[Book] Indo A Birni Complete by Rasheedat Usman

Indo A Birni

Title: Indo A Birni

Author: Rasheedat Usman

Category: Fiction

Doc Size: 515KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2020

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya  Rashidat Usman suna "Indo A Birni" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: Yara biyu na hango suna cin Uban gudu, yayin da wacce ke gaban take gudun ceton Rai, sosai take gudun Saboda kar wacce ke bin bayan nata ta kamo ta,  wani gida naga yarinyar ta fad'a, binta cikin gidan itama yarinyar dake biye da itan tayi, da Gudu ta fad'a wani madaidaicin d'aki, cikin haki.

   d'akin da yarinyar ta shiga, itama wacce ta biyo tan take k'ok'arin shiga.

   Cikin Sauri wata matashiyar mata ta tare ta tare da cewa.

  " Lafiya *INDO* kuke wannan Uban gudu, sannan kuma zaki bita har d'aki, aiko mutuwa ma tana kunyar Idon Uwar d'a, meye *Zainabun* ta Miki?

 kika biyo ta har gidan ubanta ba ko kunya.

  Huci wacce aka kira da *INDO* take Cikin masifa da bala'i take cewa.

 " Sai mutuwa taji kunyar Idon ki, ni kuma *INDO banji taki ba, wlh yau Babu mai hanani cin Uban Zainabu cikin gidan nan, gobe koda kud'i aka Had'a ki baxaki k'ara nema na da tsokana ba, cemin fah tayi *INDO BALA'I* a gidan uban waye aka yanka min suna da *INDO BALA'I* Kinga *Goggo Hali* ki kauce ki bani hanya, kar nayi gefe dake kiga rashin kunya ta, dan wallahi, na ture ki na shige cikin d'akin nan baxai bani tsoro ba, ehe sai dai duk abunda zai faru ya faru, ta k'arasa maganar tana murgud'a baki.

 Gam sukaji An rufe k'ofar d'akin tare da dannawa k'ofar sakata, daga rufen zainabu tace

 "Baxan fiton ba, kuma na fad'a *INDO BALA'I* ko k'arya nayi ke ba masifaffiyar bace.

Matsawa wacce ta kira da *Goggo Hali* tayi tare da cewa to Kinga ma ta rufe d'akin sai dai idan ni zaki Kama ki daka, tunda ke baki da mutunci, kowa ya miki shaidar tsiya a cikin garin nan.

  Cewa *INDO* tayi

  " Idan anga dama Amin shaidar Abunda yafi Rashin mutunci ma, kuma wlh yau sai kinga yanda ake tsiya a cikin gidan nan, badai y'ar ki ta rufe d'aki ba, d'aga murya *INDO tayi, tace zainabu kina jina ai idan ba tsoro ba ki fito, mana shegiya y'ar matsorata, kuma wallahi Yau saina huce haushi na akan *UWARKI*.

  Juyawa *INDO tayi, karaf kuwa sai idon ta yayi toxali da Randar k'asar Goggo Hali, Wacce take cike fal da Ruwa, Da Gudu tayi madafin Goggo Hali ta d'auko tab'aryar ta, Randar k'asar INDO* ta nufa da Gudu tare da buga tab'aryar akan Randar, fashewa Randar tayi, take kuwa Ruwan ya zube kasa, bokiti na k'arfe dake ajiye gefen Randar k'asar *INDO* ta raruma tare da shek'awa a d'akin mahaifin Zainabu, tsayawa Goggo Hali tayi tana kallon ikon Allah a gun *INDO* domin kuwa Idon ne kawai tsakanin ta da ita, tasan Idan tayi gangancin zuwa ta tare *INDO* to Babu shakka zata iya sauk'e mata tab'aryar a kanta ba damuwar ta bane, domin kuwa tasan Halin INDO tsaf babu wanda ta gyale kaf fad'in kauyen.

 Cikin Huci INDO tace.

 " Kuma na watsa Ruwan a d'akin Malam Hamxa idan ya dawo shima yasan cewa y'ar sa ta tab'o *INDO* yau,

  Bata jira mai Goggo Hali zata ce ba tayi ficewar ta tana rera wak'a.

