[Book] Zeenat Yar Jarida Complete Hausa Novel by Fresh Ummie Xeey & Nabilancy Luv

Zeenat Yar Jarida

Title: Zeenat Yar Jarida

Author: Fresh Ummie Xeey & Nabilancy Luv

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Fiction

Doc Size: 184KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuciya Fresh Ummie Xeey tare da Nabilancy Luv mai suna "Zeenat Yar Jarida" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu complete dinsa.

Book Teaser: Tana Zaune a dakinta ita kadai tanata faman rubuce rubuce 

Dare ne sosai kusan biyu saura gari yayi tsit bakajin komi sai rugugin hadari dayake haduwa

Zeenatu kenan jajirtacciyar "yar jarida wacce takasance batada tsoro a ckn ranta arayuwarta bataki tayi qunar bakin wake ba inhar zata cimma burinta

Inta d 'anyi rubutu jim kadan saita dakata tayi tsai da ranta ta kalli silin din dakinta kana taci gaba 

Ahanakali aka turo dakin aka shigo 

Ta dago kai da sauri takalli me shigowar

Mahaifiyar tace gwagwgo Sa,a

"Yanxu ashe bakiyi bacci ba zeenatu har yanzun kinata faman wannan rubutce rubucen naki na wahala ayi mutum baxai hutawa ransa ba nifa gaskiya nafara tsanar aikin nan maku zinatu domin bakya hutawa ko kadan kuma bakya kallon hatsarin dake ciki ina dalilin hakan.

Zeenatu tayi murmushi tace da gwagwgon

" kwantar da hankalinki gwagwgo na yanzu xan ajiye nakwanta dan allah kidaina damun kanki da Tsaurin da aikina kedashi Duk wani abu na hatsarin ciki da yardar Allah bazai kusanceni ba kiyita min addu,arki nasan Allah zai tsareni 

"To hakane Allah yatsareki da tsarewarsa Amma nikam yanda nakejin wasu "yan jaridun ke shiga taskun rayuwa inajiye mk tsoro yar nan da zaki ajiye wannan aikin ki sami wani da zanfi farin ciki.

Zeenatu tace

" oh kash gwaggo kenan yaushe zanyi kasadar ajiye aikin dana samu awahalce haba ai yanda ma nake kaunar aikin jarida banga abinda zaisa na karaya kona fasa yinsaba ai duk tsanani yana tareda sauki kin manta wahalhalun dana sha kafin nasameshi ? Kin manta irin gwagwarmayar rayuwar da nayi gwaggo akan karatun aikin jarida ke kanki kinsha tausayan akan fafutukar dana ringayi wajen buga bugar ganin nakammala karatuna kema ai yau innace nadaina aikin jaridar nan saikiyi min fada ko kin manta tun ina karamata nake sha,awar naga nakasance *"YAR JARIDA ne*?

Gwagwgo taja ajiyar gwauran numfashi tace "to ya zanyi dake yar nan amma gaskiya ina ckn jin tsoron yanda kike kai dare kafin kishigo gida tunda kince wani xubin bakya samun abin hawan dazai shigo dake lungun nan namu gashi antaba biyoki kwanaki abaya kartai Allah yasa kika farga dasu Allah kuma yatsareki kk tsallake rijiya da baya 

Zeenatu tace " hhhhmmm wannan abun ai ya zama shudadde kima daina tunashi ya wuce guna sau fatan Allah yatsare ni agaba.

" to Amin Amin dai, yanzu dai yakamata ki kwanta haka

Zeenatu ta ajiye biron dake hannunta tace " to gwagwgo na yanzu ma kuwa zankwanta da sassafe naci gaba don da wuri zan futa ma.

Gwagwgon na futa ta kwanta akan katifarta 

Tana kwanciya tahau karanta addu,ar kwanciya bacci

Ckn minti biyar baccin yai awon gaba da ita.

Awa daya da kwanciyar baccinta ta farka afirgice tana salati da addu.a

Mafarki tayi me ban tsoro 

Tagantane ackn dokar daji tanata gudu kanta ba dan kwali kafarta ba takalmi ga wani plate C.D ahannunta

Da alama akan CD din nam suke binta 

Domin data fada kan wani katon dutse suka cimmata duka suka kai mata suna cewa ta basu

plate din

Da taki basune suka daureta da igiya hannayenta abaya da kafarta sukaiwa daurin

Suka dauki CD din suka tafi suka barta adokar dajin nan

Yayinda wata kura ta tunkarota a yunwace tayo kanta zata cinyeta

Adaidai lokacin da kurar ta bude baki xata cinyeta alokacin ta farka afurgice

Gumine yaringa keto mata tahau sarcewa

Adai dai lokacin taji ankece da ruwan sama tun hadarin daya hado da daddare ne ba,ai ruwan ba sai yanzun

Ta tashi ahankali cikin sanyin jiki ta saki labulan windonta ta rufo windon saboda feshi dayake shigo mata

DOWNLOAD BOOK


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post