[Book] Yar Jami'a Complete by Herwwerh Jidderh

Yar Jami'a

Title: Yar Jami'a

Author: Herwwerh Jidderh

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Fiction

Doc Size: 314KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2016

Description: Sauke littafin marubuciya Herwwerh Jidderh mai suna "Yar Jami'a" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu complete dinsa.

Book Teaser: Hi Daddy shigowar tane yasa daddy da umma tsayawa daga hirar da suke da mai da kallon su gareta dariyar da daddy ya sakarmata yasa ta kara langwasar da jikinta ta hanyar fadawa jikin umma tana wani shashsheka kamar mai shirin kuka daddy xan wuce scul na ji ance jiya anyi lecture toh ai kinga irinta dama ai nasan xa'a rina kamar na sani nace jiya karkije airport tarar mahaifinki amma kika ki ji ki sani fa wannan makarantar ba kamar ta baya bace dole sai kin kula cewar umma tana kallonta fuska ba yabo ba fallasa tuni hajara ta mike daga jikinta tana bubbuga kafa a kasa tana daddy ka ganta ko ai bashiri daddy yaja hannunta fuuuu suka haye sama yana mai bata baki shigarsu dakinsa ke da wuya daddy yace  beauty rufe idonki ki karbi tsarabarki amma fa bayawa kin san ba shiri kika sa na dawo dan naga murnar xagayowar haihuwarki gobe cikin sauri ta rufe tare da cewa toh na rufe daddy dakko min hannu yasaka cikin aljihun  riga yaxaro karamar takarda ya bude hannunta ya saka mata yace gashi babu yawa kya iya bude idonki yanxu;ai kamar jira take ta bude me xata gani takarda(check)da rubutun kudi har naira dubu dari biyar,tace daddy wannan fa bade shine na kayan da xan siya na birthday na ba tana fadi tare da bata rai yace haba beauty kamar ni na baki haka a birthday"kawai na shiga scul ne dan ki farin cikin daddynki ya dawo" woooo" ihun da tasa ke nan tana mai rungumesa da fadin sai daddy na wallahi ko garin ba kowa amma fa ki kula maza kisaka a jakarki kafin......bude kofar da akai ne yasa ta yi saurin saka takardar a jaka da fadin bye daddy kam tayi bakin kofa ita bata wuce ba kuma batai magana ba har sai da daddy yace bata hanya fa kar 'yata tai latti matsawar umma yabata damar fita cikin sigar sauri batayarda tayi magana ba sai da takai bakin kofa da sauti mai karfi tana umma xan siya miki ice-cream rufe kofar tai da xura wa mijin nata ido  sanin da abinda ya kawota yasa yayi azamar juyawa da bude kofar bandaki murmushi kawai ta saki tace kashiga kafito ina jiranka don akwai maganar da xamuyi!

Abangaren beauty kuwa kamar jira take ta karasa wajen aje mota tana dariya ta bude jaka ta xaro key ta bude motar tare da rufe ta tadau kusan minti biyar tana kallon kanta a madubin motar kafin tunaninta ya koma kan takardar daddy!yanxu toh yau me xanyi wanda yafi na kullum yanda xai sa na wuce duk wata kaza a scul din nan don allah yau sai an bini ko ba'a so hhhhhhhhh!jin dariya kawai kake na tashi kamar tana hira da wata karar wayarta ya katseta daga kogin tunanin data fada ganin wacceta kirata yasata saurin dauka da karawa a kunne tana fadin duk inda kike yanzu ki fito ki tsaya a bakin gate na scul dan yau akwai harka... 

Harka kuma?ka ga shegiyar gari waya gina ki haka ?gaskiya beauty ba kyau wajen samu kalaman matashiyar yarinya xee-xee kenan wacce ta amsa sunanta! Shike nan dama ina hanya na tsaya gidan mai ne amma yanxu xaki ganni,ok toh sai mun hade haka ta fada tare da kashe wayar tana maida numfashi! Cikin nutsuwa takunna motar tare da kara sautin wakar (u are my african queen) wanda ya bata damar  juya kan motar tai hanyar gate gaisuwa baba me gadi ke kai wa da washe baki yana kokarin bude kofar!jaka ta bude ta zaro dubu hudu ta mika masa tai waje ai godiya da kirari wajen baba me gadi ba kama hannun yaro!!

