Buhari ya Taya Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar II Murnar Cika shekaru 65 a Duniya

Buhari Sultan

A ranar Laraba ne Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya bi sahun daukacin al’ummar Musulmi wajen taya Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar III murnar cika shekaru 66 a duniya a ranar 24 ga Agusta, 2022.

Sakon shugaban kasar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a yammacin Laraba ta hannun babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu.

Sanarwar mai taken ‘Shugaba Buhari na murnar cikar Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar III da cika shekaru 66.

Buhari ya bayyana sarkin a matsayin shugaba nagarj wanda ke ci gaba da fafutukar tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a kasar nan ta hanyar ba da shawara akai-akai ga cibiyoyi, kwararru da ma’aikatan gwamnati don bin ka’idojin da aka amince da su.{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post