[Book] Doctor Deejert Complete by Xeyyneb

Doctor Deejert

Title: Doctor Deejert

Author: Xeyyneb

Category: Love Story

Doc Size: 308KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2020

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya Xeyyneb mai suna "Doctor Deejert" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: *Q*atuwar estate ce

(Unguwa).

wacce ta tara dangi da 'yan uwa a cikin ta,

zaman lpia a koda yaushe babu fad'a bare haniya a cikin wannan kyakkyawan ahalin,

Alhj Abdul samad

(Kakus) shine  dattijo na gari  fulanin usuli, ma'ikacin gobnatine mai  babban matsayi , 

danginsa ma ma'aikatan government ne irin qusoshinnan wanda suka jiqu da nera.

Riqaqqun 'yan boko ne family n.

Tun bayan rasuwar iyayen alhj Abdul samad dayake shine babba a dangin  ya gina wannan qatuwar unguwa da qayatattun gidaje na bugawa a mujalla ya gayyato danginsa suka zauna a tare sbd son zumunci dake garai .

babu abinda babu a cikin estate din kama daga islamiyya, boko, place ball

( wajen qwallo)

Irin wajajen exercise (wajen motsa jiki)

Irinsu oasis da qaton swimming pool and library

(dakin karatu,)

Alhj Abdul samad (kakus) ba qaramin dadi yakeji ba, duk in ya waiga yaga danginsa kewaye dashi ta ko Ina.

matan sa 4 ,

ta farkon sunanta hjy zulfa'u, sai ta 2n itace hajy zulaihat, sai ta 3n hjy baraka, ta 4n itace hjy xainab.

Sai-dai  Allah bai basa haihuwa ba, gashi har girma ya soma cimmasa,

kullum cikin roqon Allah yake akan ya azurta sa da zuri'a d'ayyaba, 

da yake ubangijin mu Allah sami'uddua'une ,

sai gashi haihuwa ta bud'e wa matan sa .

hjy zulfa'u Nada maza 3,

Sulaiman da Mahmoud da musa,

Sai hjy zulaihat Nada Abdul qadir ishaq, saima ,

Sai hajy baraka nada saddiqa da kuma saliha .

sai hjy xainab Nada nmj 1 Abdul Hakim.

to daga nan kuma sai Allah ya dauke musu haihuwar.

Haka suka taso har ya zuwa girman su .

Anan cikin dangi suka xabi mataye suma matan suka zabi mazaje akai bikin tare, anan cikin estate  suka zauna suma , riqe da aikinsu na government mai tsoka .

haka suke rayuwar su cikin farin ciki.

Zuwa lokacin alhj Abdul samad tsufa ya cimmasa yayi ritaya , 

yanzu 'ya'yansa suke kula estate d'in,

Kullum zaka samesa a qaton falon sa,

 saye da medical glass mai q'ara q'arfin ido,

 yana lazumi ko karanta Qur'an KO daily trust, ko kallon tashar larabawa ta wa'azizzikan sunnah,

d'an kyakkyawn farin gemun sa ba qaramin kyau yaiwa tsohon nan ba, wannan kenan.

babban d'an hjy zulfa'u wato  sulaiman  sunan matarsa sailuba, d'ansa na farko shine  hesham,

Sai Mahmoud na 2 sunan matarsa husna dansu 1 sunan sa akram,

Sai musa na 3 sunan matarsa lubabatu  'yarsu daya sunan ta basma , 

Sai babban d'an hjy zulai wato Abdul qadir sunan matarsa haseena da yarsa miemie   , sai na 2n ishaq nada maza 2 , Salem da nura, sai 3n macen wato saima Nada mace 1  jawaher ,

Sai babbar diyar hjy baraka wato saddiqa tana da nmj  d'aya aslam , sai ta 2n saliha  itama 'yarta 1 sunan ta deejert, sai   dan hjy xainab wato Abdul Hakim babban dan sa shine saifullahee

Suna kiran sa da saif.

duka samarin gidan da 'yan matan gidan kullum suna liqe da kakansu alhj Abdul samad wanda yanzu jikokinsa sun canza masa suna da *kakus* suke kiransa , ....

A matan deejert babba Wanda a satinnan ta amshi result Nata na shedar zama cikakkiyar doctor, burinta knn a rayuwa kasantuwarta  likita.

