ta bad'e basa kifi da k'asa taja masa asara kuma ba yanda zaiyi. Ya k'ak'aro dariyar dole yace "yi hak'uri 'yar gidan tsohuwa ai bansan kece ba."

Ya d'auko leda yasanya mata kifi. Yace 'yar gidan tsohuwa ga wannan kici,

  Ta dubeshi ta ya mutse fuska tace "ya'u kabar kifinka kawai yau  bana ra'ayin cin kifin."

Abokananta suna su, amma saboda tsoron da suke mata yasa ko wacce ta had'iya yawunta."

Ya'u mai kifi yana ganin haka yatashi tsam ya d'auki tiren kifinshi ya bar wurin ya canza wurin zama yayi nesa da su sosai."

DOWNLOAD BOOK


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post