[Book] Zabin Shi Ne Complete Hausa Novel by Mom Islam

Zabin Shi Ne

Title: Zabin Shi Ne

Author:  Mom Islam

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Love Story

Doc Size: 152KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Masoyan marubuciya Zainab Habib wacce aka fi sani da Mom Islam ku sauke littafinta mai suna "Zabin Shi Ne" complete hausa novel a text document daga wannan shafi namu mai albarka.

Book Teaser: Gida ne madai-daici wanda ya kasance mai ɗakuna biyu , ɗaya na mama ɗaya kuma namu nida yayana haidar , gefe kuma kicin ne sai bayin mu dake can hanyar fita waje .

Zaune nake a kan kujera ƴar tsugunno fuskata tasha hoda kasancewar bana rabo da kwalliya koda wane lokaci, mama dake zaune kan tabarma ta kalleni tare da cewa "Umaimah kitashi ki zuba shinkafar a kula mana kina ganin har ƙarfe goma da rabi 10:30am "miƙewa Umaimah tayi tana ɗan turo baki kana tace "mama gobe zan huta "mama ta harari Umaimah dak kwashe shinkafa da ludayi tana sawa a babbar kula , bayan ta gama sawa ta kawo murfin kular ta rufe , tare da gyara mayafin dake rataye a kafaɗarta tace "mama har yanzu almajirin bai zo ba "mama na shirin magana almajiri ya shigo ya gaishe su ya ɗauki kular mama tayi musu Allah ya bada sa'a ,Umaimah ta ɗauki bokiti mai ɗauke da robobi da baƙaƙen leda da cokula a ciki suka fita , sunyi tafiy mai nisa kana suka iso gidan mai , inda ƴan mata ke zaune ko wacce da abin siyarwa a gabanta , Umaimah na zuwa samari suka fara tasowa kowa na cewa "zai siya ,bayan ta zuzzuba musu ta hau wanke robobin da wasu suka gama ci , cikin ikon Allah abinci ya ƙare har ana nema "ƴan matan dake kusa da ita sukace "Umaimah ki jiramu mu tafi tare "Umaimah tace "wlh baba na ganin na daɗe zai biyo sahu na, kuyi haƙuri sai anjimanku " taɓe baki sukayi ,Umaimah ta ɗibi kularta da bokiti tayi gaba , tana cikin tafiya taji kamar ana binta , da ta tsaya sai taji an tsaya ,cikin mamaki taci gaba da tafiya ,tana zuwa wani lungu da ba kowa ke binsa ba taji ana cewa "maza ku toshe tacan ni zanbi tanan "juyawar da zatayi taga samari ne su biyu ƴan shaye-shaye , cikin tsoro ta wurgar da kular da bokitin kafin ɗayan ya zagaya ta falle da gudu , tana gudu suna binta sai da suka ga sun iso gurin mutane sanan suka koma ɗayan yace "idan kere na yawo zabo na yawo wata rana zasu haɗu ,Allah ya kaimu gobe wlhi ko ban tareta a lungu ba sai na mammatse na shannunta "ɗayan dake layi kamar zai faɗi yace "ai kai ka kira da sauƙi baabaa ni inhar Allah ya haɗani da ita wlh sai na yi mata zigidir "suka sheƙe da dariya .

