Tarihin Imam Hussain (AS) Ibn Ali Bin Abutalib daga Saliadeen Sicey

Imam Hussain

Hussain Ibn Ali Bin Abutalib jikan manzon Allah ne, Allah ya yarda dashi, Dan Nana Fatima diyar manzan allah (SAW), uwargidan Aliyu dan Abutalib, dan'uwansa shi ne Alhasan dan Ali dan Abutalib. Hussain shine wanda Yan Shi'a ke darajawa a matsayin daya daga cikin Imamansu na farko.

HUSAINI Suna ne da Allah Mai girma da Daukaka ya zabar ma yaron Imam Ali (AS) na biyu, kamar yadda ya zaba mababban yaron nashi suna Hasan (Amincin Allah Ya tabbata a garesu). An ruwaito ruwaya daga Asma’u bintu Umais (RA) dangane da haihuwar Imam Hasan (A.S), Wanda ya gudana a shekara ta 3 bayan Hijira, da haihuwar Imam Husaini (AS) wanda ya faru a shekara ta 4 bayan hijira. 

Kowannensu bayan an haife shi sai Manzon Allah (S) ya tambayi Imam Ali (A.S) shin da wane suna ka ambaci abin haihuwar? Sai Ali (A.S) yace ban gabace ka ba akan hakan. Sai Manzon Allah (S) yace: Haka nima ba zan gabaci Ubangijina ba.

Nan take sai Jibrilu (AS) ya sauko yana cewa: “Ya Muhammad (SAW), Lallai Allah yana gaishe ka, kuma yana ce maka: ‘Ali a wajenka, kamar Haruna ne a wajen Musa, sai dai kai babu Annabi a bayanka’. Kuma Ka ambaci sunan dan nan naka da sunan yaron Haruna.” Sai Manzon Allah (SAW) yace ma Jibrilu: “Mene ne sunan yaron Haruna ya kai Jibrilu?” sai Jibril (AS) yace: “Sunanshi Shubr” sai Manzon Allah (S) yace masa: “Ni harshena Larabci ne, me hakan ke nufi?” sai Jibril (AS) yace ka ambace shi da ‘Hasan’. Yayin da shekara ta zago aka kara haifan wani jaririn kuma, Sai Jibril ya sake dawowa ya maimaita kamar yadda akayi a baya, sannan yace Allah ya yi umurni da ka saka ma yaronka sunan yaron Haruna, wato ‘Shubair’, sai Annabi ya kara neman ma’anarsa, sai Jibrilu (AS) yace masa “Husaini”. Mai karatu yana iya duba Littafin ( Zaka’iru Ukba, shafi na 120.) 

Wannan ke nuna mana cewa sunan Imam Husaini (AS) zanannen suna ne da Allah (SWT) ya ma Annabi Muhammad (SAW) wahayinsa, kuma Annabi (SAW) ya rada masa wannan sunan da Izini kuma da umarnin Allah (SWT). 

Hakan kuwa ya ishe Imam Husaini (RA) da ‘Dan’uwansa Imam Hasan (RA) girman daraja da matsayi da falala. Ance sunan Imam Husaini (AS) a cikin Attaura shine ‘Shubair’ din, a yayin da

kuma a cikin Injila aka kira shi da ‘D’aba’. Kenan sunan wannan bawan Allah din, tare da sauran zababbu ‘yan’uwan Sa (AS), rubutacce ne a cikin saukakkun littafan sama tun kafin a haifesu da shekaru masu yawan gaske.

ALKUNYARSA 

Ana ma Imam Husain (RA) kinaya da alkunyu daban daban, amma wanda yafi shahara shi ne “Abu Abdullah”.Baya ga shi kuma ana ce masa “Abu Ali al-Asgar”, haka kuma ana kiransa da “Abul A’immah (RA)”. 

