[Book] Jajirtacce Complete Hausa Novel by Yar Mutan Arkilla

Jajirtacce

Title: Jajirtacce

Author: Yar Mutan Arkillah

Category: Fiction

Doc Size: 265KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2017

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya  Yar Mutan Arkillah suna "Jajirtacce" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser:  *Matashiya*

"Wani karamin kauyene mai suna kasa,wasa. Wand yake cikin babban birnin jihar sokoto, can a wani dan karamin gida danagani kofarshi a wangale  shiyasaka nakutsa kaina da sallam tareda fatan samo maku abinda kuke nema." 

Wata matashiyar mace ce na hango kwance akan wata yagaggiyar taburma da kallo daya nagano tana cikin mawuyacin hali na jinya, duk dacewa jikinta yana lullube cikin zannuwa har guda biyu amma sai kyarma take tana kar-karwa kamar maxari habarta na rawa hakoranta na had`uwa da yan'uwansu.

Zagayeda ita wasu kana'nan yara ne guda biyu, mace da namiji, namijin zaikai shekaru gomasha uku zuwa sha hud`u, macen kuwa bazata wuce shekaru takwas ba, kuka suke sosai kamar ransu zaifita, mai d`an wayon shine mai faman yimata sannu had`eda yimata fifita da wani farantin roba mai fad`i,  cikin tsananin dakewa da juriya ta rintse ido ta kira sunan yaron dakyar ta iya har had`a kalmomin sunan shi Am..mar ya amsa dasauri na'am Ummana saida ta nisa dakyar sannan ta koma yinkurin had`a wata maganar Ammar ga qanwarka tafad`a lokacinda tad`auko hannun karamar kanwar tashi ta had`a da nashi. 

Ga Safeena nan Ammar nasani zaka kula da ita kamar ina raye zaka riketa fiyeda kanka, Ammar ka kulada Feenah kariketa kamar yanda kasaba, yarona inaji ajikina nima zan tafi, zanyi nisa daku Ammar, saidai nayi imanin cewa wanda zai d`aukeni shizai tsaya muku, Allah yana tare daku Ammar,yaron data ke kira da Ammar yafashe da kuka a'a Umma dan Allah kibari Umma narokeki karki tafi karki tafi kibarmu Umma na kina kallo Abba yatafi yabarmu, yabarmu ba kowa sai ke, umma inkika tafi ba'ba Larai zata kashemin qanwa kinsani Umma kullum saita hantareta tana cemata yar'tsintuwa shegiya idan naji haushi nayi magana su yaya Lodo sumin duka, agabanki kenan Umma, yaki ke gani ranarda babu idonki? Umma kashemu zasuyi wlh kashemu zasuyi Ummana yakoma fashewa da kuka, wasu za'fafan hawayene suka silalo daga idon Umma ta tattaro duka ragowar karfin da ya rage mata ta rungumo yaran nata, tsananin tausayin su yakamata musamman Feenah wadda har yau batasan inda ahlinta yakeba. 

Tamatse ragowar kwallar dake idon ta cikin yanayin jin jiki tace Ammar yau zan gaya maka gaskiya, gaskiyarda saninta yazama wajibi a gareka a matsayin ka na wanda zan barwa rikon Safeenah! Ammar yakoma kankame uwar yanaji kamar ya ciro ciwon jikinta ya jefar, duk da yanada yaranta amma yaro ne mai kaifin tunani da saurin fahimta, inajinki Umma na amma dan Allah karki mutu dan Allah kitsaya damu kinji Umma ke kad`ai ce.........dasauri ta toshe bakin d`an nata tace a'a Ammar karka soma karka yarda Allah shine gatan kowa da kowa Allah shine mafi kusanci daku fiyeda ni dakuka sani ka saurareni d`ana.....

Abinda yaya Larai take fad`a akan Feenah gaskiya ne tabbas kanwarka yar'tsintuwa ce saidai hakan bai tabbatar da ita shegiya bace, kai kodama hakan din ne meye laifin yarinya?  Ka saurareni da kunnen basira kaji tarihin Safeenah da inda muka sameta bata jira cewarshi ba ta fara bashi labarin kamar haka:

