[Book] Jalala Complete Hausa Novel by Rasheedat Usman

Jalala

Title: Jalala

Author: Rasheedat Usman

Category: Love Story

Doc Size: 436KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2020

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya  Rashidat Usman suna "Jalala" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: "Sauyin rayuwa kan nuna maka alamun ka hankalta, amma ina mamakin mutane da basa gane azancin duniya, duniya tamkar waina ce dake bisa kasko takan iya juya mutum a duk sanda taso, shiyasa ko yaushe nake fatan Duniya ta muku juyin alkairi, domin bana fatan abinda zai shiga tsakanin ku har ya samu damar rabaku tamkar jinina haka nake jinka *_NAMEER_*  so nake ku kasance tsintsiya maɗauri ɗaya har ƙarshen numfashinku,

 *_HISHAM NAMEER_*  ba iya Amini yake a wajen ka ba tamkar ɗan uwa na jini haka yake tunda a hannuna ya tashi tun bayan mutuwar mahaifansa, Soyayyar ku da abotarku tun ta yarinta ne, duk da a zuciyata bana jin akwai abinda zai iya rabaku saboda tsantsar ƙaunar dake tsakanin ku, amma wasiyya da nasiha ta dole ce a gareku, abotarku tana da ƙarfin da tafi jini tasiri, nasan dole ne kuyi nasara akan maƙiyanku ina matuƙar alfahari daku ina muku wannan nasihar ce saboda ita mutuwa bata da notice haka kuma bata ƙwanƙwasawa bawa ƙofa, zan iya komawa ga mahallicina a ko wani lokaci."

    Kallon Nameer Hisham yayi tare da sakin numfashi yace.

    "Abba Ina mantawa da cewa Nameer Abokina ne, kallon jinana kawai nake masa, yana kyautata min Abba, yakan yaƙi da duk wata damuwar da yaga ta tunkaro ne, karka manta Abba, Ammi ta kasance ta bamu tarbiyya iri ɗaya, ta bamu abinci a baki tare, ta share mana hawaye tare, to ta yaya zan ɗauke sa iya Aboki kawai? ya wuce wannan matsayin Abba, domin ƙaunar da nake masa ta kai ga zan iya mallaka masa komai a rayuwata domin kuwa yafi min komai mahimmanci ina matukar alfahari da Nameer Abba shine jigon rayuwata na basa duk wata yardata."

    "Abba Hisham fa ɗan uwana ne ka daina shakku akanmu domin kuwa zamuyi ƙargo har abada, igiyar Amintar mu tana da ƙarfin da bazata taɓa tsinkewa ba ni da Ɗan uwana Hisham mutu ka raba Abba, zamu bawa maƙiya kunya ka kwantar da hankalinka a kanmu Abba."

    "Hmmm! Ni ma shaida ce Abban Hisham domin kuwa yarana basu taɓa ko da cacar baki bane bare faɗa, lokacin Office na ƙurewa kuyi maza kar ƙananan ma'aikata su gaji da jiranku Allah ya muku albarka ya tsare min gabanku da bayan ku."

  Murmushi Hisham yayi tare da cewa.

   "Ameen Ammin mu, mun gode sosai sai mun dawo."

   "Sai mun dawo Ammi."

Shima Nameer yayi Maganar cikin fara'a, da adawo lafiya Ammi da Abba suka amsa, kafin ko wannensu ya ɗauki jakar aikinsa suka fita tare, Murmushi Ammi tayi kafin ta mayar da kallonta ga Abba tace.

   "Abban Hisham, shaƙuwa da ƙaunar junan da suke yiwa junansu har yayi yawa, ina jin Nameer a jikina tamkar ni na haifesa, Abban Hisham, mutane sai saka maka albarka suke bisa ɗaura Nameer a matsayin shugaban Companyn ka *_ HISHAM RICE MILL LIMITED_* madadin ka bawa Ɗanka Hisham ka kyauta sosai na tabbata kuma zai tsare maka dukiyar ka da mutuncin Companynka, Allah ya jiƙan iyayen Nameer mutane ne na ƙwarai da suka san haƙƙin makwabtaka."

