[Book] Yar Gwagwarmaya Complete by Yar Mutan Arkilla

Yar Gwagwarmaya
Title: Yar Gwagwarmaya

Author: Yar Mutan Arkilla

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Fiction

Doc Size: 202KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Dauki littafin marubuciya 'Yar Mutan Arkilla cikakkensa mai suna "Yar Gwagwarmaya" complete hausa novel a text document daga shafin nan namu kyauta.

Book Teaser: A hankali take tafiyarta cikin isa da iya tako. Babu wanda zai dauka wata take bibiya a yanayin tafiyar tata. Domin ta fi maida hankali ga wayar hannunta, wadda take tafe tana lallatsawa. Sanye take da bakar riga doguwa, sai mayafin rigar da ta yi rolling kanta da shi. Kyakkyawar farar fuskarta ma'abociyar kwarjini ta bayyana. Yanayin lumshin da ake yi a garin shi ne ya karawa lallausar fatarta kala da armashi ga mai kallonta. Fadwa kenan. Ja'jirtacciya, kuma tsayayyar mace. Mai kafiya a kan ra'ayinta. 

Duk abin nan da take idonta na kan abin harinta, wato Suhaima. Wadda take bibiya ba tare da saninta ba. Wannan karon ta gama yanke shawara. Mai kan-kat, take so ta yiwa babban makiyinta Alh. Habib. Wanda duk duniya bata da makiyi kamar sa. Bata da burin da ya wuce ganin iyakarsa, da shi da mummunar harkallarsa.

Ta sadaukar da rayuwa da duk wani jin dadinta. Ba dan komai ba sai dan shi. Dan ganin ta kawo karshen abinda shi ne silar rugujewar ta'ta rayuwar.

Ta yi amanna cewa ita ce zata yi gyara a wannan fannin.

Ta dade da tattara duk wasu bayanai game da Alh. Habib, amma aka yi watsi da su. Daga karshe aka maida ta rikakkiyar mai laifi kuma abar nema ga hukumomi. Saboda rashin cikakkiyar shaida kuma bayyananniya, ga kokarinta na bayyana ma duniya boyayyiyar fuskarsa da mummunan halinsa, da kuma tarin ta'asar da yake tafkawa da shi da ire-irensa a rayukan bayin Allah 'yan kasarsu.

Wannan ne yasa hankalinta ya koma kan Suhaima. Babbar yarinya mai tashe a kasuwarshi ta yanzu. Kuma ta hannun daman shi. Ta tabbata muddin ta sami hadin kan Suhaima, ta shawo kanta har ta fito fili ta bada shaidar gaskiyar abinda yake aikatawa, to ba makawa duniya zata yarda. Saboda sanin kusancinta da shi.

Ta dade tana jiran wannan ranar, da zata sami Suhaima ta fito ita kadai. Amma bata samu ba sai yau. Wannan ne yasa gaba daya hankalinta ya tafi gareta. Ta ma manta da tarin jami'an tsaro da 'yan barandar da aka baza suna farautar ta..

Bangare daya kuma Dodonta ne, a's'p Sauwam yake bin sawayenta daga nesa yana murmushi, zuciyarsa cike da farin ciki. Yana mamakin wannan wace irin nasara ce Allah ya bashi haka cikin sauki? Yau ga shi ga gagararriya Fadwa. Ya tabbata a wannan karon kamar ma ta shiga hannu ne. Dan kuwa babu abinda zai sa ya rasa ta kamar sauran lokuta.

Ganin ta shiga kofar Hotel na sharaton. Yasa ya dan tsaya daga nesa, sannan ya ciro wayarsa ya danna kiran lambar ofishinsu. 

"Hello! Yallabai, Abbas ke magana." Aka fada daga can inda ya kira din.

"Gud Abbas maza ka debo jami'an tsaro, ku same ni a Sharaton Hotel. Ku yi da jikinku, Fadwa ce na rutsa, kuma na tabbata wannan karon sam ba zata sha ba." 

"To yallabai." Abbas ya fada yana sarawa mai gidan nashi, kamar yana kallon shi.

Duk wannan wainar da ake toyawa Fadwa bata sani ba. Ita kam, kanta tsaye take bin Suhaima. Bata da burin da ya wuce ta riske ta a wani lungu na wajen, kafin ta fada dakin da zata shiga.

Ita kuwa Suhaima ko alama bata san ana bibiyar ta ba. Tana isa cikin Hotel din ta hau lifta ta danna lambar hawa na shida. Da isarta ta fita, ta fara tafiya a duguwar hanyar da zata sada ta da dakin da ta zo. Cikin azama Fadwa dake bayanta ta sha gabanta. Turus ta tsaya, suka shiga yiwa juna kallon-kallo. Ita dai Suhaima kallon rashin sani take mata. Da kuma mamakin yadda ta tare ta kai tsaye. Ita kuwa Fadwa kallon kyau da tsarin Suhaima take, da kuma tsan-tsan tausayinta. Domin a yadda take sam rayuwar da take bata kamace ta ba. 

"Baiwar Allah lafiya?". Suhaima ta tambaye ta fuska a daure. Har ta budi baki zata yi magana suka ji maganar 'yan sandan dake waje. Ta cikin lasifika suna cewa "Fadwa! Fadwa!! Na san kina ji na, kar ki yi taurin kai. Ki fito kawai ki mika kanki ga hukuma. Wannan wajen duka a zagaye yake da ma'aikatanmu. Baki da wata hanyar guduwa. Ki mika kanki kawai 'yar gwa-gwarmaya." 

Murmushin nan nata na musamman ta yi. Tare da lumshe ido. Wannan ne ya tabbatar wa Suhaima cewa da ita ake maganar. "Yar gwa-gwarmaya?". Ta mai-maita sunan tana kara karewa Fadwa kallo. Hannu ta daga ta nuna ta da shi "dama ke ce 'yar gwa-wagwarmaya? me yasa kike bibiyata nima? Wai me muka tare miki ne kike neman raba mu da jin dadinmu?".

Fadwa bata kai ga yin magana ba, jami'an tsaron suka fito daga cikin lifta suka nuna ta da bindigoginsu. "Kar ki motsa Fadwa! Kin shiga hannun ma'aikata." Ta ji muryar a's'p Sauwam ta fada cike da gadara. 

Idonta a kansa. Sai murmushi yake yana tunkaro ta da inkwa. Da kallo daya zaka gane irin farin cikin da yake ciki. Fadwa ta kuma lumshe ido a karo na biyu, ta yi murmushi. "Kai babban jami'i ne Sauwam, amma me yasa kake goyon bayan rashin gaskiya? Na sha gaya maka ni Fadwa a kan gaskiya ta nake. Ba kuma zan daina gwa-gwarmaya ba har sai burina ya cika."

"Gaskiyarki da rashinta ba ni ko ke ne zamu fada ba. Shari'a ce zata bayyana." Yana maganar yana dada tunkararta. "Ka yi gaskiya Sauwam. Tabbas kotu ita take bayyana mai gaskiya. Amma ba irin wadannan kotunan da muke da su yanzu ba. Hujjoji a kan makiyana suna da wahala. Amma ni tuni kun gama hada hujjoji a kaina. Wannan ne yasa ba zan taba baku damar kamani ba."

Ta fashe da dariyar nan ta'ta da suke kira ta 'yan iska. Tace "Sai wani ganin a's'p Sauwam." Ganin haka da kuma sanin wace ce ita yasa a's'p ya fara sakar mata harbi. Sai dai kash! Fadwa kam ta bace bat!. Ta bar shi da harbin iska...

DOWNLOAD BOOK{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post