[Book] Ina Zan Ganshi Complete Hausa Novel by Xarah Bukar

Ina Zan Ganshi

Title: Ina Zan Ganshi

Author: Xarah Bukar

Category: Love Story

Doc Size: 436KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2017

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya  Xarah Bukar suna "Ina Zan Ganshi" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: Banko k'ofar d'akin da k'arfin gaske ya firgita Hajjo dake k'ok'arin had'e tabarmin dake yashe gefe guda. Fuska murtuk'e ta sak'alo k'afa ciki d'akin tana gunguni. Cike da k'unin rai Mahaifiyarsu Hajjo ta zuba mata idanu.

"Batula baki iya Sallama ba?"

Haushi ne ya kuma turnuk'e ta da sunan Batula da Hajjo ta ambata, tafison akirata da Fatima Zarah ainihin sunanta.

"gaskia Hajjo ana shiga hakkina a matsiyacin gidan nan, saurayina yazo daga fita ta Baba ya izo k'eyata, da alamun kuma da d'an maik'on sa, oh ni Fati naga samu naga rashi" karashe maganar tayi cike da tashin hankali, hannuwan ta biyu bisa kanta.

    Tak'aici ne ya cika Hajjo, wana irin k'aramar kwak'walwa yarinyan nan keda shi, "Batula miyasa baki da hankali, talauci ba hauka bane, ki kuma iyawa bakin ki, matsiyacin gidan nan gidan uwarki da ubanki ne ba yadda kika iya"

    Shuru Batula  tayi zuciyar ta na tafasa, banda harara talautaccen dakin da take.

"Maza jeki rumfar babanku ki amso kayan miya kafin ya kasa na kasuwa" acewar Hajjo batare data kula da yanayin ta ba.

Ware idonu tayi, tayi tace "nikam bazani niba, ajira dawo wan su Hassan saisu karb'o"

"Dole kije dan bazan tsaya jira harsai sun dawo makaranta zan aza abinci ba, wuce ki karbo kafin na mazge ki" Hajjo ta fadi da niyyan kai mata dundu

Gunguni tahau yi bata da alamun tafiya saida Hajjo ta hada mata tsawa mai dauke da ashariya sannan ta fice ak'ufule bayan ta tsuri mayafin ta dake lank'aye bisa taga.

    Gaban karamin gidan nasu dako fenti babu ta iske wani yaro tsaye.

"Baba mai kayan miya na nan ? Yaro ya tambaye ta.

Idan akuya na magana to ta tanka bangajesa tayi ta wuce abunta cike da haushin yadda Baba ke zubar mata da aji, wai itace diyar mai kayan miya, dogon tsaki taja ta k'arasa can gaba da gidansu inda runfam Baba yake, bata kai ka zuwa rumfam ba ta mak'ale daga gefe inda baba bazai hango taba, amma tuni ya ganta ya dauke kai, Lawali ta kira yaron auguwan su ta aikesa amso kayan miyan.

   Sabo da halinta yasa Baba bai nuna yaganta ba, jinjina kai kadai yayi, albasa batayo halin ruwa ba. leda taf ya cikawa Lawali sannan ya damk'a mai.

    Hankalin ta gabadaya ya shagala da kallon wasu yara da Mamansu cikin wata arniyar jeep, sai kallonsu take ji take dama itace acikin motar da tafi ko wace ya mace morewa, sai dai kuma aka samu akasin Baba talakana ne saidai su k'are da tumatur da albasa.

"Butula gashi" taji yaro na fadi, harara takai ma sannan ta warce ledar tayi gaba, Hajjo na iza wuta a gindin murhu ta shigo ta dire ledar tayi cikin kusurwar daki.

     Girgiza kai Hajjo tayi, tunanin barkatai ke yawan mata a kwakwalwa, inda ba a gidan ta haifi Batula ba tana iya cewa an mata musanye, amma ba daman fadin haka kamarsu daya da Baba kamar an tsaga kara.

