Tarihin Adolf Hitler Daga Saliadeen Sicey

Adolf Hitler

Hi-tler ɗan siyasar Jamus ne haifaffen Austriya wanda ya kasance mai mulkin Jamus daga 1933 har zuwa mutuwarsa a 1945. Ya hau kan karagar mulki a matsayin shugaban jam'iyyar Nazi, ya zama shugabar gwamnati a shekara ta 1933 sannan ya ɗauki sunan Führer und Reichskanzler a cikin 1934.

An aifi Hitila ranar 20 ga watan Afirilu na shekara 1889, ya kashe kansa ranar 30 ga watan Afirilu na shekara 1945 bayan an ci Jamus da yaki ( Amma Wasu sunce sojojin Rasha na red Army Ne Suka kashe shi suka kone Gawar).

An haifi Hit-ler ranar 20 ga watan Afrilu na shekara 1889 wato shekaru 133 kenan da suka gabata.

An aife shi a wani gari mai suna Braunau-am Inn, a kasar Austriya kusa da iyakar kasar da Jamus. Shine na hudu a gidansu. Mahaifinsa wani jami'in Custum ne, ya rasu a yayin da Hitler ke da shekaru 14 da haihuwa.

Marubuta tarihin Hitila sun ce bai yi wani dogon karatu ba, ya yi watsi da makaranta a lokacin da ya ke dan shekaru 16 da haihuwa.

Yayi yarintarsa cikin matsaloli masu yawa. Ya na samun 'yan kudaden tallafi da gwamnati ke baiwa marayu, sannan kuma ya na sana'ar zane-zane da kera-keren hannu. Sai dai duk da cewar bai yi wani dogon karatu ba mutum ne mai sha'awar

karance-karance, kuma a wani lokacin har ma ya kan je ya saurari mahaurori a majalisar dokokin Austriya.

Sai dai kuma tun ya na dan samari ya ke nuna kyamar tsarin mulkin demokradiya da tsarin kominisanci.

Hit-ler ya je Jamus a shekara 1913, ya gudo daga Austriya domin gudun kar a dauke shi cikin rundunar soja da kasar. Ya zauna a birnin Munich na jihar Bavariya.

Ya na nan ne yakin duniya na farko ya barke a shekara 1914.

Hitila ya shiga rundunar Sojojin Jamus a matsayin sojan sa kai, kuma ya nuna hazaka da jarumtaka kwarai a cikin harkokin soja, saboda haka ne ma ya samu lambar yabo ta mussamman daga manyan sojojin kasar. A lokacin yakin duniyar, ya samu raunuka har sau biyu wanda tilas aka kwantar da shi asibiti. A karshen yakin ya samu galar Caporal.

Bayan barkewar wani juyin juya hali a Munich, hukumomi sun kafa kwamiti wanda aka dorawa Alhakin binciko gaskiyar al'amarin da ya faru. Hitila ya na daga cikin membobin wannan komiti kuma ya nuna basira kwarai ta fannin jawabin gaban jama'a Mussaman ya shahara wajen kunna wuta ko kuma yafa mata ruwa ta hanyar kalamomin baki.

Wannan baiwa ta bashi farin jini kwarai daga mutane.

A fannin siyasa ya shiga wata karamar jam'iya mai suna DAP wadda ta kunshi ma´aikata zalla masu tsantsar akidar kishin kasa, wadda ta rikide zuwa NSDAP. Ya karbi jagorancin wannan jam'iya a shekara 1921. Ta wannan hanya ce ya fara yada akidarsa ta Nazi.

Kasancewar sa mutum da ya shahara wajen magana, sai ya zama daya daga jigajigen 'yan siyasa a jihar Bavariya. Saboda karfin fada a ji da ya fara samu, ya jaraba yin juyin mulki a birnin Munich a shekara 1923 amma ba yi nasara ba.

An cafke shi, kuma a ka zartar masa da hukuncin daurin shekaru biyar a kurkuku, to sai dai maimakon haka watani tara kawai yayi daure domin daga baya ya samu afuwa. Yayi amfani da wannan dama ta zama gidan yari, inda ya rubuta wani littafi mai suna da jamusancin "Mein Kampf", idan aka fasara da hausa, ya na nufi Yakina! wato ma'ana a cikin wannan littafi ya bayyana dalla-dalla manufofinsa da akidojin sa.

cikin manufofin Hitila ya bayana sha'awa ga akidar nan ta wani masani mai suna Charles Darwin game da fadi tashin rayuwa.

Hitler ya bada fifiko ga wata kabilar Jamus mai suna Aryenne wadda akwai ta a kasashe da dama na yankin arewancin Turai.

A tunanin Hitler duk sauran kabilu na matsayin bayi ga kabilar ariyawan Jamus, wadda yace itace kabilar da ta fi daukaka a duniya, kuma itace ta kamata ta mulki duniya gaba daya.

Hitler yayi mummunar suka ga ya-hu-da-wa wanda ya dangata da annoba a cikin rayuwa duniya saboda haka nema a lokacin yakin duniya na biyu ya sa aka hallaka miliyoyin ya_hudawa.

