[Book] Bintalo Complete Hausa Novel by Dee Love

Bintalo

Title: Bintalo

Author: Dee Love

Category: Short Story

Doc Size: 457KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2018

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya "Dee Love" mai suna "Bintalo" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: Bintalo yarinya ce 'yar kimanin shekaru goma sha shida, bak'a ce wankan tarwad'a,ita ba doguwa ba,kuma ba gajera ba, tana zaune a hannun kakarta ta wajen mahaifiyarta a k'auyen birwa, sakamakon rasuwar iyayenta.

Malam Bala da dijen bala, (iyayen Bintalo) sun rasu ne sakamakon gobara da ta taso musu cikin dare, daidai lokacin da aka kawo wutar NEPA mai k'arfin gaske, ta mamaye su gaba daya babu abinda ya tsira a gidan.

A lokacin an yaye bintalo tana hannu kakarta wato hajiya hauwa (Inna)..... Tun bayan rasuwarsu Inna ta rok'i dangin Malam bala akan su bar mata bintalo ta cigaba da kula da ita, haka suka hakura suka bar mata bintalo ta cigaba da kula da ita har ta girma, ba karamar soyayya Inna take wa bintalo ba,duk da kasancewar bintalo bata jin magana sosai.

*******************

Ihu take zundumawa, Inna kuwa ta daddane k'afuwan sai faman jamata su takeyi tace "ahh to, ai duk wanda yace bazaiji magana ba,ya dunga shan wahala a rayuwar sa, yanzu meye amfanin tsokana, sun biyo ki kin fad'i, wannan k'afar ma sai munje wajen mai gyara ya duba ta" ta fad'a tana d'aga kafar, ita ko sauke numfashi take da kyar ga gumi dayake keto mata, amma duk da haka bata fasa magana ba "ki barni da su kawai Inna, zan ci gidansu ne bari na warke Allah sena rama".

Hara rarta Inna tayi tace "zaki rufe min baki ko sai na k'arasa k'afar, mara kunya kawai, sai kinje kin yo tsokanarki,nikuma kizo ki cikani da kurin banza, tashi ni muje in kaiki wajen Malam Musa ya dubaki kafin dare yayi ki hana ni barci".

"To Inna d'an kamani in mik'e bazan iya ba"

Seda ta harareta sannan ta jata suka nufi wajen Malam musa mai gyaran k'ashi...... Bintalo kenan, jikar Inna ayi fad'a ayi dad'i.

Suna zuwa wajen Malam Musa kuwa suka same shi, bayan sun gaisa Inna tace "Malam kaganta nan, taje tayi abinda tasaba (Tsokana) suka biyota ta fad'i ta buga k'afa, kaga harta kumbura" ta karasa maganar tana janyo k'afar bintalo, ita kuma ta saki wani ihu, dan zafi take mata ba kad'an ba.

Murmusawa Malam Musa yayi kafin ya kalli bintalo yace "bintalo 'yar Inna, ga tsokana ga tsoro" kirarinta kenan, ya janyo k'afar ya fara tofa addu'a kafin ya fara jan k'afar, ihu ta dunga zundumawa tana "dan Allah Malam musa kayi hakuri ka sakar min k'afa, wallahi bazan k'ara ba na tuba nayi nadama" ko sauraronta baiyi ba, Inna kuwa tana jin kukan da bintalo takeyi har cikin ranta, dan komai bintalo zatayi, bata k'aunar taga wani abu yasameta, daurewa kawai take yi ta rurruketa, kafin ta farga, sai ji tayi bintalo tasaki fitsari a zaune, da sauri ta saki salatati tana sallallami "wato yarinyar nan kullum lamarinki k'ara cigaba yake, kina girma kina k'ara shashancewa ko" ita dai bata ce komai ba, illa maida numfashi da takeyi.

Malam ne yace "Inna rabu da ita haka mana, ba yin kanta bane azabar ciwo ne".

"Allah ya kyauta" Inna tace tare da kwance bakin zaninta ta dauko naira talatin ta bawa Malam suka mik'e zasu tafi, sukayi sallama, Malam yayi musu Allah ya kiyaye gaba.

Har sun kai bakin k'ofa bintalo ta juyo tacewa Malam "Malam mugu sai anjima,dana sani ma tun tuni na tsula maka fitsari ka sakar min k'afata" bai ce mata komai ba,sai ma dariya daya dungayi, dan shi a ganin sa yarinta ce, Inna kam hak'uri ta dunga bashi yace bakomai yarinta ce wata rana sai labari...... Haka suka koma gida bintu sai mita takewa Inna wai ta kaita wajen Malam mugu duk yabi ya murmurd'e mata k'afa, Inna bata tanka mata ba haka har suka k'arasa gida.

Ragowar tuwon da basu cinye ba na jiya ta dauko zata dumama musu, ita dai bintalo tana zaune bisa tabarma Inna ta had'a wuta ta dora tuwo, duk tana kallonta har ta gama ta juyoshi a cikin wata k'atuwar sameera, ta kawo kan tabarma ta ajiye, seda ta ciko kofin silva da ruwa sannan tazo ta zauna.

"To bintalo sako hannu muci, shike nan shi na juyo" tabe baki tayi tace "Tabb Inna! Wannan tuwon fa tun na jiya da safe, nifa gaskiya bazanci ba,kici abinki, ni kibani kud'i kawai inje wajen huda cika in siyo awara, nasan yanzu tana nan tana soyata" tana karasawa ta juya kanta ta kalli gefe, Inna tace "yanzu wannan tuwon ne da ransa da lafiyarsa kice bazakici ba, ai shikenan, amshi kije ki siyo awarar kuma kidawo min da chanji ashirin zaki d'auka,yunwa ce dai zata isheki, dan bazaki had'a tuwon dawa da awara ba" ta karasa tana mik'a mata naira hamsin.

Da kyar ta mik'e tana d'ingisawa ta fice, harta kai k'ofa Inna tace "saura kiyo halin naki, maza kisiyo kidawo gida" bata tsaya bata amsa ba tayi gaba abinta..

Tafiyar minti uku ce ta kaita k'ofar gidansu huda cika mai awara, tana zuwa ta tadda akwai layi sosai, kusa da kaskon ta samu ta tsugunna, ganin tana d'ingishi ne yasa huda tace "mutuniyasss ya akayi ne naga kina d'ingisawa?" Gyara zama tayi sosai tasa hannu cikin kwandon da ta tara awarar ta d'auki guda tafara ci kafin tace.

"Wallahi huda cika d'azune Inna ta aikeni, shine na had'u da habee a hanya na harareta shine suka biyoni ita da wa'yan nan shegun k'awayen ta zasu daken shine na arta a guje, na bi ta gonar mai gari ganyen masara ya rufemin fuska na fad'i na buge k'afa, kinga saida Inna ta kaini gidan Malam Musa, har fitsari nayi a wando sabida azabar ciwo, ai ina warkewa zanje har gidansu habee na ci uban.

Kan ta k'arasa taji mutanen wajen sun kwashe da dariya, itama huda dariyar take amma ta  ciki-ciki tayi, cikin b'acin rai bintalo ta mik'e tsaye tace "ubanwa kukeyiwa dariya?" Wata yar budurwa ce tace "ya bazamuyi dariya ba, munji kina cika bakin zaki ci uban habee, bayan kaff kauyen nan kowa yasan ke matsoraciya ce, sai shegiyar tsokana" suka k'ara bushewa da dariya, cikin b'acin rai bintalo ta rarumo wannan budurwar suka hau kokawa, ji kake tussss sun fad'a cikin kaskon awara..

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post