****************************

"Ranar laraba itace ranarda d`aukacin jama'ar garin kasa'wasa da masu makwabtaka da ita suke cin kasuwar garin wannan ne yasaka mutane daga kowane yanki suke fitowa domin kawo hajar su, to hakan ne ta kasance dani da kuma mahaifin ka a lokacin kana da shekaru shida a duniya, munje kai kayan mafifitai damuke sakawa ne wanda duk ranar kasuwa muke kaiwa domin samun abin sakawa bakin salati, kasancewarmu masu karamin karfi, lfy kalau mukaci kasuwa muka fito a hanyar mu ta dawowa ne muka sami feenah a gefen gwanakin bayan gari tana kanannade a cikin wani zani mai kyau da sheki wanda ban taba ganin irinshiba a wuyanta ansaka mata wata lafiyayyar sarka wadda bansan asalin ta mene ne ba amma na tabbata bata banza bace ta musamman ce wadda tunanina dakuma ilimina baikai na ganota ba, tanata tsala kuka ga rana data daketa muryarta harta disashe, abban ka shiya daukota cikeda tausayi mukazo da ita gida, bayan sallar magariba muka gabatar da ita gamai anguwa yasaka akayita cigiya tsawon sati daya, amma ba,a sami wani dayace yanada  wata alaka da jinjirar ba. 

Umma taja numfashi dakyar sannan taci gaba - "to shine mai anguwa yace mu kawo yarinyar zai bayar da ita a kaita birni gidan da ake renon yaran da ake tsintuwa kamarta, ana cemishi gidan marayu, nan fa hankalina yayi mummunan tashi magana ta gaskiya a d`an zaman da mukayi da yarinyar na tsawon sati d`aya ta shiga raina ba kad`anba. kodan bantaba haifa mace bane? Oho komadai ya'yane sai naji bana son rabuwa da Safeena yarinyar da nasaka mata suna da kaina a ranar da ta cika sati daya a hannun mu, dafari naso na share na mikata amma sainaji nakasa jurewa, kai tsaye na tunkari abban ka da maganar yayimin izni in karbi rikon yarinya Safeenah domin cigaba da rainonta, budar bakin mahaifinka yace " a'a maryama  badai ki reneta ba, cewa zakiyi mu cigaba da rainonta, naji dadi sosai da yanda yabani goyon baya dama banyi tunanin samun matsala ta gefenshiba domin shi mutum ne mai saurin fahimta, kyan hali dakuma tausayi. 

Bamusha wata wahala wajan samun amincewar mai anguwa ba kasancewar mune mutanenda suka tsinto yarinyar, ban sami matsala da kowa ba sai yayata,abokiyar zamana Karai wadda dama ba zaman lafiya muke da ita ba saukin abinma ni bana dakata ta'ta, shiyasa lamura suke mana sauki. 

Also Download: Yar Gwagwarmaya Complete by Yar Mutan Arkilla

Domin ita irin matan nan ce masu zafin kishi da jiyewa, sautari ni nake tare abban ku idan yayi niyyar rabuwa da ita domin munanan halayen larai sun wuce tunanika shi kuma abban ku mutum ne wanda bayason rigima da tashin hankali shiyasa basu cika jituwa da ita dakuma ya'yanta ba. 

hakadai rayuwa tacigaba da tafi mana, da madarar shanu  na shayarda safeenah harxuwa lokacin yayenta, nida abbanka muna rayuwar mutinci da mutinta juna yana kula da mu sosai yarike Feenah tamkar yarda ya haifa da cikinsa ko kadan baitaba nuna mata wani banbanci daku ba, amatsayi na na marikiyarta kuma matarshi inajin dadin hakan sosai.

Amma ita abokiyar zamana kusan ba abinda ta tsana a gidan nan samada ta bude idon ta taga Feenah bansan meyasaka ba, ko kai dana haifa bata hantararka kamar yanda take yiwa yarinyar nan sau tari duk wani duka dazata saka yayunka suyi maka saboda Feena ne domin kaiba kamar ni bane baka iya kyalewa idan aka ci zarafin yarinyar wanda nikaina bayanda na iyane banason fitina ko kad`an   hakan yana damuna sosai yana bakanta raina domin a ganina idan Feena ta kasance cikin takura a karkashin rikona kamar nice na takura mata, amma yazanyi abinda nima ban wuce amin ba? Babu abinda yafi damuna fiyeda barinku nan Ammar, amma nasan Allah yafini, gatan shi gareku yafi dorewar rayuwata tare da ku. 

