[Book] AbdulMalik Bobo Complete by Billy Abd

AbdulMalik Bobo

BOOK INFO

Name AbdulMalik Bobo
Author Billy Abdul
Size 634KB
Format TXT
Category Love Story
Modified Date 20/09/2022
Price Free

BOOK DESCRIPTION

Sauke cikakken littafin marubuciya "Billy Abdul" mai suna "AbdulMalik Bobo" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

BOOK TEASER

Kowa ka kalla yana harkokinsa acikin makarantar, wasu karatu sukeyi wasu kuwa hira da samarinsu ko k'awaye.

Shigowar wata bak'ar mota wulik cikin makarantar shine yaja hankalin mafi yawan d'aliban.

Safna tasaki Baki da hanci da ido itama tana kalo.

Motar tatsaya daidai wata bishiyar dalbejiya, ayanzu kallo yakomane akan Wanda zai fito daga cikin wannan mota mai k'yau da d'aukar hankali.

K'afarsa yafara zirowa k'asa maisanye da sauciki na farin takalmi, yakuma zuro d'ayar itama, saikuma yafito gaba d'ayansa.

Ajiyar zuciya safna ta sauke tareda fad'in ya salam!.

Zeenat tad'ago tana kallonta Dan ita kokad'an batasan bikin da akeyiba, tasaka iyafis akunne tana wayane.

Safna wai lfy mikike kallone haka kamar wata sakara?. 

Safna da bakinta yaymata nauyi takasa cewa uffan, tad'aga hannu dak'yar tanuna mata matashin saurayin dake tsaye, Wanda ak'alla zaikai shekara 33 aduniya.

Masha ALLAHU zeenat tafad'a itama tana mik'ewa tsaye.

Farine sosai dogo kuma dankuwa yanada tsayi sosai, kallo d'aya zaka masa kagane k'ak'k'arfane saidai bashida k'iba, masha ALLAHU akwai k'yawun fuska, gashi kuma ya k'awata fuskar tasa da saje bak'i sid'ik, yakwanta sai wlk'iya yakeyi, sanyake da farar shadda wando da Riga d'inkin zamani, kayan sun masa k'yau.

Tunaninsu yatsaya lokacin dasukaga ya sunkuya yafiddo wata yarinya mai tsananin kama dashi, "bazata wuce shekara 6 ba aduniya.

Sanye take da doguwar riga ja iya kwaurinta Dan batakai k'asaba, ank'awata adon rigar da fararen filawoyi, kanta kam kalbace irin mai nannad'ewarnan kamar igiya (twisting), yasha ribom ja da fari, sai lilo sukeyi.

Ta rik'e d'an k'ugunta da hannu biyu tana kallon saurayin, baby inanenan mukazo?, tafad'a tana bin ko ina da kallo.

Murmushi yay mata Wanda yazauta dayawan 'yammatan gurin, musammamma safna, shima yarik'e k'ugunsa baby nan makarantace, munzo wajen uncle Hamza ne.

Lah baby dama uncle Hamza baigama makarantaba har yanzu?, yafayi babba sosai?.

Kansa yadafe ya ce, "o,o me baby, kefa magana bata k'are miki, kinga muje ciki saiki tambayesa.

   'Yar dariya tayi tareda kama hannunsa suka nufi office d'in uncle Hamza, Wanda yakasance lecturer a makarantar.

Cikin farinciki uncle Hamza yamik'e cike da murmushi yana fad'i oyoyo Nawal d'ina.

   Itama sakin hannunsa tayi taje da gudu tashige jikin uncle Hamza, yarungumeta yana juyi da ita suna dariya.

    Shikam yajingina da k'ofa yana musu murmushi, uncle Hamza ya ajiye Nawal suna sauke numfashi da dariya.

    Sai sannan ya kalli saurayin, cikin zolaya ya ce, "oyoyo my Bobo!.

    Shima hararsa yayi cikin wasa, kace hakafa yanzu, bayan baka kulaniba tun d'azu sai baby.

   Hhhhhh afuwa kasan nida Nawal ba'a shiga tsakani, daga ina haka?.

     Bobo yayi murmushi yana sauke numfashi, wlhy daga gidansu Ni'ima muke kasan mama babu lfy shine nace bari mubiyo mugaisheka.

    Kai amma naji dad'i wlhy sosai, amma yajikin mama?, da sauk'ika gsky.

   To ALLAH yak'ara sauk'i, nima anjima nashiga nak'ara dubata.

   Okey ALLAH yakaimu.

Surutu Nawal takema uncle Hamza babu ko k'ak'k'autawa, shikam sai dariya yakeyi.

   Bobo kam yamaida hankalinsa akan latsa wayarsa.

    Aka kwankwasa k'ofar.

Uncle hamza ya ce, " ashigo."

  Safna ce da zeenat k'awarta, risinawa sukai suna gaishesu, idon safna nakan bobo.

   Uncle Hamzane kawai ya amsa, amma Bobo ko d'agowa baiyibama.

   Safna incedai lfy?, uncle Hamza yatambaya yana kallonsu.

   Zeenat ta zunguri safna dake kallon Bobo babuko k'yafta ido.

   Uncle Hamza yana kallonsu, Dan haka ya girgiza kai.

   Ina saurarenku yak'ara fad'a idonsa akansu.

    Um....um sir dama..... Saikuma tayi shiru tana satar kallon bobo.

    Bobo yad'ago yad'an kallesu fisha saikuma yamik'e, Ya Hamza bari muwuce mubarka da d'alibanka.

   Baby oya tashi muje.

    "Kai bobo da wuri haka?, cewar uncle Hamza yana kallonsa.

    Karka damu gobe idan ALLAH yakaimu zanshigo na gaida aunty Ruky, baby taso mana.

    Nawal ta mak'ale kafad'a zatayi kuka, a'a nidai zan zauna wajen uncle Hamza.

     Harararta yayi baby banason rigimar banza fa kinsani, idan nabarki da aikinsa zaiji kokuwa da shegen surutunki magananniya.

    Dariya uncle Hamza yayi, yashafa kumatun Nawal, kinga my durling kibisa kuje, idan natashi aiki, zanzo gidan Ammi na d'aukeki nakaiki wajen ya Ahmad ko?.

    Da sauri ta d'aga kai tana 'Yar dariya, by by uncle.

   By my Nawal.

  Hannu bobo yabashi sukayi musabaha yafita rik'e da hannun Nawal.

   Duk abinnan yana faruwane agaban su Safna.

   Safna tabisu da kallo kamar ta had'iyeshi.

    Murmushi uncle Hamza yayi, Dan yasan K'anin nasa yayi sata batareda yasaniba.

   Ina jinku yafad'a yana maids hankalinsa kansu.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post