    " Ikon Allah cewar Goggo Hali, yarinya ta Addabi gari, kowa yake Allah wadarai da Halin ki, Yanxu fah ki duba kiga b'arnan da yarinyar tamin, Amma dai wallahi Albasa batayi Halin Ruwa ba dan dai iyayen ki kam, mutanen kirki ne, Su kuma tasu jarabawar kenan, na Samun fitinanniyar yarinya, to Allah dai ya shirye ta.

  Jin motsin mutum a bayan ta ne yasa Goggo Hali juyawa, zainabu ta gani tsaye tana sauk'e Ajiyar zuciya, ai kuwa nufar ta Goggo Hali tayi, tare da sauk'e mata rankwashi a kanta, tace.

 " Yanxu ke zainabu ki Rasa wa zaki tsokana sai *INDO*, sai kace wacce baki san Halin ta ba, to maxa shiga d'aki ki d'auko min mayafi na, naje wajen Uwar ta wlh sai sun biyani Randa ta, dan baxan yi Asara ba wlh.

  D'akin Zainabu ta nufa tana cewa.

 " Kije ki wlh Goggo a biyaki Randar ki, tunda y'ar su bata da mutunci.

 Ita kuwa INDO fitar ta daga gidan su zainabu, hanyar gidan su ta nufa, tun daga nesa ta hango motar sa, cikin murna da zuwan sa, garin nasu yasa *INDO* kwasa a guje, cikin zumud'i, ta nufi motar, kasancewar Gudu baya bawa *INDO* wahala, kullum a cikin sa, take sam bata da nutsuwa, k'azanta kuma wajen *INDO* subhanallah ba'a magana, domin kuwa k'azama ce ta ajin farko, duk inda ake neman k'azama, to idan aka Samu indo ayi fatiha a tashi, domin kuwa kaf fad'in K'auyen Babu wanda yakai *INDO* k'azanta.

   Wannan kenan.

 A nutse ya fito daga cikin motar, tare da tsayawa jikin motar yana duba yaran da zasu shigar masa da Kaya cikin gidan, tsohuwa mai ran k'arfe *HAJIYA INNAH* da Gudu INDO ta k'araso wajen nasa tare da yin turus da k'afar ta cikin bak'ar kasa mai k'urar dake shinfid'e a wajen, take kuwa k'asar ta bulewa wannan bawan Allah k'afar sa.

  Da sauri ya daga kansa ya dubi *INDO*  cikin takaici kuma cikin tsawa yace.

  " Wacce irin mahaukaciya ce ke, ki duba kiga yanda Kika bule ni da k'asa, wawiya marar Hankali, Zaki kauce min da gani ko sai na makeki, Useless kawai.

  Tura bakin ta INDO tayi, tace

  " Wlh yau Kam baxan bar nan ba sai kace kana Sona, shikenan kullum sai ni kad'ai zanta sonka, kai baxaka soni ba, wlh yau sai kace kana Sona, ko kuma kamin Irin Abunda nake gani y'an India suna yiwa y'an matan su, a tibin *Hajiya Innah*,  Bari ma na tuno sunan Abun.”

Yawwa na tuno kuss, suke cewa, sai kamin sannan zan tafi, turo masa bakinta tayi, tace gashi kamin, kaji mustapha na.

  Zaro Idon sa, mustapha Yayi tare da saurin kawar da kansa gefe, jin bugun warin bakin INDO ya bigi hancin sa, wani Irin hucin wari yaji mai tayar da zuciya, cikin k'yank'yamin ta yake cewa.

 " Allah ya sauwak'a naso k'azama irin ki, k'azamar k'auye, waima tukunna uban waye zai miki kiss, da wad'annan yellown hak'waren naki, b'ace min da gani kafin na targad'a ki, mahaukaciya kawai, marar lissafi, Amma dai wlh Allah ya isa tsakanina dake, ki rasa waye zakice kina so saini, to wlh Allah ya isa kin cuceni.

   Murgud'a masa Baki tayi tace.

  " Niba mahaukaciya bace wlh, kuma sai kamin kuss d'in nan, rarumo rigarsa tayi, ta duk'unk'une a ciki.

 kasancewar babbar riga yasa, sai buga k'afa take, tana ihu tana cewa.