Ta fasheda kuka sosai, hankalin yaran yakara tashi suma suka koma fashewa da kuka. Ta yunkura ta d`aga fatarinta wata ma'ajiya ta mutanen kauye, taciro wata sarka nad`e acikin wata leda ga dukkan alamu sarkar tasha ajiya ba kad`an ba, tace d`ana wannan itace sarkar damuka samu a wuyan kanwarka Safeenah ka riketa da muhimmanci ka tabbatar ka hannunta ta gareta a lokacin da zata mallaki hankalinta ba mamaki wannan sarkar ta taimaka mata wajen gano asalin iyayen ta  iyayenta wata rana. 

Wannan shine labari akan Safeenah ina fata zaka cigaba da rike ta yanda ka saba. kuyi hakuri da rayuwa a duk yanda ta kasance a gareku, rayuwa dakake gani bata dorewa kamar yanda ita kuma wahala komin yawanta bata kisa.  Takarasa maganarta had`eda sauke ajiyar zuciya mai nauyi.

 Ahankali Ammar ya d`ago da idanunshi dasuka rine suka canza kala daga fari zuwa jaaa! Alamar yasha kuka harya gode Allah domin tunda Umma tafara maganar kuka yakeyi kamar me, yakafe Umma da ido ko kiftawa babu irin kallonda bai taba yimata irinshi ba tunda yazo duniya,  ko'kari yake na saita zuciyar shi ya rarrashe ta ta karbi maganar da Umma tagaya mishi domin yasan Umma bazata taba gaya Mishi karya ba, tabbas uwa uwa ce yau da ace ba Umma ce mai bashi wannan labarin ba da sam bazai yarda ba bayan haka ma bazasu rabu lfy damai bada labarin ba, ya sharce hawayen idonshi sannan ya maida kallonshi ga Safeenah wadda ke makale jikin Umma tana sauraron su sai dai babu wayon gane inda maganar ta dosa. 

Allah sarki tausayi da kaunar kanwar tashi suka bai baye shi ya d`agota daga jikin Umma ya rungume ta sai kawai ya fashe da kuka, ita ma Feenah kukan takeyi ganin yayan ta nayin kuka.

Farin cikine ya lullube Umma dan tasan ko ba rayuwar ta Ammar zai kula da yar'amar ta Safeenah ta yarda da d`an ta d`ari bisa d`ari, wani ni'imtaccen murmushi ne ya wanzu akan fuskarta dad`i ya lullube zuciyar ta, a hankali tafara motsa lebenta tana yiwa yaran fatan samun rayuwa mai albarka da kariyar Allah sanan daga bisani tarufe da karanto kalmar shahada ruf. bakinta ya rufe lokaci daya, fuskarta d`aukeda murmushi. Su Ammar sun dad`e a hakan kafin daga karshe ya sake kanwar ta shi ya koma kan umma yana mata sannu, yadauki farantin robar nan yacigaba dayi mata fifita.

Sallamar ba'ba Uwale suka ji ta shigo gidan kai tsaye kofar Umman su ta nufa ba'ba Larai na daga kofar ta tana ganin ta amma ko sallamar da tayi bata amsa ba saima harara da tsaki data bita dasu, ba'ba Uwale kam ko ajikinta dan tariga ta saba da wannan kasancewar ta aminiyar Umman Ammar. 

Shida Feenah duka suka gaisheta ta amsa cikin sakin fuska ta karasa gaban kawar tata tana gaisheta saitaji shuru ta kura mata ido ba alama ko motsi a tattareda ita, cikin tsoro da firgici tayi gaggawar kai hannunta kan kirjin umman taji shiru ba motsi takoma cirewa tamayar kan hancinta ta kara yatsanta dai dai kofar hancin amma shiru takeji ba numfashi, ta daga hannun ta ta saki sai taga yakoma ragob! Innalillahi wa inna ilaihi raji,un  Allahu akbar! Allahu akbar! dasauri tad`ibi ruwan karamar randar sha dake kusada Umman ta shafeta, sannan taja zanin dake rufeda jikinta ta rufe mata fuskarta.

Ammar yabi ba'ba Uwale da kallon ma'maki fuskar shi da alamar tambayoyi shi atunanin shi Umma bacci tayi sai dai kabbara da sala'lamin ba'ba sun tsorata shi  cikin firgici ya kalli ba'ba hawayen da ya gani a fuskarta sun koma rudar dashi da sauri yamatsa ga mahaifiyar tashi yana ko'karin yaye rufinda aka mata ba'ba Uwale tayi gaggawar riko'shi tana sharar kolla Ammar ya fashe da kuka     "me hakan yake nufi ba'ba? Me ya sami Umma na? Dan Allah kibari in gan ta"