Tsabar gudu Umaimah kamar zata kifa har wani duhu take gani ,tana zuwa dai-dai gurin wani mai shago ta faɗi tana mai sakin kuka sbda jiri days ɗauketa ,mai shago ya fito yana salati ya duba fuskarta yace "ai Umaimah ce "sai kuma yayi bismilah ya ɗagata yana ce mata sannu "dafe kai Umaimah tayi ta kalli kuɗin dake damƙe a hannunta ta kalli mai shago tace "nagode "murmishi mai shagon yayi mata kana yace "yau babu abinci ne ?"Umaimah tace "eh "tare da cigaba da tafiya , tana tafe tana saƙa da warwara a zuciyarta har ta iso zauren gidansu , tsayawa tayi tana nazarin me zatace wa mama idan ta shiga , Yaya Haidar ya shigo da sallamarsa , ganinta tsaye a zaure ya sashi cewa "Umai ya akayi ?"Umaimah ta shagwaɓe fuska kana tace "yaya an sace kayan abincin "dariya yayi mata kana yace "idan bakison talla sai ki ɓoye kayan abinci yau kuma da wanan salon kikazo ? Umaimah tace "wllahi yaya babu kular wallahhi wasu ne suka tareni ƴan iska shine nabar kular na gudo "mama dake  zaune tana haɗa miyar dare ta fara magana cikin ɗaga murya tace "wlhi Umaimah idan bakije kin ɗaukomin kayan ba Allah ranki zai ɓaci "yaya Haidar yace "Umai muje ki ɗauko inyaso gobe ki huta da tallan "mama dake tsaye tana kallonsu  tace "Aliyu kana ɗaure mata gindin zama ko ?"kana sane mahaifinku ba kuɗin cefane yake bamu ba "cikin ƙosawa Umaimah tace "yaya Haidar mu tafi ", da fitarsu suka miƙi hanyar da zata sadasu da gurin da samarin nan suka tareta , koda suka kusa gurin yaya Haidar ya shige gaba ita kuma ta koma bayansa , tun da su Umaimah suka taho samarin ke hankalce dasu ,sai da suka zo dai-dai lungun  yaya Haidar na shirin shiga yaji an rufe masa fuska ana tafiya dashi , Umaimah dake ihu tace "na shiga uku na lalace zasu kashemin yayana "samarin na ɗazu sukace "babu kisa ki bari mu kwashi kayan daɗi zamu dawo miki dashi "gaban Umaimah ya bada rasss ta fara waige-waige tana neman agaji ,shirin gudu take amma ina sunfi ƙarfinta ,suka sanyata a tsakiya tare da riƙe hannunta tana yaƙushinsu amma ko a jikinsu , wani ɗaki suka nufa da ita wanda babu kowa a cikinsa , da'alamu ɗakin na kwanan su ne ,su biyun suka rufe ƙofa tare da....!

Matsowa gabanta ɗayan yayi ya fara  cewa "dan kinga kin cika shine kike neman raina mana hankali koh ? to wlh yau ɗinnan zanga wanda zai hanamu jin daɗi dake "suna tsaka da magana Umaimah ta ƙwalara ƙara a tunaninta ko akwai wanda zai zo wuceww ya taimaka mata , sai taji shiru .

Ƙokarin cire belt ɗin wandonsa  ɗayan yayi shi kuma ɗayan ya tsaya a bakin ƙofa , wanda ke tsaye a gurin Umaimah yace "ki gama zagaye zagayenki babu inda zaki "Umaimah ta miƙe jiki na rawa tayi hanyar ƙofa taji gam ta fashe da kuka , mai sauti  .

Cafko mata nono yayi tare da cewa "wayo laushi "ihun data kuma saki ne yasa suka ihun abokin waanda ke gurin Umaimah ,cikin ɗaga murya suka jiyo ihunsa , a lokacin da wanda ya riƙe Umaimah ya buɗe ƙofa wando a sakwar kwace ,lokacin ita kuma ta samu damar gudu idonta na ci gaba da tsiyayar ƙwallah , ɗayan abokin na fita sukaji an rufesu da duka , suna ihu suna cewa "dama Baabaa baka kulle Haidar ɗin ba ?"Haidar dake dukansu yace "wlhi da kunyiwa ƙanwata wani abu da sai na zamo ajalinku "ya juya ya tafi , yana tafe yana tunani , a fili yace "Allah sarki Umai gani nazo taimaka miki ,kin wuce baki lura dani ba .

Also Download: Lamarin Kaddarar Aurena Complete by Mom Islam

Umaimah kam gudu takeci sosai dan ko bayanta bata dubawa ,wani azababben horn taji wanda ya karaɗe kunnuwanta ta tsaya cak tare da juyowa "wata mota ta gani sabuwa fil mai numfashi ,sai kuma ta ci gaba da gudunta , jin motar tasha gabanta yasata fashewa da kuka tace "kukuma me kukeso a gurina ?"wani dattijo ne ya fito hannunsa riƙe da key ɗin motarsa a ƙalla zaiyi shekara 58") yace "ƴan mata mai ya sameki tun ɗazu naga kinata gudu ko wani abun kike nema ?"Umaimah da kuka ya kuma ƙwace mata tace "malam dan Allah ka ƙyaleni "taci gaba da maganar tana kuka ,cigaba tayi da gudu har ta iso gidansu ,tana shiga  ta faɗa jikin mama dake zaune ta zuba tagumi Haidar na bata labarin abunda ya faru da ya riga Umaimah zuwa gida kasancewar ba hanya ɗaya sukabi ba "Umaimah tace "mama kinga abin da nake gudu da tallah ko kince dole sai nayi "ɗago kanta mama tayi kana tace "Umaimah  insha Allah bazan ƙara cewa "ki ɗauki tallah ba "cikin tausayawa yaya Haidar yace "mama in Allah ya yarda zan fasa asusuna yau dama nace kuɗin aure nake tarawa yanzu ko na fasa "mama da hawaye ya wanke mata fuska tace "a'a Aliyu bazaka fasa ba ,kaci gaba da tarawa Allah zai kawo mana mafita .