 ***

K'asak'asa suke zantawa da alamun wata muhimmaciyar magana sukeyi, nisawa Hajiya Fatima tayi tace "Safara ya kikeso nayi kinsan Rasheed wani irin murd'add'en mutum ne da baa iya tank'wara shi, tun rasuwar ubansa ya koma hawainiyar da babu kala"

Murmushin dabai kai zuci ba Hajiya safara ta mata sannan tace "yaron nan dai d'an kine ke kika haifeshi bashi ya haifeki ba sai kisan yadda zakiyi ya amincin da kudirin mu.."

Turo kofar tafkeken palon ne ya katse masu zance, sanye yake cikin black suit, haunna sa rike da karamin brief case, ciki ciki yayi sallama, basu amsa ba banda kallo da suke bisa da shi, maihaifiyar sa hajiya Fatima ce tayi karfin halin cewa my boy ka dawo.

"e" kawai ya amsa mata agajarce ya wuce hanyar dakinsa cike da haushin Hajiya Safara dake hakince kan babban kujerar palon, idan bai manta ba tun yana yaro yake ganinta saidai jininsu bai taba haduwa ba, ya rasa mai suke yawan zantawa tare da momyn sa akullm idan suka hadu, tsaki kawai yaja ya cusa kai ciki had'add'an dakinsa.

    Fitowa tayi daga kitchen, hannuta ruke da kwalin exotic ta karasa cikin palon cike da yauki da iyayi. "Mardiyyah mutumin ki fa ya dawo"

Acewar hajiya Safara,

"Dagaske " Mardiyya ta fadi tare da kwalalo ido tana kallon Momy dake mata murmushi, sai kuma ta kalli ogogon hannuta tun 4 tabaro office amma shi sai yanxu 8 ya dawo.

Tashi tayi da azama, zata bar palon, hajiya safara tace "kardai ki dade, dare yayi kar Abban ki yajimu shuru"

"Toh Umma" ta fadi  tayi rushing zuwa kitchen ta sanya ruwa a glass cup sannan ta nufi kofar dakinsa gabanta na dukan uku, tasan sarai xai iya korota shiyasa tayi dabarar kaimai ruwa, ahankali ta tura kofar dakin ta shiga.

    Tsaye yake yana kokari cire neck tie bayan ya ajiye coat din gefe, ganinta da yayi ya dakatar dashi yanai mata kallon kina bukatar wani abune, kaman tasan abunda yake aynawa, girgiza kai tayi tace "Mr Rasheed sai yanxu ka kawo, ga ruwa kasha" ta fadi at once hade da mikamai glass cup, bai karba ba balle ya tanka, closet ya nufa yadau towel yabar ta tsaye ya shiga bandaki, ya rasa wace irin mayyace Mardiyya, at work bai tsira ba sai taxo har office yimai shishigi ya dawo gida kuma ta biyosa, wace irin rayuwace wanan, most annoying part of her shine yadda take kura mai manyan idanuwan ta da mak'e muryarta tamkar wata sabuwar farar kura.

   Rashin tankata da yayi ko a kwalar rigarta, inda sabo ta saba, sukanyi shafe awa hudu biyar ko tari bai yiba, duk wannan ba matsalarta bane koda ace ma wuka zai dauka yana datse naman jikinta bata damu ba, tana sonshi kuma ganin  kyakyawan fuskar sa ya ishe ta farin cikin shekaru ashiri. Murmushi tayi ta kwank'wade ruwan tas sanna ta fito palo, hajiya safara na ganin empty glass cup din taji farin ciki ya ziyarceta, komai yafara kankama tsakanin yarta da Rasheed kenan tunda har ya iya amsan abu gareta. Duk aganinta shiya sha ruwan.

    Sallama sukayi da Momy, ta rakasu har bakin motar su sannan ta dawo cikin gida ta wuce dakinsa.

   Gefe gado yake zaune yana brushing lausassiyar kashin kansa bayan ya fito daga wanka, zama tayi kusa garesa heda da amsan brushern tahau tazarmai lufluf tana fadin,

 "my boy ya aikin ?

"fyn" ya amsa mata, fuska ba yabo ba fallasa.

"My boy ka girma, ga kudi ka tara ta ko ina, yanxu miya rage ?"

