Alhamdulillah: Kotu Ta Aike Da Dan China Da Ya Kashe Ummita Zuwa Gidan Yari A Kano

Frank Geng

Wata kotun majistare mai lamba 30 da ke zaman ta a titin Zangeru a jihar Kano ta tasa keyar wani dan kasar China mai suna Frank Geng Quanrong, mai shekaru 47 zuwa gidan yari.

A na tuhumar Quanrong da laifin kashe tsohuwar budurwar sa, Ummukulthum Buhari a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa Quanrong ya bi marigayiya Ummukulthum har gidan iyayenta da ke Kano, ya kutsa cikin dakinta sannan ya riƙa daɓa mata wuka a yammacin ranar Juma’a.

Sai dai kuma a yau Laraba ne rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gurfanar da shi a gaban kotu.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Hanif Sanusi Yusuf, ya tuhumi Quanrong da laifin kisan kai,  wanda ya ci karo da sashe na 221 na dokar hukunta manyan laifuka.

Alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Oktoba.


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post