Ba'ba ta kasa rike kukan da ke bijiro mata sai kawai ta rungume Ammar ta fashe da kuka wiwi, "Umman ka ta tafi Ammar yau maryama ta tafi ta barmu da kewar ta ta har abada, sai dai hakuri Amar tariga tayi nisa damu." ta koma fashewa da kuka Ammar ya kankame ta nashiga uku Umma ta mutu? Yadafe kai ya kwarara uban ihu yazube kasa sumamme, abinda yajawo hankalin ba'ba Larai kenan tayo kansu a d`an tsorace ganin umma a rufe Uwale na zubawa amar ruwa yasa ta rafka salati Maryama ta mutu ne? Ta tambaya ido waje ba'ba Uwale bata kulata ba saida taga farfadowar Amar sannan taja hannunshi dana Feenah ta fita dasu sukabar ba'ba Larai nan tana sambatu akan gawar Umma. Amar sai waiwayen gawar yake har suka fita gidan saidai tunda ya farfad`o daga sumar dayayi bai koma zubarda hawayeba yarasa abinda ke masa dad`i jin kansa yake kamar matacce yanaso yayi kuka amma ya gagara yanaso yayi maganar Ummar shi amma ya gagara yin ko d`aya. 

Gidan ta ta kaisu ta zaunar dasu sannan ta sanarwa mijinta da labarin rasuuwar Umma malam bawa shima yaji mutuwar bama kad`an ba da hanzari yafita ya sanarwa limamin garin da mai anguwa nan take mazan garin suka had`u aka suturta gawar Umma aka kaita makwancinta, ta bakunci gidanta na gaskiya. Allah sarki rayuwa kenan Umma kam ta shud`e rayuwar yara ta dawo abar tausayi ba'ba Lrai ta d`an yi sanyi na kwanaki ukun rasuwar Umma.

Yau kwana bakwai kenan da faruwar lamarin Amar yadawo abin tausayi yazama wani iri gaba d`aya ya canza baya magana baya walwala hatta abincin da ake tsakura musu bai damu dashi ba, ga matsi da takurar dayakesha daga Feenah kullum cikin kuka take tana tambayarshi ina Umma,  gaba daya sun rame sun lalace idan ta dameshi da tambayar sai ya fashe da kuka ganin hakan itama saita fara lokaci mai tsayi suke d`auka suna kukan bamai rarrashin wani, wani lokacin sai bacci ya dauke Feenah sannan.

Ba'ba Uwale tana iya ko'karinta wajen kula dasu wani d`an abinci da fura duk ita take basu dukda Amar baci yakeba sai in Feenah ta saka mishi kuka yake daurewa yadan tsakura kad`an. 

Haka sukaci gaba da rayuwa cikin kunci da damuwa kafin sati biyu wata sabuwar wahala ta bud`e musu...............wani sabon salon shafi na zalinci da cin amana ba'ba Larai da ya'yanta suka bud`e musu kullum sai Amar yayi wanki na ba'ba dana yaranta katti guda biyu shine zuwa kiwo da ban ruwan dabbobi shine d`iban ruwan gidan da shara da kankanta gida basubarshi hakaba duk sati sai sun turashi kasuwa yayi dako ya kawo musu kud`i, ita kuwa Feenah bata da aikin daya wuce talla sau uku take daukar awara a rana  da safe da rana da daddare dandali take kaiwa.

Ga yunwa ga detti yara duk sun haukace kai kace ya'yan bayine gabad`aya garin bawanda bai yiwa ba'ba Larai tofin Allah tsine ba sai dai ita ba damuwarta mutane ba, a yanzu jitake ba abinda zai dakatar da ita gayin arziki da wayannan marayun yaran tunda nata ya'yan ba amfanarta suke ba, kyakkyawar yarinya Safeenah ta kod`e tadawo kazama futuk hatta hasken fatarta yafara dishewa gashin kanta da Umma ke gyara duk sati a yanzu sai tayi watanni ko bud`a kan ba ayiba tun bayan rasuwar Umma sau uku suka shiga gidan ba'ba Uwale  ana karshen ne yaya lado ya kama su yayi musu lilis kamar zai kashe su tareda gargad`i mai tsoratarwa shiyasa basu koma shigaba.  

Sai itace take zagayo wa da kanta tazo tabasu abinci ko abinsha ta fita.  Rayuwar yara dai abar tausayi basuda kowa sai Allah duk inda suka bi nuna su ake suna bawa kowa tausayi, sai dai ba wanda ya isa ya taimakesu saboda gudun masifar ba'ba Larai.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post