[Book] ImranFad Complete Hausa Novel by Maman Noorul Hudah

ImranFad

Title: ImranFad

Author: Maman Noorul Hudah

Category: Love Story

Doc Size: 289KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2020

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya Maman Noorul Hudah suna "ImranFad" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: Wata yariya na gani da baza ta wuce shekara goma sha takwas ba a filin kwallo sanye da jersey da wadon shi,ita kadai ce mace cikin su.

Buga kwalo take cikin maza kamar namiji sai cewa" suke FAD bani nan"itako sai juya su take cikin kwarewa dan in ta rike kwallo sai anyi da gaske ake ansa.

Mummy ne zaune  a falo tana hutawa daddy ya shigo da sallama mummy tace"sannu da dawowa"

Yace"yauwa"zama yayi,ita kuma mummy ta tashi dan d'auko me ruwa a fridge.

Bayan ta bashi ruwa yasha yace" wai ina FADILA ne?"

Tace"hmmm ai yariyar nan bata jin magana dubi duk irin duka da kayi mata jiya amma yau ma sanda ta koma filin kwallon yariya kamar mai aljanu"

Yace"ai laifin ki ne da kika bari ta fita a gidan"

Mummy tace"haba mana kai ma kasan yariyar nan ba jin magana take yi ba daga inje inyi sallah ta gudu yanzu ma rabonta da zuwa islammiya yayi kwana biyu"

Yace"ai zata dawo ta same ni "

Fadila ko sai kwallonta take bugawa hankali kwance suna cikin hakane sai ga hadari kowa ya fara gudu amma banda ita,NAZIR yace"FAD zo mu tafi gida ko baki ganin hadari ne?"

Tace"ai.wasan yafi dadi cikin ruwa"

Yace"toh ni dai na tafi"da gudu Nazir ya bar filin da abokan wasa su.

Bayan tafiyar su da minti 15 aka fara ruwan sama mai karfin gaske sai dai ba iska,dama fadila akwai son ruwan sama wasa tai tayi cikin ruwa sanda kayan ta ya jike har dogon gashinta sai tsalle take tana wasa da ruwa.

Wani haddadiyar motar ne yayi parking gabanta cikin masifa ta je window motar ta kwankwasa.

Tace"malam wani irin wulakanci ne wanan?"

Shiru aka yi ba a yi magana ba kuma ba bude ba gashi bata ganin ciki domin bakin glass ne amma wanda ke ciki na iya ganin ta.

Gajiya tayi da tsayuwa ta bar wurin cike da haushi.

Shiko dariya yayi yace"IMRANFAD"

Sauri takeyi  cikin tashin hankali dan sai yanzu ta San dare yayi ga wuri yayi duhu tace"nashiga uku da daddy yau sai ya yanka ni da raina gaskiya bazan je gida ba gidan su umma zani gobe ta biyo ni muje wurin ta roki daddy"

Gidansu ummi take tayi sallama a gate,mai gadi yace"waye?"

Tace"ban sani ba"yana jin haka ya fito da sauri ya bude kofa,yi tayi kamar  bangaje shi da sauri ya masa gefe tana shigewa yace"wanan yariya akwai raini yanzu sai ta zazzage mun rashin mutunci"

Tana shiga ta samu ummi zaune karasawa tayi

Tace"ummi ina yini?"

Ummi tace"lafiya lau dota"

Fati tace"wani laifi kika yi kuma?"hararrar Fatima tayi ta kalli ummi.

Also Download: Akan So Complete by Lubn Sufyan

Tace"ummina"

Ummi tace"na'am dota"

Tace"so nike kira mummy ki ce ina gidan ki tun d'azu"

Ummi tace"dota so kike inyi karya kenan ko?wai meyasa baki jin magana ne,gaskiya in baki canja ba zamu b'ata"

Tace"yi hakuri ummi"

Bayan ummi ta gama magana da mummy a waya ta kalli fadila.

Tace"je ciki ki canza kayar ki kar sanyi ya kama ki inki gama kije shiyar IMRANA Ku gaisa yau ya shigo gari

Tace"toh ummi"

Tashi tayi ta haye sama d'akin da ta saba sauka ta shiga duhu ne a d'akin kunna wuta tayi amma ba wuta,tsaki tayi 

Tace"ga duhu a d'akin nan ya zanyi yanzun nan?ga shi na bar wayana wajen NAZIR bari dai in lallaba in samo ashana

Lalube ta fara yi amma babu alaman ashana tace"bari dai in lallaba in Shiga bayi inyi wanka dama ai ni jaruma ce"

Bata lura da mutum a kwance a gado ba tayi shigewarta bayi

Tana shiga ta bude window bayi ta fara wanka bayan ta gama wanka ta fito d'aure da guntun towel ta zauna bakin gado 

Tace"wanan IMRANA akwai iskanci wato dan bakin ciki generator ma wai sai 8:pm za a kunna dan shegen makon siya da kayi magana a ce yaya IMRANA yace kaza yace kaza ai ya gode bamu taba haduwa ba da sai na koya me hankali,ai nasan bai taba haduwa ba da jarumar mace ba irina shiyasa yake iskanci,ummi wai naje in gaishe shi ashe zai bushe dan ba inda zani shi ya zo ya gaisheni mana inda dadi"tsaki tayi tace"bari inje in kulle kofa da an kunna gen sai nasa kaya nayi sallah

Tashi tayi ta je ta kulle kofa ta dawo ta haye gado,jin ta jikin mutum yasa ta yin......... 

Jin ta jikin mutum yasa ta yi ihu,tuni jikin ta ya fara rawa tace"waye?"

Shiko jinta jikin shi san da ya lumshe ido ya kuma bude su yana sane tun shigowar ta ya dai yi shiru ne

Tace"waye kai?"kallon fuskar shi tayi amma bata ganin komai sai inda blue eyes din shi ke sheki 

Tace"inalillahi wa ina ilaihi rajiun aljani ne yau nayi gamo"

Shiko Kara rungumeta yayi jin na shanun ta a kirjin shi yasa shi cikin kasala ya ma rasa abin yi"

Tace"dun Allah aljan ka taimake ni kar ka kashe ni sai na zama shaharariyar footballer please"

Dariya yayi cikin ranshi ya canja murya yace"ke yariya na zo ne in tafi da ke duniyar aljanai in aure ki,ki haifa mun yar......"maganan ya makale ne sakamakon sauka fisari da yaji a jikin shi"

Tace"yi hakuri aljani ka rufa min asiri dan allah ba dan ni ba"

Ya kuma yin muryar tsoro yace"ai ke kika ce ke jaruma ce ni kuma ina son jarumai"

Tace"ai ni da kake gani aljani shegen tsoro ne dani,ni da nike sauna ina naga jarumtaka"

Yace"toh yanzu kin yi mun laifi fisari a jiki kuma sai na hukunta ki"

Ihu ta fara yi tana cewa" ummi ki taimaka min dan allah"

Ji tayi yace"hahahahahahaha ko kinyi ihu ba mai jinki"abinda fadila bata sani ba shine kofar gidan duk sound proof ne 

Tuni ta rude da sauri ta bar jikin shi ta koma gefen gado ta rakube wuri d'aya

Ganin ta tsorata yace"na yafe miki na yau ki rufe idon ki inki ka kuskura kika bude toh tare zamu tafi"

Da sauri ta rufe ido gam yana ganin alamun ta rufe ido  ya fita a d'akin yana dariya yace"hmmm IMRANFAD akwai tsoro ashe "

Yana fita da minti biyar aka kunna gen.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post