  " *Wayyo Allah na shiga uku wayyo jama'a kuzo ku tayani rok'ar ya mustapha ya min kuss wayyo Allah Jama'a kuxo ni kad'ai nake sonsa shi baya Sona.*

  Rasa Yaya mustapha zaiyi da INDO yayi, gashi kuma yana hango wasu dattawa biyu suna, tahowa, ta inda suke, 

  "Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Allahumma ajirni fil musibati, nidai wannan yarinyar ta zamo min masifa wlh, Duk Randa zanzo k'auyen nan, da tsinkewar zuciya nake Zuwa, tunda nasan zan had'u da Bala'i. 

da k'arfi mustapha yasa Hanun sa cikin kyamar INDO ya b'anb'aro ta da kyar, tare da hankad'a ta, gefe.

 fad'uwa tayi tare da bige kanta jikin bango, wani Irin zafi taji a kanta, Amma duk da haka Bakin *INDO* bai mutu ba, cikin Rashin Kunya, ta taso kamar wacce zata Doki Mustapha, tace.

  " Ka ture Allah ya Isa wlh, mungun Azzalumi, kuma wlh Bashi ka d'auka, sai na Rama wlh.

 Tana gama fad'in haka ta juya ba tare da ta k'ara Kallon mustapha ba.

  Tsuka mustapha yaja, tare da tab'e bakin sa, yace.

  " Wawiya kawai marar Hankali da nutsuwa, ai ko d'aura min ke Akayi a kaina, saina sinke ki da k'arfin tsiya, nayi wurgi dake gefe, *K'AZAMAR K'AUYE* kawai.

   Yara biyu ya hango, Kira ya k'wala musu, bayan sunxo ne, ya umurce su, da su kwashi kayan sukai masa gidan *Hajiya Innah.*

  Tsayawa yayi har suka gama shigar da kayan sannan yasawa motar sa security, yayi gidan, *Hajiya Innah*.

  Sauk'ar Ruwa a jikin sa  mustapha yaji' wani Irin shid'ewa Yayi,  a gigice ya bud'e Idon sa, karaf suka had'a Ido da *INDO* tsaye da bokitin Ruwa a Hanun ta wanda ta juyewa Mustapha a jikin sa, takaici da haushin ta, shine ya hanasa magana, saima wani mungun kallon  daya tsaya yana aika Mata.

  Juyawa INDO tayi a guje tana dariyar k'eta tace.

  " Na Rama tureni da kayi, daman ai na fad'a maka Bashi kaci, kuma na Rama Yanxu Babu bashi tsakanin mu, masoyina mustapha, *INA SONKA ARADU* tana gudun ne take wannan zancen.

  Kad'a kansa mustapha yayi, cikin Jin haushin *INDO* da mamakin ta, yake cewa.

 " Anya kuwa wannan yarinyar bata da Aljanu, don ba k'alau take ba, Kam, wai *masoyina mustapha* ko a gidan uban waye na zama masoyin nata, sai Allah, shigewa Yayi cikin gidan, tare da Sallama.

  Tana Zaune gefe tana b'arar gyad'a ga kuma tarin kayan da mustapha yasa aka shigo masa dashi, a gefen ta, d'aga kanta tayi tare da cewa.

 " Lale maraba' da mutanen Binni, sai Kuma tayi shuru tare da tsurawa jik'ak'k'un kayan jikin sa Ido, cikin mamakin meya jik'a masa Kaya, kasa hakuri *Hajiya Innah* tayi tace.

  " Muhammadu dake haka take kiran sa dashi, menene ya jik'a maka kayan ka, kodai ka biya Rafi ne kayi wanka?

  Tambayar *Hajiya Innah*  ta k'arshe itace ta bawa mustapha Haushi, *wai ko ka biya Rafi ne kayi wanka* sai kace ta tab'a ganin nayi hanyar rafin nasu, cikin gatse ya mayar mata amsa da cewa.

  " *A'a ba Rafi Naje ba, tekun Maliya na biya nayi wankan na dawo*.

 " To Uban y'an bak'ar magana da zafin Zuciya, Idan da Akwai inda yafi tekun Maliya ruwa ma kaje kayi wankan, aikin banxa kawai daga tambaya sai cibi ya zama k'ari.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post