Also Download: Indo A Birni Complete by Rasheedat Usman

    Numfashi Abba ya saki yace.

    "Na lura yafi Hisham nutsuwa da sanin abinda yake zaifi mai da hankali ga cigaban Company shiyasa na basa dan haka ki daina gode min abinda ya kamata nayi, Nameer shima ɗana ne."

    "Hakane to Allah yayi jagora, bara naje na bawa TUTU key ɗin store ta ɗauko coffee na kitchen ya ƙare."

    "Okay kina iya tafiya."

Abba yayi Maganar yana maida glass ɗinsa idanunsa tare da ɗaukar jarida ya cigaba da karantawa itama Ammi bedroom ɗin su Nihal ta nufa.

    Tafe suke a ƙas sun fito daga ofishin Jaridar Aminci, suka hango cincirindon mutane, a gefen hanya, duban Basmah tayi tace.

    "Basmah meke faruwa a can.?"

    "Kaji wata tambayar rainin wayo, mu fito tare sannan ki tambayeni aljana ce ni ko boka da zansan abinda ke faruwa a wajen."

    "To sarkin ɓakar magana, ni bara na ƙarasa wajen naga abinda ke faruwa."

  Kanta Basmah ta girgiza tare da cewa.

    "Kina da matsala *JIDDA* baki san meke faruwa a waje ba ki kai kanki saboda kawai kina ƴar jarida mai tarar kasada ko ke gaki mai son ɗauko rahoto."

   "Bani da lokacin ki idan zaki iya zuwa ki biyoni idan bazaki iya ba, mu haɗu a gida."

   Tayi Maganar tana saka kai tabar wajen, bakinta Basmah ta taɓe tare da bin bayanta, ko da Jidda ta isa wajen a cike yake babu masika tsinke jama'ar wajen ta dinga ketawa har ta samu ta shiga tsakiyar wajen da ƙyar, wata ƴar matashiyar budurwa ce baje ƙasa, da alamu bata motsi, yayin da jama'ar dake Wajen suka zuba mata idanu babu wanda yayi yunkurin taimakon ta, jikinta duk ya kuje da alamun yaguni da sauri Jidda ta sunkuya a kanta tana furta.

    "Subahanallah! Meya faru da ita, kun zuba mata idanu bazaku kaita asibiti ba idan ta mutu a wajen nan fa.?"

  Wani daga cikin wadanda ke tsaye a wajen ne yace.

   "Ta yaya zamu sanya hannu a jikinta bayan muna kallo aka wurgota daga mota, mun sanya hannun mu a cikin masifa kike so, idan taimakon ta kike son kiyi to ki fara kiran Police tukunna."

   Ɗago idanunta Jidda tayi a zuciye tace.

    "Amma dai Allah wadarai wallahi kuna kallon mace wurge gefen titi ku gagara taimaka mata, idan ƙanwarku ce zaku zuba mata idanu haka ba tare da taimako ba, mtsss! Wai kuma har kana da bakin bani shawara, ku kauce ku bani ni zan rungumi kasadar idan yaso masifar da kuke gudu ni ta kasheni."

   Tayi Maganar tana miƙewa tare da kwaɗawa Basmah kira, duk kaucewa gefe sukayi suka bata hanya babu wanda ya ce komai a cikin taron, Basmah ƙarasowa tayi ta tsaya a gabanta tare da cewa.

    "Gani kiran me kike min.?"

    "Taimakon ta zamuyi Basmah domin kuwa tana buƙatar taimako ta zubar da jini da yawa Sannan bata motsi zata iya rasa rayuwarta muddun muka tafi muka barta a hannun wadannan marassa imanin."