Sai mai bi mata basma sai miemie sai jawaher, dayake Kansu d'aya baa gane babba a cikin su, suna matuqar qaunar junansu , 

a cikin  samarin gidan saif ne babba sannan sai akram sai hesham sai salim sai  nura sai aslam ,

***

cikin takun hankali da nutsuwa dejeert ta shigo cikin gidan, Kai tsaye falon kakus ta nufa , sanye take da riga irin 'yar q'asar Morocco d'in nan ta yane kanta da siririn  mayafi , kyakkyawa ce ta bugawa a mujjala yarinyar ,

Tamfar shuwa Arab,

duk da kingin 'yan matan gidan suma akwai kyau,.

amman Nata na daban ne ,

 Sam magana bata damu deejart ba, 

sai ta zama dole take yinta , 

shiyasa samarin gidan ke kiranta da miskila, 

a duk samarin  gidan bamai nuna wa  'yan  mata gidan mugun ta Kala 2 sama da yaya saif ,

dan shine dodonsu ,

 wani masifar kwarjini kyansa ke Mata  a ido , hatta su basma su ma shakkunsa suke, duk rashin kunyar su wa sauran samarin gidan kuwa. 

Shi daban yake dasu,  kullum fiskarsa a had'e  d'aure zaka ganta, ba wasa Sam , amman hakan bai tauye sihirtaccen baiwar kyan Saba, handsome ne na fad'a a kwatance , har cewa suke dan yaga yana da kyau ne shiyasa yake yin yanda yaso?"

Kuma kakus bayya son ace ga laifinsa ,

har tsoro suke kada  tsautsayin wani case ya hadasu dashi , 

dan jawaher ma descipline master take ce masa.

Haka rayuwar deejert take silently

sabanin kingin 'yan matan gidan wato jawaher , basmah miemie,

 in suna waje sai ansan suna nan.

***

"Wash kakus wlh nagaji , cewar  deejert data kwantar da kanta a kafadar kakus tana shagwaba mai marairaicewa,

Shafo kanta yayi yace,

" shalelena  sannu, ai aikita  likita sai an daure daman"

Wad'an nan fitunannun 'yan uwannaki basu dawo ba su kuma?"

turo d'an mitsitsin bakinta tayi jawur lips din dasu ,

 zatayi magana knn ta hango su basma sun biyo jawaher da gudu sun iso falon suna rige rigen isa gun kakus,

 Kai tsaye jawaher ta ruqunqumesa tana fad'in "hey kakus munyi missing naka duk yau school ta boyemu, 

hot lecture akai mana yau from 1 to 4  shiyasa mukayi delay na dawowa  ,"

 ta qarasa mgnr tana jawo furfurar gemunsa tana dariya, 

casbin hannun sa ya  shaud'a mata , wata uwar tsuwa jawaher tayi ,

da sauri ta saki gemun ta miqe tsaye tana rarraba ido tare da Mirza  wajen da casbin ya sauka,

 habawa tuni basma da miemie suka hau qyalqyala mata  dariya harda dafe ciki ,

da gudu jawaher taje ta rungume deejert tana fadin

"sis deejert kin gansu ko sunamin dariya😕?"

murmushi tayi tace 

"Sorry sis  jawaher, 

tana dan bubbuga bayanta , ta jiyo Kansu basma  ta watsa musu harara da dan siririn tsoki , tace  " kunfaye  shirme pa ladies d'in nan 😏"

basma tace "anyi din ay maganin abin mu gani in kin isa,

yarinyar nan kifita hanyata fa koda ke nike ne ma tukun👉🏻?,"

" hhhhh Ku ware kawai ladies a fidda raini cewar miemie ,

Deejert ta miqe tsaye taja tsoki taqi sake cewa komi ta kwashe books d'inta ta nufi labirary.

Da kallon harara miemie tabi deejert dashi tace "Mtss banza miskila kawai da ita   "😏 

 Tuni jawaheer ta hasalo tace karki qara cemata banza wlh kona dakaki a wajennan, tuni wajen ya kaure da hayaniya ,

 ita kuwa wadda akeyi dominta tuni tai ficewarta tana fadin ku kuka sani dai , badani zakuyi wannan hayagagar ba ,

Kakus yace " kudai kamar zakaru dakun hadu sai fad'a?."

Nan anjima kad'an kuma a tare za'a ganku kuna fira lpia,

Wai  Yaushe zakusan kun girma ne...?"

Cikin kakkausar muryar da suka San mamallakinta sukaji yace "Kakus qyaleni dasu , jikinsu Zan tsumamasu yanzun nan wlh kuwa , dan haka kowacenku ta iso nan da jan gwiwa and hands up,😡".  