LAKABOBINSA:

Lakabobin Imam Husaini (RA) kuwa suna da yawa, amma kadan daga cikinsu, sune: Al-Mubarak, As-Sibdi, Ar-Raheed, Ad-Dayyib, As-Sayyid, Raihanatun Nabiy (S), Al-Wafiy, Al-Zakiy, Al-Waliy, Sayyidus Shuhada, Sayyadis Shababu Ahlal Janna, Al-Waliyul Kabir. Da sauran lakabobi tabbatattu a gare shi da ake kiransa da su.

ZOBEN IMAM HUSAINI (AS) Imam Husaini (RA) ya na da zobe, kasancewar sanya zobe na daga Sunnar Manzon Allah (SAW) da Ahlulbait (AS), har ma ya zamana sanya zobe a hannun dama na daga cikin alamomi ko siffofin da ake gane mabiyan Ahlulbait (AS) a duk inda suka tsinci kansu, musamman ma a lokutan baya. Dan haka a jikin zoben Imam Husaini (AS) an rubuta “-HasbiyalLah-” ne. Imam ya kasance daga cikin Sahabban Bargo, na’am, Ma’abota bargo su biyar ne, sune; Annabi (SAW) da Imam Ali da Sayyida Fatima da Imam Hasan da kuma Shi Imam Husaini (AS). Wadanna ma’abota bargo din, sune wadanda Allah (T) ya tafi da dauda da kazanta daga garesu, kuma ya tsarkake su tsarkakewa. Wanda akwai Hadisin Bargo (Hadisul Kisa’i) wanda aka ruwaito shi daga Sayyida Fatima Azzahara (SA).

Imam Husaini (AS) ya rayu tare da kakansa Manzon Allah (SAW) tsawon shekaru bakwai ne, dan haka ya kasance rainon Annabi (SAW) ne, kuma sanyin idanuwansa, kuma ma bangaren jikinsa mai albarka (AS). 

Imam Husaini (AS) kuma ya rayu tare da Mahaifinsa Imam Ali (AS) shekaru talatin da bakwai. ya kuma rayu da ‘Dan’uwansa Imam Hasan (AS) shekaru Arba’in da bakwai. kuma tsawon

lokacin Imamancinsa da Halifancinsa na Manzon Allah (SAW) a bayan Yayansa Imam Hasan (RA) shi ne, shekaru goma da watanni. 

HAIHUWARSA

Dangane da haihuwar Imam Husaini (RA) kuwa; An haife shi ne a ranar 3 ga watan Sha’aban a shekara ta bakwai bayan Hijirar Manzon Allah (SAW). 

Annabi Muhammad  SAW a irin wannan rana Kamar yadda aka ruwaito daga Abdullahi ‘Dan Abbas (RA) a cikin littafin Fara’id-as-Simdain. Imam Husaini (RA) ya rayu watanni

shida ne a cikin Mahaifiyarsa, sai aka haife shi, kamar yadda Muhammad bin Dalha As-Shafi’I ya ambata. Kuma dangane da

shi (Imam Husain) ne Allah (SWT) ya saukar da fadinsa “Da

daukan cikinsa da shayarwarsa watanni talatin ne.” Dan haka ma ma’abocin littafin( ‘al-Kamil-az-Zi yaaraat’) ya kawo maganar Imam Jafarus Sadik (RA) dake cewa: “Ba’a haifi wani abin haihuwa a cikin watanni shida ba, in banda Isa ‘Dan Maryam (AS) da Husaini ‘Dan Ali (RA).” Dama Maryam (AS) ta dauki cikin

Annabi Isa (AS) har na tsawon watanni 6 ne ba tare da an iya fahimtar hakan ba sai daga baya ta haife shi.

