Tarihin Dalhatu Bin Ubdaidullahi (R.A) Daga Saliadeen Sicey

Dalhatu Bin Ubadiullahi

"Wanda duk ke son ganin shahidi yana tafiya da kafafun sa to ya, dubi Dalhatu dan ubaidullah" inji manzon Allah (SAW)

Dalhatu dan ubaidullahi dan usmanu, dan Amru dan Ka'aban dan Sa'adu dan tanimu dan muratu. Bakuraishe, bataime. Anayi masa lakabi da "Dalhatu khairi".

Talhah ibn Ubaydullah ( طلحة بن عبيدالله‎ ) Ya kasance sahabin annabi Muhammad Muhammad SAW A cikin Musulmin sunna galibi an san shi da  zama daya daga cikin sahabbai goma da Akayi musu busharar Aljanna tun daga nan Duniya, An fi saninsa da rawar da ya taka a yakin Uhud da na Raƙumi, wanda ya mutu a ciki, a wurin Ahlus-Sunnah Annabi Muhammad SAW ne ya ba shi taken “Mai karamci”.

Yana daga cikin musulman farko, wadanda sayyidina Abubakar ( RA) ya kira su zuwa musulunci. Yayi musu jagora wurin manzon Allah (SAW). Ya dandani irin azabar da kafiran makka suka rika ganawa sahaban manzon Rahama na farko. Yayin da ya musulunta shi da sayyidina Abubakar ( RA) sai Naufal dan khuwailad ya kamasu, ya hadasu wuri guda, ya daure da kakkarfar igiya, ya tsaresu wai dan kada suyi sallah da zuwa wurin Manzon Allah (SAW ) ya Allah ya Kara musu yarda.

Manzon Allah ya hada sayyidina Dalha ( RA) da zubairu dan Awwami, a matsayin 'yan uwa, kafin yin hijira zuwa madina. Yayin da musulmai sukayi kaura zuwa madina kuwa sai manzon Allah ya hadasu yan uwanta da Abu ayuba, mutumin madina (mai masaukin manzon Allah SAW na farko).

Sayyidina dalhatu yana daga cikin sahabban Annabi goma, da aka yiwa bushara da gidan Aljanna. Yana daga cikin mutane shidda da khalifa Umar ( RA  ) yayi wasiyar da suyi shawara, su zabi khalhfa tsakanin su. Shine kuma wanda sayyidina umar ya sanya suyi limanci, yayinda bamajushe, Abu lu'ulu'uatu ya soke shi a masallaci..

Bai samu halartan yakin badar ba domin a lokacin manzon Allah (SAW ya turashi kasar sham, shida Sa'idu dan zaidu (RA) domin nemo labarai da sirrin abokan gaba, amma ya halarci yakin uhudu da dukkan yake yaken da akayi bayansa. Ya kuma halarci caffar yarda (bai 'atur ridwan), ya ragargaji ka-fi-rai sosai a yakin uhudu. Ya kare manzon Allah da kansa, ya rike kibiyoyi da aka harbowa Annabi da hannun sa, har sai da yatsunsa suka shanye, aka kuma sare shi ga kai, a cikin wannan hali ya goya manzon Allah a bayansa ya hau dutse da shi. Ya Allah ka kara yarda agare shi.

Sayyidina dalhatu yace " ayakin uhudu manzon Allah ya kirashi da 'dalhatu khairi' (tafiya) a yakin tabuka kuma ya kirashi da 'dalhatu fayyad' (mai kwaranyar da alheri) a yakin hunainu kuma ya kirashi da 'dalhatu judu' (dalhatun baiwa)

Sayyidina Aliyu ( RA) yace " kunnuwana sunaji ma'aikin Allah (SAW) yana cewa "dalhatu da zubairu, makwabta ne a aljanna."

A wani hadisi kuma manzon Allah (SAW) yace" wanda duk yake son ganin shahidi yana tafiya da kafafunsa to, ya dubi Dalhatu dan Ubaidullah".

Haihuwa

An haifi Talhah An Haifeshi A Shekarar 594, dan Ubaydallah bin Uthman na dangin Taym na kabilar Kuraishawa a Makka . Mahaifiyarsa, al-Saaba bint Abdullah, ta fito daga kabilar Hadram. :

Talhah ya kasance dan kasuwa mai fataucin kaya wanda daga karshe ya bar gidajan da aka kiyasta zai kai 30 dirhami miliyan. 

Iyali

Talhah ya haifi aƙalla yara goma sha biyar ta akalla mata daban-daban guda takwas. 

Sayyidina Dalhatu ya Rasu yana da shekaru 62 a zamanin khalifancin sayyidina Aliyu (RA). 

Kabari

Kabarin Talha bn Ubaydullah yana cikin Basra, Iraq. Kabarin yana wani katafaren masallaci wanda yake da gine-ginen zamani.

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post