A zabure suka juya suna kallon qofar falon ,

" wayyo yaya saif plsss Kai haquri ",

tuni ya Fara zare belt din jeans d'insa

Yace

 " tun dazun kun cikamun kunne da shouting Ina  aiki a side na , Ammn hayaniyar ku ta hanamun nutsuwa? wlh sai jikinku ya gaya muku yau , tuni ya nade belt din a hannun sa, yace kuma duk wacce ta kuma yi man magiya sai nazo nan nayi wasan ball da ita na fasa mata baki yayi jini sannan.

Wajen zaman kakus suka juya a tausaye,

 wayam ba kakus ba alamar sa ,

 yau sudai sun shiga 3,

a haka suka dinga tafowa gunsa da  Jan gwiwowi hannuwan su  a  saman Kai

suna hango Nisan wajen da ke tsakanin su dashi habawa tuni suka soma zubar qwallan hango wahala, yau sun shiga hannun mugu yaya saif...

Da rarrafe da Jan gwiwa suka isa wajensa , wajen qatuwar harabar gidan ya fiddo su yace su dinga Tsallen kwado da Marin kumatunsu kuma duk shegiyar da batayi sauri ba saiyaci ubanta ,ba arxiqi suka dinga yi ba qauqautawa dan sun San hali , tuni xufa ta game masu jiki sai q'wallan wahala suke matsewa .

 kujera ya jawo ya zauna,

 ya d'ora q'afa d'aya kan d'aya yana Lila belt din hannun sa,

Kunnen sa daya maqale da  bluetooth yana amsa waya ,

 akram da Salem ne suka qaraso wajen suka jawo kujeru suka zauna , 

xare Bluetooth d'in akram yayi  yace 

"saif halan laifi sukai ma ,?"

Tsoki saif yaja ,

yaq'i tankawa kuma, sai ma murza belt d'in hannun sa da  yake yi yana hura iskan bakinsa.

Saleem  yace 

"ay da gani ma akram laifi sukayi masa , 

Kuka suka fashe dashi basma tace

 "  plsss yaya saif, 

dan Allah su yaya akram kubawa yaya saif haquri ,

 wlh bamu san yana nan ba shiyasa mukaita hayaniyar!".

maganar kakus sukaji ta bayansu yace 

"saifullahee qyalesu haka nan ,

 ai sa kiyaye gaba kuma ,

dan haka yanzun ay musu afuwan ".

cikin takaici saif ya watsa musu harara yace 

" kunci darajar kakus dasai kun d'an d'ana kudarku yau Allah ,

yanda kuka batan rai d'in nan ,

Ku tashi nace 'yan iska kawai ko nazo nan nayi ball daku kunzo kun tsareni da idanuwa kamar mayu ,😡".

da gudu suka kwasa  sukayi waje , 

dariya su Saleem suka kwashe da ita suka tafa ,

kakus kuwa murmushi yayi ya wuce ciki abinsa .

Sam saif q'in yin  dariyar yayi,

 ya q'ara tamqe girar sama data qasa yace 

"Ku kuma daga gidan mahaukata kuka fito koko?" , akram yace

 " hhhh ,

wlh saif nasan cinka qwallon  da deejart tayi jiya a wajen wasa shiyasa ka sauke wasu jawaher wannan kwandon masifar ka yau mlm",

Saleem yace 

"Is a correct my brother wlh, hakan take akram 👍🏻".

Sai da saif ya maida belt d'in sa Sannan ya d'ago ya dube su, ya d'ora hannun sa a saitin xuciyar sa yace 

"wlh akram a nan naji zafin lokacin da shegiyar yarinyar nan taban zero a wasan nan,

Naso ace harda ita sukai mun laifin nan wlh dasai tagane kuranta".

Saleem yace 

"never wlh saif, deejart miskilar babyn nan har taya zatai maka laifi bare kasamu damar hukunta ta ?"

Nooo  wlh sai dai kaci zalinta kamar yanda ka saba".

tsoki saif yaja  yace 

"Alright Nothing  zamu had'u ne a next play, 

Nina fad'a muku sai nayi wng d'inta soon,,,". 

(Al'adar matasan gidan ne buga ball duk weekend ).

da gudu suka shige library suka zube a gaban deejart  suna mayar da numfashi, zaro beautiful eyes nata tayi tace

 " miyafaru  ne ku kuma?

Wlh kun tsoratani sisters".