Imam Husaini (AS) yafi kowa kama da Manzon Allah (SAW), musamman ma daga kirjinsa zuwa tafin kafansa, dukkansu

kamar na Manzon Allah (SAW) ne. kamar yadda kuma aka bamu labarin cewa Imam Hasan (RA) kuma yana kama da Annabi

(SAW) ne daga kirjinsa zuwa samansa. Kuma Imam Husaini (AS) ya kasance matsakaici ne wajen tsawo, ba dogo bane ba kuma gajere  bane. Yana da yalwar kirji. To kuma har wala yau Imam Husaini (AS) yana kama da Imam Ali (AS) ta samansa (daga kirji zuwa kai). Kunga kuwa ta ko ina ya kure ma kyau kenan MANZON ALLAH (SAW) YANA CEWA:

“Husaini daga ni yake, kuma ni ma daga Husaini nake. Allah ya so wanda yake son Husaini.”

Matsayin Imam Husaini (a.s)

Hakika Abu Abdullahi al-Husain (RA) na da babban matsayi. 

Bayan ayoyin Alkur'ani da suka ambaci matsayinsa cikin matsayin Ahlulbaiti (AS), wadanda muka ambata a baya, kamar su Ayar Tsarkakewa, Ayar Mubahala, Ayar Kauna da sauransu; akwai hadisan Annabi masu yawa da ke nuna girman matsayinsa da daukakar darajarsa. Daga cikin su akwai:

1, Abin da ya zo cikin Sahih al-Tirmizi cewa: Manzon Allah (SAW) ya ce: "Husaini daga gare ni yake, ni kuma daga gare shi nake. Allah Ya so wanda ya so Husaini. Husaini jika ne daga cikin jikoki(2).

2, An ruwaito daga Salman al-Farisi, ya ce: na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: "Hasan da Husaini 'ya'yana ne, wanda ya so su ya so ni, wanda kuma ya so ni Allah zai so su wanda kuwa Allah Ya so zai shigar da shi Aljanna. Kuma wanda ya fusata su ya fusata ni, wanda kuma ya fusata ni Allah zai yi fushi da shi, wanda kuwa Allah Ya yi fushi da shi zai shigar da shi wuta(3)"

3, An ruwaito daga Ali bin Husaini daga babansa, daga kakansa (AS.), cewa Manzon Allah (SAW) ya kama hannun Hasan da Husaini (AS) sannan ya ce: "Wanda ya so ni ya kuma so wadannan biyun da babansu da mamansu, zai kasance tare da ni ranar kiyama(4)".

Dabi'un Imam Husaini ( RA)

Hakika kasantuwan Imam Hasan (a.s) ya tashi ne karkashin kulawar kakansa Manzo (SAW), babansa Ali da mahaifiyarsa al-Zahara (AS), ta sa dabi'unsa na misalta sakon Allah Madaukaki a tunance, aikace da halayya. A nan za mu bayar da wasu 'yan misalai.

1- Shu'aib bin Abdul-Rahman ya ruwaito cewa: "An ga wani tabo a bayan Imam Husaini (RA) a Karbala; sai aka tambayi Imam Zainul-Abidin (RA) game da shi, sai ya amsa da cewa: "Wannan ya samo asali ne daga buhunan abinci da yake dauka a bayansa yana kai wa gidajen matan da mazansu suka mutu da marayu da miskinai".

2- Ya taba bi ta wajen wasu miskinai alhali suna cin abinci a akushi, sai suka yi masa tayi, sai ya sauka ya ce: "Lallai Allah ba Ya son masu girman kai", sai ya ci abincin. Sai ya ce musu: "Na amsa muku, to ni ma ku amsa min." Sai suka amsa, suka tafi tare da shi har zuwa gidansa, sai ya ce wa matarsa: "Fito da duk abin da kika adana (5)".

3- An taba ce masa: Me ka fi tsoro daga Ubangi-jinka? Sai ya ce: "Babu mai amintuwa daga ranar kiyama sai wanda ya ji tsoron Allah a duniya".

4- A daren goma ga watan Muharram Imam Husaini (a.s.) ya bukaci rundunar Umayyawa 'yan adawa, da su jinkirta masa wannan daren yana mai cewa: "Don muna so mu yi salla ga Ubangijinmu da daddare mu kuma nemi gafarar Sa, domin Shi ya san ni ina son yin salla gare Shi da tilawar LittafinSa da yawan addu'a da istigfari".{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post