Suna tsaka da magana sukaji sallamar baba hannunsa na riƙe da akwatin gyaran takalmi ya ajiye tare da cewa "wash wlhi na gaji ace tun safe ina yawo iyakacin ɗari da ashirin nayi "babu wanda ya kulashi har sai da yace "ku kuma me ya faru kun wani yi durun-durun sai kace anyi muku mutuwa "yaya Haidar yai ƙarfin halin cewa "baba muna shawarar sana'ar data dace ne "to yayi "baba yace "ya shige ɗaki "ba tare da yaya Haidar ya jira mai mama zata ƙara cewa ba ya miƙe ya nufi ɗakinsu na matasa dake can ƙofar gidansu ya ɗauko jakarsa dake saƙale da ƙaramin ƙwaɗo ya buɗe ya tura hannunsa ƙasan jakar ya ciro asusun ,ya mayar da kwaɗon ya rufe ya fito ya dawo gida .

Da ganinsa da asusun mama tace "Aliyu  ba nace karka fasa ba ?" ba tare daya saurari ƙarashen maganarta ba ya sanya wuƙa ya cicire ƙusoshin asusun ya zazzage kuɗin ,dama baba na leƙe  da wundo yana ganin kuɗaɗe sun zubo ya fito kamar mai jin yunwa yace " wai baku gama abinci bane ?"mama tace "ka bada cefane ne ?"baba bai ce komai ba ya waro ido tare da sanya hannu a baki yace "Gadanga dama kanada kuɗi haka ka barmu cikin talauci ?"ran yaya Haidar ne ya ɓaci yace "nima ba nawa bane na Kamalu ne da muke kwana ɗaki ɗaya yau zai tafi gida yace "in shirya masa "cikin gamsuwa baba yace "to ai na ɗauka naka ne ?"babu wanda ya sake kulashi ,ya kalli Umaimah da har yanzu kuka take yace "ke kuma sangartacciya me akayi miki ?"babu komai Umaimah tace "sbda sunan yana mugun ɓata mata rai ,komawa ɗaki baba yayi ganin ba'a kulasa ba  ya ciro awara a cikin aljihunsa ya fara ci ,yana gama ci ya nannaɗe ledar ya mayar aljihu .

Bayan yaya Haidar ya gama fito da kuɗin duka suka ƙirga dubu ashirin ne dai-dai ,ya ciri dubu uku ya miƙawa mama dubu goma sha bakwai yace "gashi ta saro wani abun "godiya mama tayi masa tare da sa albarka ,Umaimah dake kwance cinyar mama tace "ga ragowar cinikin da nayi "yaya Haidar ya karɓa yace "nawa ne ? Umaimah tace "dubu biyu da ɗari biyar "mama tace "ai dole dasu zamuyi cefanen dare baza'a haɗa da wanan kuɗin ba "yah Haidar yace "daga yau a dinga aikana mama wlhi fitar Umaimah hatsari ce "baba dake ɗaki yace "idan bata fita ba ka gayamin waye zai aureta munafukai kawai "tsit sukayi ,mama tace "ka siyo taliya leda biyu ka siyo manja na ɗari da hamsin da magi na hamsin munada kayan miya da gawayi "ficewa yaya Haidar yayi ya tafi cefane Umainah kuma ta fara haɗa kayan miya .

Fitowa baba yayi hannunsa riƙe da riga da wando masu datti ya miƙawa mama yace "a wanke min su yau "to mama tace "har ya juya tace "kuɗin omo fa ?baba yace "kin ɗauka banji abin da kukeyi bane ?to ki ɗauka a wanan kuɗin "daga haka ya fice .

DOWNLOAD BOOK

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post