Basma tayi qarfin hali ta jawo numfashin wahala ta Fara magana cikin shessheqa 

"Wlh deejart yaya saif ba qaramin azzalumi neba mugu wlh , 

Allah ya taimakeki baki wajen da wlh sai kin sha azabar da muka yanzu ,,,! nan basma ta kwashe komi ta fad'a wa deejart ,..

deejart dariya take qyalqyata musu cikin sanyin ta,

 tana fad'in

 "Kai wlh I am pleasure such ".

caaaahh suka yo mata  da masifa,

 da sauri ta to she bakin ta da kunnen ta.

harara jawaher ta watsa Mata ta Fara masifa tana cije lips

da dafe q'ugu na azaba tace

 " ke deejart KO?"

Yanzu fa  sbd tare miki fad'a ne shiyasa discepline master can😏  ya horamu , 

amman shine zakina mana dariya KO ?"!

fari deejart tayi tare da wurga musu harara tace

 "sbd ni nace kuyi argument har yazo yai punishment naku bare kuzo Ku sauke fushinku a kaina kenan ?"

 Cikin sanyi  take furta  maganar ta,

Haka halittarta take,

Cikin sanyin murya take yin kowane motion Nata, 

" bala'i inji miemie, kuna jintafa sisters abinda take fad'a ?"

Wlh kutaso murage zafi wajen ta ".

aikuwa zumbur suka miqe sukayi kanta , 

da sauri deejart ta jefar da book din hannun ta tayi bakin qofa da d'an gudunta tanayi tana waiwayen su. 

da gudu suma suka rufo mata baya suna rige 2n iskota.

Wata tirjiya sukayi ganin yaya saif ya dunfaro library d'in,

haba wa da gudu suka juya suka fice ta  qofar baya suka koma shashin kakus ,

suna sheq'awa deejart dariya dan sun san ta shiga hannun discipline master itama yanzun,

inda tuni ya buge musu wroning kan guje guje amman basu daina ba.

Garin waiwayen su da takeyi sam bata Lura ma da tafowar saif ba,

 garamm ta jita a q'irjinsa ta fad'a tayi male-male,

 a zabure ta dube sa,

 carab suka had'a idanuwa tare a lokaci d'aya , 

wani irin fad'uwar gaba taji a lakacin,

ganin yanayin fiskarsa da tayi ba sasssuci,

tana q'oqarin raba jikinta da nasa ne,

da sauri taji ya in gizata baya tare da kifeta da lafiyayyen mari a kumatu 1,

ya fixgota ya had'e ta da hango yasa yatsunsa ya matse Mata lips saka makon wata uwar q'ara da tazo tayi ba shiri sbd zafin Marin daya ratsa Mata kwanya a bazace.


q'ara matseta  yayi cikin mugun ta , idanunsa sunabin baby  face round  Nata da kallo,

wani dogon tsoki yaja tare da jawo ta fili yace "honored to meet you,

 (naji dadin ganinki),

 dan haka zo muje ki karbi naki kason".

tuni ya jawo hannun ta yayi bangaren sa da ita ,

zuciyar ta kuwa sai tsinkewa take yi ...!

Nan bakin shiga falonsa ya tsayar da ita cikin tsananin zafin rana yace ta tsaya nan yana zuwa ,

ciki yayi shigewarsa ya q'ara esin d'akin ya kwanta a qatuwar  3 seater dake mamaye a falon nasa , ya fiddo phone d'insa ya shiga using da ita hankalin sa kwance alhalin kuma yana sane da ita , 

a can waje kuwa deejart tuni rana ta fara cizon jikinta , duba da yanayin rigarta mai ledace sam bata raina daukar abu mara zafi koya yake,

tun  tana jin tsoron ta zuq'unna ya fito ya ganta har takaita ta ga kasa jurewa_, qafafunta suka zame ta q'asa,

 tuni masassara ta soma shigar duk wani na lungu dake jikinta ,

"Wayyo Allah na "!

ta furta lokacin da taji wata tsananin zafin rana a q'asan tayis d'in wajen , 

a zabure ta miqe tsaye tana Sosa hips d'inta , 

Ta soma magana a hankali

 " wlh yaya saif saina fadawa kakus,

ai bakai kad'ai keda power a gunsa ba Ina tunanin ma na fika , mugun mutum ba abinda ya aje sai zafin mugun ta kawai "😚

tana cikin guna gunin tane  taji motsin fitowarsa ,

da sauri ta miqe tsaye tana rarraba idanu , gani tayi ya watso mata singlet da hankicef ya iso gabanta ya tsareta da mayatattun kaifafan idanunsa masu kashe mata gwiwoyi ba tare da tasan dalilin hakan ba a gareta , 

Jitayi yace

 "  ki wanke mun wad'ann nan now,.