    "Hmmm! Jidda ba rashin imani yasa basu taimaketa ba, karki musu mummunar fahimta domin kuwa rayuwa ta lalace, a sanadin taimako sai ka shiga cikin wata masifar banga laifin su ba, ko da ma suna da laifi to laifin ɗaya ne na rashin kiran jami'an tsaro da wuri, karmu taɓa wannan yarinyar idan har taimakonta zamuyi to police ya kamata mu kira kamar yadda wannan bawan Allah ya faɗa miki."

    "Kinga Basmah bazan tsaya har sai an kira Police sunzo ba! Kafin a kaita asibiti rayuwarta zamu ceta bama bukatar jira idan zaki taimaka to idan bazaki taimaka ba kija baya zan iya ba tare da taimakon ki ba."

   Tayi Maganar cikin masifa tana fita sarari da kallo Basmah ta bita domin kuwa ko yaushe bata gajiya da mamakin taurin kai da kafiya irin na Jidda ba, sam ba'a juyata inda ta sanya kanta nan kawai takeyi tana kollonta ta taro adaidaita, da ita da mai adaidaitan suka kama yarinyar suka sanya ciki kafin Jidda ta shiga ta tallafota jikinta, Basmah kanta ta kaɗa tare da shiga cikin adaidaitan, harara Jidda ta watsa mata tare da cewa.

    "Nayi zaton ai imaninki ya gushe ashe har yanzu da saura."

  Tayi Maganar dai-dai mai adaidaitan yana ja.

     "Bazaki fahimce ni bane, yanzu da kika ɗauketa kina zaton asibiti zasu amsheta ba tare da Police bane.?"

    "Bazasu amsheta ba na sani, shiyasa ma na turawa Ahmad text cewa kinyi accident muna  IBUNKU OLU CLINIC wataƙil ya rigamu isa kinga police ɗin ma aishi zai jiramu."

    "What! Jidda meye kikayi haka."

    "Ceton rayuwar mace ƴar Uwar mu shi nayi ko akwai laifine ayin hakan."

    "Ƙwarai kuwa akwai babban laifi ma, akan me zakiyi ƙarya dani ki faɗa masa gaskiya mana zaki wani ɗaura min mungun abu."

    "Koma dai mai zaki faɗa kiyi haƙuri ni ne na miki laifi amma kin sani muddun na sanar dashi gaskiyar abinda ke faruwa ba zuwa zaiyi ba."

    Tsuka Basmah taja cikin ɓacin rai tace.

     "Dole ki bani haƙuri ai tunda kin cuceni."

   Tayi Maganar dai-dai suna shigowa asibitin, shima Ahmad dai-dai yayi parking ɗin motarsa ya fito a gigice turus ya tsaya ganin  Basmah sun rungumo wata, wajen su ya ƙarisa da sauri yace.

    "Jidda ya haka kince Basmah tayi accident kuma naga kin rungumo wata ga Basmah tsaye lafiya.?"

      "Ahmad bamu lokacin Doguwar magana dan Allah ka sanya hannu a duba wannan baiwar Allah, kafin mu maka bayani, a gefen titi muka tsinceta cikin wannan halin."

    Ahmad zaiyi Magana Basmah ta katsesa da cewa.

     "Kar ka mata gardama domin kuwa kasan mayya ce ita, ka sanya hannun."

     Numfashi Ahmad ya saki kafin likitoci suka taho da keken marassa lafiya aka turata, ganin Ahmad da kayan Police a jikinsa, bayansu yabi ya cike dukkan wata takadda rashin sanin sunanta yasa ba'a rubuta sunanta ba kafin sukayi emargency da ita.

    Bayan an shiga da ita ne Ahmad yayi kan Jidda da faɗa na ɗaukar wannan kasadar, ita dai bata kulasa ba, suna nan tsaye har doctor ya fito duban Ahmad yayi yace su samesa a Office bayansa sukabi tare da zama doctor ya dubi Ahmad yace.

