Me Yasa Wasu Matan Basa Kawo Ruwa Yayin J*ma'i

Kawo Ruwa

Kusan duk mako sai na samu mata sunyi mini wannan tambayar.

Akwai matan da tace shekarunta 35 da aure kuma tana da yara 9, amma har ranar da take magana dani tace bata taba yin zuwan kai ba.

Masu karatu zuwan kai ga 'ya mace shine wani yanayi na kololuwar jin dadi a yayin jima'i.

Dayawa suna dauka cewa ruwan dake fita daga gaban mace a lokacin da ake saduwa da ita shine zuwan kanta.

Ita mace zuwan kanta ba irin yadda namiji yake yi bane ruwan maniyi ya fito daga gabanta ba. 

Shi zuwan kan mace tamkar gaban zakara yake, ba a ganinsa sai dai a jishi. Mace kawai zata ji alamun zuwan kai ne da kuma bayan yazo.

Kamin muyi bayanin yadda mace zatasan tayi zuwan kai, zamu fara ne da bayanin abunda yake hana wasu matan zuwan kai.

Sai dai matsalar ta kasu ne kashi biyu. Akwai matan da sun taba yin zuwan kai, amma daga nan basu sake yi ba. Akwai matan da kwatakwata basu ma tabayi ba.

Masana sun kawo dalilai da daman gaske da suke jawo mace bata samun yin zuwan kai. Wadannan dalilan dai sun hada da:

Bakuwar Jima'i 

Yanada matukar wahala mace ta soma yin Jima'i a yau, ta kuma yi zuwan kai a ranar. Sabanin maza, yanzu zai soma yanzu zai kawo.

Ita mace sai ta dauki wasu lokuta tana Jima'i ne sannan ta soma zuwan kai. Wannan yasa sabbin amare basusan zuwan kai ba sai dai dadin shi Jima'i.

Rashin Gano Mace

Duk wata mace akwai inda yake motsa mata sha'awa akwai kuma abunda yake sa tayi zuwan kai, matsalar shine ba duk maza bane suke iya bata lokacinsu su binciko wannan ba a jikin matansu.

Macen da taba aure zata iya sanin abunda yake sata zuwan kai, ita kuwa sabuwar shiga dole ne har sai mijin nata ya binciko daga nan ne zai dora.

Idan Ma'aurata zasu shekara dubu ba tare da sun binciko abunda yake sa matarsa zuwan kai ba, haka zasu yi ta jimai ba tare da matarsa tayi ba. 

Muddin zaka murza matarka sosai ka tabo mata lungunan jikinta ta hanyar wasa da Jima'i kana iya gano abunda ke iya sata zuwan kai.

Auren Dole

Da yake shi Jima'i ana yinsa ne da kwakwaluwa amma bada zuciya ba, wannan yasa duk mutumin da bai samu natsuwa ba bazai taba gamsuwa a Jima'ince ba.

Matan da aka aura musu mazan da basa so yana da wuya suyi zuwan kai. Bama zuwan kan ba hatta dadin Jima'i ma bazasu ji ba.

Don haka muddin tana tare da wannan mijin har tsawon lokaci haka zata yi ta zama ba tare da yin zuwan kai ba a Jima'i.

Don haka duk yadda mace take da wani damuwa a ranta to babu yadda za ayi ta iya yin zuwan kai har sai ta ajiye wannan damuwar a gefe tukun.

Tsayawar Al'ada

Matan da suka daina yin al'ada koda a baya suna zuwan kai to fa suna iya daina yi a lokacin da suka daina al'ada.

Wani hikiman da Allah SWT Ya kimtsa game da al'adar mace shine, yakan sata yin sha'awa kamin ta soma, tanayi da bayan ta yi wanka, hakan ne yakan sata son kusantar namiji, daga kusantar ne kuma ciki yake shiga sai a samu haihuwa. 

Don haka a lokacin da mace ta daina al'ada sha'awanta game da son Jima'i yana raguwa. Idan ma tayi bata jin dadin sa kamar yadda take ji a baya, rashin jin wannan dadin kuma shi yake hanata zuwan kai.

Shi yasa masana suka tabbatar da cewa da zaran mace ta daina al'ada to yanada wuya tayi zuwan kai duk da yanzu akwai magungunan da tsoffin matan suke amfani dasu domin samun gamsuwa.

Matsalolin Rashin Lafiya

Akwai wasu cutukan da suke hana mata yin zuwan kai a cewar masana.

Cutaka na ciwon zuciya dana shuga duk suna iya hana mace yin zuwan kai. 

Haka nan wasu kwayoyin magungunan da mace take amfani dasu suma suna iya hanata zuwan kai. 

Wadannan sune manyan abubuwan da suke hana wasu matan yin zuwan kai.

Sai dai shi rashin zuwan kan mace baya hanata jin dadin Jima'i. Zuwan kan nata sheke sata kara son mijin datake aure. Don mace bata zuwan kai hakan ba wai yana nufin bazata ji dadin Jima'i bane, sai da wannan kololuwar jin dadin da hakan ke samarwa bazata samu ba.

Sannan rashin zuwan kan mace baida alaka da yin cikinta. 

Mace bada maniyinta ake gina mutum ba. Ita kawai ajiyar abunda zaka gina ake bata saboda itace take da majiyar abunda za a haifa ba uban yaron ba. Wannan yasa ko mace tayi zuwan kai ko batayi ba ciki na iya shiga mahaifarta.

A darasi na gaba zamuyi kawo mahimman wuraren da suke da mace zuwan kai kamin mu kawo darasin yadda mace zata iya fahimtar tayi zuwan kan.

Sanarwa: Wannan dai rubutun Tonga Abdul Tonga ne, shahararen malamin nan fannin auratayya da kwanciyar aure. Za ku iya bibiyarsa ta "Tsangayar Malam Tonga" a shafin Facebook.

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post