Anxo gurin, daure fuska Rasheed yayi tamau, tacigaba

" sa'anninka masu shekaru talatin da uku duk sunyi settling banda kai, ya kamata kayi aure"

Murya can kasa yace.

"am not ready, infact ban samu wace nakeso ba har yanxu" 

"wannan ba excuse bane, kana da alot of yammata masu sonka, ga Mardiyya yarinyar kirki masu hannu da shuni, itace daidai dakai, naira na gugan naira"

Kai ya girgiza "bana son Mardiyya infact banason ya'ya masu kudin nan yawanshi basu da isheshen tarbiya, it better nasamo wata can cikin talakawan nan"

B'ata rai Momy tayi, inda akwai alumma data tsana bai wuce talaka ba, mikewa tayi tsaye tanai mai wani mugun kallo, cike da karaji tace "talauci badai a xuri'ata ba, na gwamma ce mutuwa ta akan naga ka auri dangin tsiya, ban haifi dana dan talaka suci arzikin saba, tunda ubana ya haifeni bansan miye talauci ba kayi na farko kayi na karshe koda wasa karka kuskura ka ambata kalmar talauci a gidan nan, Mardiyya kuma saika aureta" karashe maganar tayi cikin huci sanan tai wurgi da brushen ta fuce dakin afusace.

Murmushi mai sauti yayi,

ya lura dai dabiar Momy bazata gyarabu, hatred dinta towards talakawa bazai canxu ba, ya rasa miye tsakanin dinta da takala, same story dinta kenan tun yana karami shiyasa yake da burin aurar talaka dan ganin miye illarsu da Momy ke masu kara tsana. Wayarsa dake kusa dashi ya dauka yayi dailing numbern Daddy Malam, bugu daya ya dauka suka gaisa. Yace "Mr  Rasheed kwana biyu, fatan kana cikin k'oshin lapia

"Am good, Aikuwa suka min yawa a office, kayi ready din komai gobe xan zo na cigaba a inda na tsaya"

"Toh sir, Allah ya kaimu"?

"Amin ya amsa mai sanan ya katse call din ya shingid'e bisa gado hade da lumshe idanu.

     Safa da marwa Momy keyi adakinta, wana irin abun kunya my boy yake son jaza mata, ga Hajiya Safara duk ta daura mata zafi, wani zubin ma k'awarka ma tasan sirinka wani tashin hankali ne, dole ne ta tursasa Rasheed auran nan ko yanaso ko baya so.

Tafiyar kusan minti goma  tayi kan babban titin Kawo dake cikin garin Kaduna. Hankalinta gabad'aya na bisa titin da babu alamun abun hawa na haya banda mayan motaci dake walk'yawa. Ajiyar zuciyar mai dauke da wahala ta sauk'e, rashin abu hawa a unguwar tasu ba k'aramin ci mata ruwa a k'warya yake ba, ina ma ace tana da motar kanta saidai kawai yan polytechnic su ganta da ride dinta koda ma ace comot make i enter (One door).

    Jakarta irin wace ake sak'alewa a hammata ta bude ta ciro dubu biyu da Baba ya bata na siyan handout, kallon su tayi tana jinjina rashin k'yaun da dattin kud'in dayasha satalif, mai shesu tayi cikin jakar akayi rashin sa'a iska yayi sama dayan canjunan.

    Da azama ta mike tahau tsintarsu, saidai kash, ashirin uku sun haura saman titi, tsabar rud'u bata ankara da SUV dake dannowa aguje ba tahau bin ashirin dinta dake tsilla tsilla a titin.

    Kiiii!!!! Kakeji, yaja mugun burki da ita kanta saida ta razana, jiki na rawa take kalan motar da tunda uwarta ta haihefa bata taba gamo da irin taba, ko inuwar mutum bata hange ciki kansancewar tinted glass dinta, kallan motar kawai take tana imaging kanta aciki. Kallo daya yakai mata ya dauke kai yaja motarsa yabi gefenta ya wuce, RMD data gani cikin plate number yasata wage idanu, tanajin labarin family din a fulanin talla, yau gashi tayi gamo da motar, inama ace taga mai tuka motar yau da tayi kwanan farin cikin haduwa da mai kudi, duban kayan jikinta tayi ta buga tsaki, ta tabbata ya fola mata, ba mamaki kodaddiyar arabian gown dun jikinta ya kwafsa mata, last week kadai ta siyeta a gwanjan kasuwar bacci ganin sabuwar ita yan makaranta ke yayi.