     "Wannan marar lafiya da kuka kawo, gaskiya ta zubar da jini da yawa, muna da jinin da yayi dai-dai da nata kasancewar tana neman jini cikin gaggawa yasa bamu muku magana ba muka sanya mata da alamu faɗowa tayi daga sama ko dai something haka ta kuje sosai amma dai Alhamdulillah! Babu matsalar buguwar kai, mun mata allurar bacci sannan akwai zazzaɓi a jikinta zata iya farkawa ko wani lokaci zakuje receiption ku biya kuɗin jini, ga kuma takaddar magani zaku saya."

   Hannu Ahmad ya sanya tare da amsa yace.

    "Thank Doctor."

Tashi yayi ya fita bayansa suka biyo, Jidda ce tace.

     "Akwai kudi a account ɗina ni zan biya wannan taimakon da kayi da jikinka ma kaɗai ya wadatar na gode sosai."

    "Hmmm! Jidda kece zaki biya kudin kika ce, Karki manta ɗawainiyar mahaifiyarki da ta ƙaninki kuɗin hayar gidan ku duk a kanki suke, dan haka idan ba'a ƙara miki ba baza'a rageki ba, ni zanje na biya da aljihu na."

   Numfashi Jidda ta saki tana ganin darajar Ahmad sosai musamman yacce yake tausayawa rayuwarta.

    "Hakane Ahmad na gode sosai, yanzu yaya za'ayi da kwana a wajen yarinyar kaga fa Ummana ba lallai ta amince na kwana ba infact ma bazata yarda ba."?

    "Karki damu Jidda, zan kira A'isha sai tazo su kwana zuwa gobe ta dawo hayyacinta sai musan ahalinta, kuna iya tafiya zanje na gama komai kafin Aisha tazo ni sai na wuce."

   Murmushi Jidda ta yi tace.

    "Na gode Ahmad Allah ya maka abinda kayiwa wannan yarinyar sai goben."

  Tayi Maganar tana yin gaba, Basmah duban Ahmad tayi tare da sakin murmushi tace.

    "My Dear ina matukar girmama Soyayyar mu, kai Mutum ne na Musamman a rayuwata, ina sonka matukar Soyayya."

    "Hmmm! Basmah idan ban kyautata miki ba waye zan kyautatawa, kinfi ƙarfin komai a gareni Basmah dan haka ki tafi kuje huta zan shigo anjuma."

    "Shikenan farin ciki na bye."

   Tayi Maganar cike da soyayya tana bin bayan Jidda.

            💫💫💫💫💫💫

 "Na rantse da Allah sai naga bayan zuri'ar Iyabo bazan taɓa gushewa ba sai naga ƙasƙantarsa da tozarta sa, koda kuwa zanyi yawo tsirara, nasan zuwa yanzu saƙona ya fara ƙwanƙwasa musu ƙofa, sai na sanya su a cikin *_JALALAR_* da sai sun roƙi mutuwa da kansu, *TUNDE* muddun kai jinina ne to tabbas bazaka gushe ba har sai ka ɗauki bashin gabar da ke tsakanin mahaifinka *Babawale* da *Iyabo*, kadda ka saurara musu nima kuma bazan saurara musu ba, na sanya mutanena a cikin Companyn su suna sanya min ido akan dukkan  abinda zaije ya dawo acikin Companyn to yana tafin hannuna dan haka karka saurara."

   *Mama Bisola* tayi Maganar cike da tsantsar wutar fansar dake ruruwa a cikin zuciyarta da tsanar familyn Iyabo.

    "Mamabisola karki manta cewa babu mutanen dana tsana a wannan duniyar sama da su Iyabo ba kuma zan gushe ba har sai naga bayansu, daga ƴaƴansa zan fara da wannan tsintaccen yaron da ya ijiye ya basa yardarsa fiye da matar sa da ɗansa, wallahi Mamabisola sai na sanya su kuka a tsakiyar titi."