Kofar shiga jami'a cike take da motoci,mashina,kekuna da kuma dalibai matafiya kasa kowa cikin layi don karbar takardar shedar shiga jami'ar(gate pass)hange take tayi ko ta gano inda aminiyarta ta tsaya amma yawan motoci sun hana dole ta kira ta a waya tasanar da ita inda ta tsaya!can gefen titi kadan da gate ta tsayar da motar!gano lambar motar yasa beauty tai saurin karasawa tare da tsayar da motarta,tsayuwarta ya ba xee-xee damar bude motarta da nufowa wajen beauty;ai kamar jira take ta shigo beauty ta saki wata dariya jikake tana fadin ai mun afuwa na jima ko? sarkin fushi kallon data sakar mata yasa tai ajiyar zuciya tare da fadin mene labari!

Sannin kanki ne  xee-xee daga haduwarmu wancan satin xuwa yau mun shaku da yawa kuma tamu tazo daya dan haka ina so na ke ta raini a scul yau fiye da yadda na yi satin daya wuce don so nake na zama 'yar jami'a lamba daya da kowa zai so ni a makarantar nan duk da ana cewa sai ka gama tashenka wani bai san da zamanka ba!amma ni beauty kisani da ban nake kuma dole abi ni don salona daban yake tawan!!hhhhhh dariya xee-xee ta saki tare da kallonta tana fadin kina wuta beauty! Naga wani country mall wajen ya hadu amma fa ban taba lekawa ba kawai xamu shiga ki siya ki canja acan tunda akwai wajen sa kaya sai kuma nima asai min nawa ko kuwa??xee-xee tai furucin tana mai watsa hannayenta!hmmn kema kin san wannan ba matala bace ke dai shiga motarki ki biyo ni kawai!!

Haj.Halima ce zaune bakin gado"wato umma tana jiran fitowar daddy daga wanka" tunani fal cikinta ta sak'a wan-can ta kunce wan-can" jin da tayi an watsa mata ruwa a fuska ana dariya yasa ta dagowa tana kallonsa"!har ka fito dear ta fada tana kauda kanta" !juyawa kawai yayi yana fadar ai tunda ba taimako ba dole nai saurin fitowa ba" don nasan ko fita ban gama yiba na fito !jin tayi shiru yasa shi juyowa tare da fadin ki tallafa min wajen shafa lotion mana uwar'gidan!mikewa kawai tayi ta dawo kusa dashi batare data bari sun hada ido ba"tahau shafa masa sai da tagama tsaf tana shirin tashi yace yau kuma fuskar laifi me tai miki kika barta?cikin halin ko in kula ta debo lotion din ta kai hannunta fuskar ke nan ya ruku hannun tare da fadin haba farin ciki na ki shafamin mai tare da kallon kwayar idona shine abinda nafi so sama da komai a yanzu dan nasan baki da musu.

Sannin halin matar tasa yasa ya dago fuskarta suna duban juna yace kiyi sauri mana ina so naji damuwarki fa kallon daya bita dashi ne yasa ta murmushi tana fadin dear kasan lagona da yawa duk damuwata ka iya da ita maza tashi kasa kaya muyi maganar!!murmushi ya saki ai kin san mata da miji sai allah tawan!