Cike da tausayin kanta ta ida tsince kudin sannan ta nufi k'aramar kasuwar dake gurin, tafi awa daya tana zagaye kasuwar kanan tasamu jakar swagger da ake yayi, cikin dubo biyun ta fidda duba daya ta siyeta, acewarta ta gaji da rike mak'ale mata. 

    Bayan ta ida dakyar  tasamu achaba ya karasa da ita inda yan Marwa (keke Napep) ke tsayawa, aranta sai mita take tayi latti zuwa makaranta (sai kace wani ya aiketa kasuwan).

   "Ke tafiya ne" Ogan gurin ke tambayar te, amsa mai tayi da eh, yahau k'walla kiran Mamuda dake zaune can gafe yana gabtar rake.

"Kaida kake layi maiya kaika da zama can" acewar ogan cikin muryar sa nayan tasha.

"gani zuwa" Mamuda ya fadi hade da mik'ewa kyakyabe jikin sa, wata tsohowar yadi mai araha ke sanye jikinsa da wata jar hula bisa kansa, jikinsa dukun dukun da bakin mai tamkar wani mechanic, fari ne dago dasai mai ido ne zai gane akwai farin, kacakaca da yake yasa na kasa tantance kamannisa.

   Tamkar wani shashasha haka yake magana, cikin maganar sa ta e'ena yace "shi shi gaaa muje"

Tsulum Batula ta fad'a cikin marwan, ta k'agara tabar gurin.

Suna tafe tahau gyaran rolling din veil dinta dake nema warwaro, bayan ta gama kudin da suka zube tahau dirgawa dari uku da saba'in tagani, babu naira ashiri cikin, Allah ya isa taja, tana maganganu kasa kasa, yasata asara ya tafi yabarta.

    Duk abunda take yana kallonta ta circle side mirror,  daure fuska yayi tamau had'e da dauke kai ganin ta dauko jar hoda tana shafawa, suna hawa booms hodar ta subuce hannuta, tas kake ji dankarariyar jar hoda ta fashe mai hade da madubi, baima lura ba, lailayo ashar da tayi yasa shi tsayar da Marwan.

"Kan uban can, dan Marwa kamin babban asara"

Kallonta yayi sannan ya kalli inda idon ta yake, yace "ayi hakuri abisa rashin sani ne, banda ke wake shafe shafe a titi"

Harara ta kaima, "dayake titin na ubanka ne, ai dole kace haka, ina ruwanka kaine ke siyamin kayan shafan komi"

"Allah ya wuce zuciyar ki, cikin kudin da zaki biya ki cire murtala uku da goma ki siya sabuwa"

Wani k'askantaciyar kallo ta aika mai, "bura ubar murtala uku da goma, nayi maka kama da talaka mai shafa hodar hamsi, banxa matsiyaci, talaka kun dauka kowa irin kune" tsaki ta buga tana cigaba da banka mai harara.

Kallonta kawai yake yana maimaita abunda tace, shidai baiga banbanci sa da ita ba da take kirasa talaka harda zagin dan tsohonsa dabai san hawa ba balle sauka.

Shareta yayi ya kunna Marwan yaja, tsine tsine tahau yi bai tanka ba.

"Kad poly xaka ajiye ni" yaji ta fadi cike da karaji.

Suna isa ta sauka ta fiddo tsofin goma da ashiri, naira saba'in tabasa, bata jira cewar saba tayi gaba abunta.

Mamaki da tsoron Allah ne ya turnuk'esa, yahau juya saba'in din, akalla daga Kawo zuwa gurin daya ijiyeta Jaka biyar ce, danta raina masa wayo ta basa saba'in tsabar tsiya, mai take nufi kenan, kudin hodar ta cira komi. Kai ya girgiza ya karasa gaba inda yaga passenger.

