Budurwar da Likitoci Suka Yiwa Karin Girman Duwawu Ta Koka

Girman Duwawu

Wata budurwa mai shekaru 20 zuwa 30 da haihuwa ta koka yadda mazaunanta suke mata ciwo bayan da aka mata karin su.

Ita dai wannan yarinyar da rohoto majiyar mu bai ambaci sunanta ko daga Inda take ba. 

Yace tun farko kawayenta sun hanata yin wannan karin amma tayi burus dasu. Sai gashi yanzu tana ihu da kukan cewa duwawunta tana jinsu kamar wuta akan kunna mata a jikinsu.

Ta kuma ce tunda aka mata aikin karin ita bata ga sun kara girma ba sai azabar ciwon da suke mata, inda take tambayar likitan daya mata aikin anya kuwa yasan aikinsa ko dai kawai kudinta yaci.

Na kusa da ita sunce tun bayan da sukaji tana cewa mata masu manyan duwawu sun fi jan hankalin maza zata je a mata Karin nata suka jawo hankalinta da cewa nata data zo dashi wato follow come bai da matsala amma taki.

Yanzu dai mazaunan na ta sun shiga wani halin inda idan batayi sa'a ba zata yi biyu babu.

Tattara Rahoto: Tonga Abdul Tonga{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post