[Book] Zubar Hawaye Complete by Maman Hanan

Zubar Hawaye

Title: Zubar Hawaye

Author: Maman Hanan

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Love Story

Doc Size: 216KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuciya Maman Hanan mai suna "Zubar Hawaye" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu complete dinsa.

Book Teaser: Garin yola kowa yasan mazauna wannan garin mafi akasarinsu fulani ne.

Anguwar DAMARE yan matane da samari yara da manya sunyi cincirindo a gurin diban ruwan Borehole da ake siyarwa bokitin sharon Naira Goma bokiti uku Naira ishirin,

Yawanci anfi zuwa gurin ranar da aka kwana biyu babu ruwa kasan cewar mafi akasarin wadanda suke siyan ruwa a gurin Masu saida ruwan jarka ne wanda suke amfani da kuran ruwa (amalanke)

Idan kaga wata yarinya ko yaro sunzo siyan ruwa gurin toh ba shakka iyayen marasa karfine sosai ko kuma masu cikakken son banza.

Aysher tana zaune a gefe tanajiran layi yazo kanta dan batazo da wuri ba saida Yadikko taga ankawo wuta sannan ta turota 

Dan idan da wutan nefa zaka sayi ruwan yafi arha akan idan sun tayar da Gen.

Aysher tasowarta kenan daga makarantar boko harta zauna zata fara cin abinci yadikko tace tatafi ta nemo mata mai ruwa.

Toh ganin ankawo wutan Nepa ne yadikko tace tazo tasiya mata bokitin Penti babba guda uku.

Kasan cewar Aysher ba ma'abociyar son hayaniya bane yasata komawa gefe tazauna tanacin dankalin hausa danye wanda kawarta fatima Alhasan tabata daman ta6oye a jakarta ganin zata taho diban ruwan ne yasata daukowa aboye ta taho dashi.

Sai da tayi awa d'aya kafin akazo kanta aka zuba mata tadinga daukar bokitin da guda d'ai-d'aya harta gama tana shiga gidan da sallama kanta dauke da bokitin sahun karshe  tana mai farin ciki zataci abinci ta wuce makarantar islamiyya dan shirye-shiryen saukar karatun Qur'anin da zasuyi nan da sati biyu masu zuwa.

Bayan tagama cin abinci ta mike ta wanko hanunta daman tayi sallah tundaga makaranta 

Hijabinta ta dauko da alqur'aninta ta daga labulen yadikko cikin yaren fulatanci tace"Yadikko nagama zantafi makaranta"

Yadikko tadago fuska a had'e tace"Bazaki tafi yanzuba kitafi gidan Innawuro kigama mata aikinki na safe da baki kammala ba kafin kizo kitafi inyaso idan kidawo daga makarantar ko sha ukun dare ne saiki gama aikin gidan nan

Ina dalili ubanki yabugi kirji yace karatu zakiyi toh gaki ga karatun naji dadin wannan saukar da zakuyi aradun Allah kina gama saukar nan babu wata islamiyyar da zaki sake zuwa aiki zaki kamayi tukuru gidan Innawuro tunda ubanki yahana kimin talla toh ai shikenan".

Cikin sanyin jiki Aysher taja kafarta maida Qur'anin d'akinta kafin tafito tabar gidan takama hanya dan zuwa gidan Innawuro.

WACECE AYSHER

Aysher Usman Abdullahi shine cikakken sunanta shekarunta 16 tana S.S one a boko, islamiyya kuma tana ajin karshe Aysher cikakkiyar bafulatana ce dan idan taga dama saita wuni batayi maka magana da hausa ba miskilace takarshe kyakyawa balaifi.

Mahaifinta yana harkan gwarine zuwa lagos balaifi yanada rufin asiri dai-dai gwargwado.

Mahaifiyarta kuwa aysher bata santa ba sai a hoto.

Ayanda mahaifin Aysher yake bata labari tuntana wata takwas wata rana da sassafe ta tsallake tabar Aysher akan fo tabar gidan.

A lokacin yadikko ce uwar gida tanada yara 3, Muhammad,Bilal, da   zulai wanda yanzu haka anyi mata aure dan yadikko taki yadda tayi karatu.

Bayadda ba'ayi da mahaifiyar Aysher tadawo gidan ba amman taki dawowa kuma balaifin tsaye bana zaune tsakaninta da Baffa Usman (Kamar yadda ake kiransa)

Bayanda baffa zaiyi dole yasaki matarsa yanaji yana gani bakuma sonta bane bayayi.

Bayan tagama iddarta labari yazo masa cewa Hafsat (mahaifiyar Aysher ta tafi kano karatun aikin jinya)

Fatan alheri yayi mata tareda da cewa"inda rabon musake zama zamu zauna tare Hafsat.

Anguwar damare takasance anguwa wanda take gauraye da talakawa da masu kud'i.

Gidan inna wuro yakasance d'aya daga cikin gidaje masu sukunin anguwar

Aysher tana zuwa aiki gidan ne bisa neman alfarman da Yadikko tajeyi gidan batare da sanin aysher ba ta samo mata aiki gidan danyin wanke wanke shara da girki dan innawuro tana aiki a Nepa bata zama agida sosai mijinta kuma ma'aikacine a CBN.

DOWNLOAD BOOK{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post