    "Haka nake so Tunde kaje kana tare da Sa'a."

    "Na gode Mamabisola, zan wuce wajen Bola."

   "Ka dawo lafiya."

Mamabisola tayi Maganar cike da ƙaunar Tunde, yana fita  Wemimo dake gefe zaune ta dubi Mamabisola cikin harshen yarbanci tace

    "Mamabisola, ina mamakin yadda Iyabo ya bawa wannan dan Hausan Amana sunansa Nameer ko, meyasa ya basa shugaban Kamfanin sa bayan ga Hisham ɗansa.?"

    "Hmmm! Wamimo ke kanki hakan zai baki mamaki har yanzu ban gano wani ƙwaƙƙwaran dalili da yasa yayi hakan ba, duk da cewa yaron abokin ɗansa ne, amma ni na sani sai yaci amanarsa domin kuwa Hausa babu amana."

    "Hakane Mamabisola, amma Mamabisola, gani nayi kinfi MamaIyabo yawan yara naki yaran Uku ne, ita kuma MamaIyabo nata yaron ɗaya ne Iyabo amma har kikayi sake dukiyar MamaIyabo ya yaɗu ku naku ya lalace, meyasa Mamabisola, meyasa kuka sake haka."?

    "Hmmm! Wamimo bazaki fahimta ba, amma maigidan mu shine wanda ya cuce mu ni da yarana, shi ya bawa Iyabo ƙyautar Companyn sa na Auduga, wanda bai shiga cikin gado ba, wanda shine yanzu iyabo ya gyarasa ya maida shi  Hisham rice mill limited, wanda a yanda Ademola yake sanar dani a ko wani wata suna samun kuɗi sama da 50m ni kuma gani ni da ƴaƴana muna zaune bama samun rabin abinda suke samu, dan haka Wamimo na ɗaura aniyar tozarta rayuwar Iyabo da iyalinsa, wacce hanya ce zaki iya taimaka min."?

   Numfashi Wamimo ta saki tare da cewa.

   "Huuuu! Mamabisola, ni kuwa nake da hanyar taimaka miki, zamuje wajen sarkin aljanu domin ya tarwatsa dukiyar su rasa komai ya kike gani zamuje."?

    Girgiza kanta Mamabisola tayi tace.

    "No Wamimo, bazai yiwu zuwa wajen Sarkin Aljanu yanzu ba domin kuwa mai gidan mu *ABDULWASI'U* yayi kafi a jikin yaransa idan mukayi tsafi yanzu zai iya dawowa kanmu, da badan wannan kafin ba, da na juma da hallakar da Iyabo, sai dai taimako ɗaya zaki min ki shiga ki fita wajen sarakan tsafi ki samo min makarin kafi idan har aka samu to tabbas zan hallaka Iyabo da tsafi."

    "Za kuma a samu tabbas ni ne nake tabbatar miki da wannan, zan fara bibiyar Sarakan tsafi kuma sai na kawo wannan makarin."

    "Idan kika min haka Wamimo bazan taɓa mantawa da ke ba, kije ki bincika ni kuma zan cigaba da jifansu da makaman sharri."

    "Baki da matsala Mamabisola, ni yanzu zan shige sai gobe zan fara nawa aikin."

    "Na gode Wamimo muje na rakaki."

   Mamabisola tayi maganar tana tashi har bakin get ta raka Wamimo kafin ta koma cikin gida.

   *****************************

  A bakin ƙofar gidan su Jidda suka rabu da Basmah kasancewar gidan su Basmah yana gaba da nasu Jidda, sallama sukayi da nufin sai gobe zasu haɗu, kafin Basmah ta shige ita kuma Jidda ta shiga cikin gida, Umma ta samu zaune a tsakar gidan gefenta kuma AbdulRahman ne yana mata wanke wanke zama tayi tana cewa.

     "Wash Umma na gaji sosai yau."