( Ance Yawansu Ya Kai Miliyan 6 ) Hitila ya sami goyon bayan babbar Cocin Katolika da ke Rum, da ma babban limamin birnin Kudus kan irin mugun nufinsa kan Yahu-dawan Duniya.

A cikin wannan littafi na yaki na Hitila ya bayyana aniyarsa ta mamaye duniya.

A wani abu mai kama da faduwa tazo daidai da zama, lokacin Jamus da sauran kasashen Turai, sun fara tsunduma cikin wata matsalar kariyar tattalin arziki. Ta la'kari da fadakarwa da Hitila ya tsananta yi, sai jam'iyarsa ta NSDAP  ta kara samun karbuwar daga jama'a.

Sannu a hankali magoya bayan wannan jam'iya suka fara daukar shi a matsayin wani abin bautama.

A zaben da aka shirya a shekara 1930 jam'iyar ta samu kujeru.

Wannan babban ci gaba ya sa tilas shugaban kasar Jamus na wacen lokaci Mashal Hindenburg ya nada Hitila a matsayin shugaban gwamnatin Jamus ranar 30 ga watan Janairu na shekara 1933.

Hitila ya shimfida mulkin kama karya, ya kuma haddasa barkewar yakin duniya na biyu:

Wata daya bayan da Hitila ya kama shugabancin gwamnati sai majalisar dokoki ta yi gobara.

Hitila sai ya dora alhakin gobara ga Marinus Van der Lubbe wani jigo a jam'yar 'yan communist wadda ya ke mummunar adawa da ita. Yayi amfani da wannan dama inda ya cafke dubunan magoyan banyan wannan jam'iya. A washe garin wannan gobara sai shugaban kasar Jamus ya rattaba hannu kan dokar tabaci wadda ta ba Hitila cikkaken mulki, sannan daga baya shugaban sake rattaba hannu kan wata sabuwar doka, wadda ta ba Hitler wuka da nama har tsawan shekaru hudu ya gudanar da mulki ba tare da katsalandan din shugaban kasa ba.

Daga wannan lokaci ya fara cin karensa babu babbaka, ta hanyar shimfida mulkin kama karya. Ya soke jam'iyun siyasa da kungiyoyin kwadago, sannan yayi amfani da wannan dama domin kara yada manufofin jam'yarsa.

Shugaban kasar Jamus Hindenburg ya rasu ranar 12 ga watan Agusta na shekara 1934. Hi-tler yayi gadon sa sannan kuma shi ke rike da matsayin shugaban gwamnati da kuma Führer wato shugaban jam'iyarsa.

Hakikanin gaskiya Hitila shi ne ya yi sanadiyar barkewar yakin duniya na biyu.

Tun lokacin da ya wallafa littafinsa mai suna Yakina ya bayyana manufofinsa na mamayar duniya.To kuma gashi dama ta samu, domin shine shugaban kasar Jamus kuma shugaban gwamnati.

A cikin burinsa na mamayar duniya, Hitila ya kuduri aniyar cimma wani buri da ya saka wanda aka fi sani da jamusanci da suna Anschluss: wato ya hade Jamus da  kasashen masu makwabtaka da ita kamar su Austriya da Chekoslobakiya.

Banda wannan kasashe ya aika dakarun Jamus domin mamaye kasashe kamar su Poland, Danmark, Belgium, da Faransa.

Mamayar kasar Poland daga nan ne yakin duniya na biyu ya barke, a shekara 1939. ( Wanda A ka Rasa Rayukan Sojoji Da Fararen Hula Kimanin Miliyan 75 )

An yi ta gwabza fada tsakanin dakarun Jamus da sauran sojojin kawance har zuwa shekara 1945, inda Jamus ta yi saranda.

Marubuta tarihin Hitila sun ce ya kashe kansa a cikin gidansa na karkashin kasa ranar 30 ga watan Afrilu na shekara 1945, amma akwai mahaura game da mutuwar tasa.

Wata ruwaya ta ce ba  a wannan rana ne Hitila ya mutu ba.

Wasu sabbin bayanai na cewa watakila Hitler bai kashe kansa ba. ya samu Ya tsere ne zuwa wurin abokinsa shugaban Argentina aka bashi mafaka, wannan zargi ya sami karbuwa sosai wurin masu son bin kwakwaf, wadanda har hotunan tsufansa ta rasuwarsa wai a 1976 suka wallafa. 

Tserewar Albert Einstein

Baya-hude da ya tsere daga kasar Jamus, Albert Einstein, cikin fargabar cewa Hitila na hada makamai na nukiliya masu kare dangi kaf, ya rubutawa shugabn Amurka na wancan lokacin wasika, inda nan da nan aka karbi shirinsa a sirri Amurka ta fara kera nata makaman na Nukiliya, wadanda guda hudu kawai ta iya kerawa a lokacin. Yanzu suna da dubbai. 

Da yawa daga cikin masana kimiyya na Jamus da Hitila yayi amfani da kwakwalwarsu sun sami yafiya, sun kuma taya gwamnatocin Rasha da Amurka wajen sabbin kere-kere, wadanda suka kaita da samun damar zuwa duniyar wata a 1969.


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post