Nasarullah: 'Yan sanda sun kashe Masu Garkuwa da Mutane 2 sun Kama 9 a Bauchi

Nigeria Police

Yayin Musayar Wuta 'Yan sanda sun kashe Masu Garkuwa da Mutane 2 sun Kama 9 a Bauchi

Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta yi nasarar kama masu garkuwa da mutane su tara tare da kubutar da mutum daya a kauyen Maina Maji da ke karamar hukuma Alkaleri a jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Ahmed Wakili, shi ya bayyana haka ranar Juma'a a Bauchi, inda ya ce jami'an 'yan sanda tare da hadin gwiwar wasu 'yan banga ne suka kai samame a maboyar masu garkuwar.

Ya kara da cewa an kashe biyu daga cikin masu garkuwar.

Mista Wakili, ya bayyana sunayen wadanda aka kama, sun hada da Ali Ibrahim (20), Damina Musa (22), Yusuf Mohamed (32) da Buba Abdu (25).

Sauran sun hada da Buba Sulaiman (22) da Isah Manu (25) da Sulaiman Yusuf (46).

Ya kuma kara da cewa, biyun da aka kashe yayin dauki-ba-dadin, wani likita ya tabbatar da mutuwarsu.

Kazalika Wakili ya bayyana cewa an kwato Babura hudu daga hannun wadanda ake zargin masu garkuwa da mutanen ne.

"Wadanda ake zargin sun amince da aikata laifin," in ji shi.


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post