*******

Katon katafaren kantin nan na country mall beauty ta tsaya tare da fitowa cikin zumudi don taga lokaci na tafiya!besty yi sauri fito mu shiga ba lokaci fa cikin karamin lokaci suka shiga dauki wan-can aje wan-can" har sai da mai kula da wajen kayan mata  ta karaso (area sider) lura da yadda suke bincike kayan tana tambayar baku sami abinda kuka zo nema bane?" naga tun daxu sai bin cike kuke? cikin sauri xee-xee ke labarta mata me suke so!murmushi kawai tayi tare da jan hannun beauty xuwa wani daki"daki ne madai-daici amma fal yake da kaya na alfarma"dubanta beauty tai cike da mamaki tace wow fantastic"nan matar ta dafota tana fadin wannan kayan da kika gani anan d'akin sai manyan mata ke sayansu ga k'yau ga kudi in zaki iya nasa ashirya ki a tailoring room dinmu" ya kika gani?baki kawai beauty ta bude tana kallon matar ai auntyn 'yan gayu kudi ba matsala ta bane ke dai ashirya ni kawai!auntyn 'yan gayu kuma kaji sabon suna cewar matar tana dariya"nan suka fito daga d'akin xee-xee de na tsaye tana kare ma wajen kallo auntyn 'yan gayu ce ta waigo tace kawar beauty ki zabi naki bari na kai ta ciki a gyara ta!toh kawai tabita dashi xee-xee tana kare ma wajen kallo lallai gaba  da gabanta wai aljani ya taka wuta!

Shalele na ya kika ga wannan shigar! dagani ba tambaya wannan shine namijin da baya tsufa!dariya suka saki a tare sannan ya dawo gefen gado kusa da ita ya zauna yana mai mata nuni da ta juyo inda yake!uwar gidana mata daya tal gare ni a duniya har lahira inshaallahu haleematu na gaya min damuwarki!Damuwata sanin kanka ne baza ta wuce taka da ta 'yarka ba wallahi dear ina shiga cikin wani matsanan cin hali idan naga yadda kake tafiyar da rayuwa hajara katuna yanxu ba da bace!ace yarinya tun tana karama sai abinda take so ake mata bata san fada ba!har tana ganin kamar kafi sonta akai na gaskiya dear da sake don haka kasan abinyi akanta!ya kamata muzauna muduba rayuwar yarinyar nan don nan gaba fa aure zatai haka zataje gidan mijin nata kuma har ta iya rike 'ya'yanta da wannan tarbiyyar hab.....ke!ke!ke dakata halima wannan ne daman damuwar naki ashe kuwa zaki jima cikinta ko dan bana miki magana kina gani ina kauda kai shiyasa yau kika biyo ni ta haka"?eeyee"?nayi zaton ma kina missing beauty ne din xata je scul ta barmu  da kadai ci"ashe ke ba haka ba!toh idan ban nuna mata so ba wa zai nuna mata?ai wannan shine gata!"gata"?gata fa kace dear?wannan ba gata bane wallahi cutar kaine kuma ya kamata ace kasan da haka" inda nima haka aka kawo maka ni ai da nasan yanzu labari ya canja kafa tsaya ka duba maganar nan dear!"dubawar kenan kuma kisani rai na ya baci dan haka idan bazaki iya taimaka min akan tarbiyyarta ba ni zan iya ni kadai !kuma kar naji kar na gani bacin ranki akanta halimatu!

Mekewar da yayi ne yana neman fita rai a bace wai shi me 'ya yasata durkusawa gabansa tana mai sunkuyar da kai!dear dan Allah ka gafarta min kada fushinka yasa na samu fushin mahaliccina natuba kuma bazan sake ba amma na san da ranar nadama!hmmm tawan kenan tashi na ji ba komai kuma ya wuce amma ba ranar nadama!!cikin yanayin bacin rai ya fice tare da rufo kofar gammm kake ji !!tashi tai ta zauna tana kare ma dakin kallo!hmmn Allah gatan bawa ga dukiyar ga soyayyar ina samu amma tarbiyar 'yar ciki na an hana nabata wannan wace irin rayuwa ce da anyi magana ya hau fushi yana kururuwa kamar wani zaki wai shi me 'ya!"

hmm na biye ma tunani tabbas zan iya kamuwa da wata cutar bari kaga na  tashi na leka kitchen naga me ladiyo ta ke yi!

DOWNLOAD BOOK


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post