Ya nuna Mata tankin ruwa yace kije ki wankesu a can ki kuma tsaya a wajen  su bushe , 

In sun bushe ki shigo ciki na ida fad'a miki shauran aikin, ya matso gab da ita sosai yasa hannu ya d'ago baby face d'inta yace "saura kimin wankin q'azanta a kaya kiga yanda Zan miki q'asa q'asa Allah kuwa yarinyar nan  , 

ya saketa 

   cikin tafiyar taq'ama yayi shigewarsa falo,

 da kallon harara ta bisa dole ta xuq'unna  ta kwashe kayan singlet ne farare tas guda 5 sai hankicif 3 , 

ba alamun anma sanya su bare a Kai ga batun wanki kuma, 

"Wahalalle "

 ta furta a hankali tana yamutsa face d'inta tare da turo d'an bakinta . 

Clean ta zuba a farin roba ta zauna ta fara wankewa tuni qamshin turarensa na kayan  ya cika wajen ,

 d'an siririn tsoki  taja can q'asan maqoshi ta furta "mayen qamshi kawai dashi ",

a haka _tana yin wankin  tana duba a gogon hannunta dan karda memmen ta  taga tajima bata koma cikin gida ba, tasan fad'a zata sha ne ,

a haka tana zufa tana gumi har tasamu ta ida wankin ta shanyasu a white ware tall ,

duk ta jiqe rigar jikinta ,.

A matsayinta na doctor kuma tasan illar matsalar sanyi a jikin 'ya  mace, dan haka tayi tunanin cireta tasha iska sannan kayan nasa sun bushe saita mayar da rigar jikinta tym din tasan itama natan ta bushe,

  inda ana sun hot sosai a wether d'in, 

bayan ta sanya rigar jikinta ya rage daga ita sai best da wando iya q'aurinta

( lagis)

ta d'auraye q'afafunta da hannayen ta ta koma cikin inwa wajen wasu furanni inda grass carpet ke malale a wajen tayi kwanciyar ta tana hutawa a ranta take fad'in dole Tasha body rst inta koma gida kuwa ,

 Lumshe idanuwanta tayi iskar wajen na ratsata  batasan sanda  barcin gajiya ya dauketaba , .

a can falon saif ya dubi agogo yaga har  5 saura bata shigo ba, yasan zuwa yanzu kuma kayan ya isa su bushe , tsoki yaja ya jefar da wayar a kujerar ya miqe ya fice a zafafe , 

hangowa yayi bata wajen daya barta saidai kayan shanyar sa data shanya a wajen, kama qugu yayi yace" lallai ma yarinyar nan kar dai guduwa tayi?"

Wlh kuwa zata gane kuranta kuwa....

Mgnr sa ta yanke lokacin da idanunsa suka sauka a inda take kwance , 

taku ya fara yi har ya   isa wajen ta yaja ya tsaya a kanta , 

abin mamaki tunda idanunsa suka dira a shatin best d'inta inda ramun cibiyarta ya bayyana  yaji jikinsa yayi sanyi duk wata masifa daya q'unso da nufin ya rufeta da ita gaba daya basirar hakan ta q'wace masa ,

zuq'unnawa yayi ya tsurawa kyakkyawar fuskarta idanu ya kasa daukewa, zuciyar sa na double beat, 

shi kansa baisan miyasa ba in dai ya kalli  face d'in yarinyar yake jin wani some many feelings a tattare da shi yana tasowa can ta qasan xuciyarsa ,?"

Da ace ma yasan miye so? to dasai yace shi yake mata yarinyar, 

to Sam Sam yamaq'i yarda a tsarin sa wai akwai ranar da xuciyarsa zata so wata bare har bakinsa ya furta Mata  hakan , 

kawai dai mamakinsa  a kullum miyasa xuciyarsa ke masa kaikawo in ya ganta ne wai ma ?"

kullum cikin q'aqarin boye hakan yake a gabanta da gabansa akram in suna tare,

bayya son su hankalta da wata alama a akansa bare su bada questions mark(?)

Kuma shi da kunya ma koda ace son tan yake ya furta Mata hakan to tayaya zama ta kallesa ?"

qilanma ta rainasa daga  ranar ,

tabe bakinsa yayi ya d'aga kafad'u yace "barema bance ina so ba kuma🤷🏻♂",

ai da har su akram sai sunmin dariya ba  ma matanba kawai , duba ga yanda yake musu jar fuska ko yaushe.

Sauke ajiyar zuciya ya d'anyi mai nauyi,

'Yan siraran lips  dinta ya bi da kallo yana kwad'ayin jin kalar taushin su tuni batun yauba , amman yasan hakan Sam bamai yuwuwa neba.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post