A Kan Yajin Aiki: SERAP Da Wasu Dalibai Sun Maka Shugaba Buhari A Kotu

Shugaba Buhari

Kungiyar dake kare hakkin bil’adama ta Najeritmya wato SERAP da wasu manya-manyan daliban Najeriya guda biyar sun maka shugaban kasa Muhammdu a kotu tare da wasu biyu kan yajin aikin ASUU,

Sauran mutanen guda biyu da SERAP da daliban suka maka a kotun sun hada da ministan kwadago Chris Ngigge da kuma ministan shari’a Abubakar Malami.

Inda suka bayyana a karar tasu cewa gwamnatin ta tauye masu hakkinsu na damar samun ilimi sannan kuma yajin aikin yasa ana bata masu lokaci da dama.

Kungiyar malamai ta ASUU ta kasance tana yajin aiki tun ranar 14 ga watan Febrairu kuma har yanzu bata janye ba, wanda hakan yasa dalibai sukayi watanni bakwai a gida basa zuwa makaranta.

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post