    Murmushi Umma tayi kafin tace.

    "Ai dole ki gaji jiddatul kair tun safe fa kika fice, kece sai yanzu gabannin magaruba, meya tsayar dake ne haka ke da kika saba dawowa 4:00pm.?"

   "Hmmm wallahi Umma wani matsala ne ya faru a hanyar mu ta dawowa, wata yarinya ce aka bigeta da mota to shine muka taimaka ni da Basmah aka kaita asibiti yanzun ma daga asibitin muka dawo shiyasa nayi dare."

   "Subahanallah! Amma dai haɗarin da sauƙi ko.?"

    "Ehh Umma da sauƙi sosai ma, amma dai mun baro asibitin bata dawo hankalinta ba, amma likita yace zata farka lafiya."

    Gyaɗa kanta Umma tayi tace.

   "To masha Allah, Allah ya bata lafiya, ki cigaba da taimako Jiddatul kair insha Allah kina tafe da gagarumar nasara a rayuwarki, nakan jin daɗi harma nayi alfahari idan naji kin taimakawa wani, Allah ya miki albarka ya rabaki da sharrin maƙiya."

    "Ameen Umma."

"Adda Jidda sannu da dawowa."

    "Yauwa abdulrahman kana taya Umma aiki ne, magaruba ta gabato, ka tashi kaje kayi alwala ka tafi masallaci bara naje na ijiye mayafi na sai nazo na ƙarisa wanke wanken."

    "To Adda."

Yayi Maganar yana tsame hannunsa daga ruwan wanke wanken, ya ɗauki buta Jidda tashi tayi taje ta ijiye mayafinta da jakarta kafin ta dawo ta idda wanke wanken, ita ta tuƙawa Umma tuwon kafin aka kira sallah sukayi alwala sukayi sallah bayan sun idar ne ta ɗauki Alqur'anin ta ta hau karatu bata idda karatun ba har sai da tayi sallar isha'i"

   "Jiddatul kair tashi kije ki sako mana tuwo muci, naga alamar Abdu bazai shigo yanzu ba."

   "Ina ga sun tsaya karatu ne, bara naje na ɗauko."

  Tayi Maganar tana tashi taje ta ɗauko musu tuwan masara miyar ɗanyar kuɓewa, zama tayi ta ijiye tuwon tare da Bismillah suka fara cin abincin babu wanda yayi magana har suka kammala cin abincin suka wanke hannu sannan Jidda ta fitar da kwanukan ta dawo."

     "Umma wai nikam dama haka yaruba suke basu da kirki."

   "Jiddatul kair meyasa kika min wannan tambayar wani abin suka miki na rashin kyautatawa.?"

    "A'a Umma wacce nace miki an bigeta da mota mun kaita asibiti ita suka gwadawa rashin imani domin kuwa Umma Yarinyar ta juma sosai wurge tsakiyar titi cikin halin rayuwa ko mutuwa sun cika a kanta Umma amma babu wanda yayi tunanin taimaka mata sai ma idanu suka zuba mata tamkar tv suna kallon ta hakan ya ƙona min rai sosai Umma."

   "Jidda a gaskiya Bayarben mutum, bashi da daɗi ta wani fannin amma ta wani fannin kuma yafi kowa daɗin mu'amala, domin kuwa ba duka aka taru aka zamo ɗaya ba, basu da matsala ta fannin mu'amala domin kuwa suna kyautatawa talakan da suka fisa ƙarfi, nayi zama cikin su sosai na fahimci ɗabiun su suna da zumunci da kyautatawa ga maƙwabci, amma nayi mamaki da basu taimaki wannan Yarinyar ba."

   "To dai gashi basu taimaketa ba, ni har na fara ma jin haushin wannan yaren Yaruba basu da im............

    "A'a jiddatul kair kul kika ƙarisa, ko kin manta Mahaifiyata Yaruba ce kike ƙoƙarin aibata su.?".

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post