    B'angaran Batul kuwa dama saba'in tayi niyya basa koda ace hoda bata fashe ba, tana isa hall har angana 8 to 10 lec, ta tsaya jira na 12 to 2. Jikin motar Minal yar ajin su ta jingine jikinta, duk wanda yaxo wucewa saiya tsamma nin motar tace, daga gefen motan taji murya Minal da kawarta Billy suna hira da dariya sam batasan sun kunno kai ba da alamu suma basu lura da ita ba, hirar wata magazine dake rike hannun Minal sukeyi.

"Amma fah RMD dinnan ya burgeni, duba fa kiga CEO ne a Mobile oil Nigeria(MON), one of the major petroleum product marketing companies amma ji yadda yake keeping low profile, ko picx dinsa baa gani, koda yake ance ma hardly 20 letter word ke fita daga bakin sa" acewar Billy

Murmushi Minal ta saki wanda babu tantama ta fola mai dukda sunansa kadai yaya appearing a magazin din, "Ina zan Ganshi, na jima ina neman sa, ni wlh ganinsa kadai ya wadatar ni."

Dan duka billy takai mata tana dariya, "ance komai nasa customised yake da sunansa, kila idan da rabo zakiga motocin sa ko wani abu nasa wataran.

Tsur Batul tayi tana sauraran su, tana tuna motar RMD data gani dazu, dabarace ta fado mata ta saki murmushi, yawaci yaran masu kudi nan basu fiya sanyi kawace da talaka ba saidai iri iri su, balle ma Minal da take daukar kanta diyar shugaba, maganin su kadai zatayi ta hanyar raina masu wayo, tun shigowar ta poly bata samu kawaye ba yawanci yan kuci ku bamu ke manne mata, ita kuwa ta wuce ajin su.

Wayar ta chaina kirar S7 da screen yagama tsagewa ta fiddo ta dasa a kunnuwanta, da ganin wayyar sai ki rantse original dince.

"Hello RMd nayi fushi tun d'azo kace zaka xo"

"Toh ba komai, ka gaishe min dasu mama sai naxo gida gaidata" katse wayan tayi tana kallon su ta gefe ido, sarai sun jita, imani ya hanasu magana banda saki baki da sukayi suna kallon ta. 

Taku daya biyu tayi da niyan barin gurin, sukayi azama tarota, Minal tace "Fatima kin san shine ?

A yatseni ta dubeta, aranta tana fadin shegia ashe tasan suna na, a fili tace "wa kenan ?

"Rmd mana, naji kin kira sunansa ne"

"Ayyo wai cousin dina Rmd, kina neman sane ?

Kafin Minal tayi magana Billy ta janye ta gefe, 

Tana magana kasa kasa, alamun bata gamsu da Batul ba, kayan jikinta ma ya isa ya nuna class din data fito.

Gyara murya Batul tayi tace "nasan bazaku yadda dani ba, amma kusani ni abun duniya bai dameni ba shiyasa nafison zama simple, dan kun ganni haka dat doesnt mean am poor" k'arashe maganar tayi dakai masu harara sannan tayi gaba.

Da azama Minal tayi saurin taro ta tanai bata hakuri, harga Allah ta gamsu da kalamanta tunda shi kanshi Rmd din ance kudi bai dame saba same goes to his cousin kenan. Dakyar jidda ta hakura bayan billy tasa baki, sai wani ja masu aji Batul take wai ita mai cousin, Minal dai sai kokarin chilling dinta up take, a lecture ma kuna da ita suka zauna bayan an gama suka wuce African dish cin abunci, nan ma sai yatseni take ko dogon surutu tak'iyi karsu k'ureta da tambaya, gabanta sai dauks uku uku yake karsu barta da biyan kudin abinci dan plate dinsu akwai tsada gashi ta cire kunya taci tayi nak, sa'ar ta Minal ta biya duka bill din sannan suka firo tafiya gida, ba yadda basuyi da ita su ijiyeta gida ba taki yadda acewar ta  library xata shiga karatu, sai da taga sunja sun tafi da mintuna talatin sannan ta hau Marwa ta wuce gida murna fal zuciyan ta tasamu b'agas, sai dai tunanin ta daya "Ina Zan Ganshi?".

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post