[Book] Kishiyar Uwata Complete Hausa Novel by Rabi'atu Abou Hama

Kishiyar Uwata

Title: Kishiyar Uwata

Author: Rabi'atu Abou Hama 

Category: Fiction

Doc Size: 171KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya Rabi'atu Abou Hama mai suna "Kishiyar Uwata" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: """"""""""""""""""""""Wallahi yau idan baki siyar da awaran nan ba kika maidomin ita na rantse da Allah  na lahari ma sai ya fiki jin dad'i kuma mai ceton ki a hannuna ba a haifeshi ba, shashashar Banza balagaza matsiyacita Inna Beeba ce  ke wannan cin mutuncin da zage zage.

Ke Aqeelah ba Kai jinane wace Aka Kira da Aqeelah ta d'ago kanta sai hawaye  shar a fuskarta  tashi tayi ta d'auko robar awarar kuma babbar robace tana cike fal da awara ga kuma robar miya da tashshi { yaji } kuma wai dan tsabar rishin Imani KO d'a guda ta maiyar gida  sai anci Ubanta.

Aqeelah tun da ta tashi da safe itace tayi aikin gidan kama daga shara wanke wanke ta had'a musu abunda zasu yi kumallo da shi kuma idan akwai wanki sai tayi shi babu islamiya babu boko dama dama wani lokaci ana Barinta ta tafi islamiya.

Yar lele kina ina ne har yanzu baki gama shiryawa ba ki huce school kar kiyi late kuma ga Kwai da biredin ki nan da tea  ki zo Maza ki karya Bana son kinayin late wace Aka Kira da yar lele da sauri ta fito cikin inuforme kinta na school sunanta na gaskiya Aseeyah amma mahaifiyarta ke Kiranta da yar lele saboda ita kadai ce yarta wannan kenan.

Kusa da Inna Beeba ta zauna Inna da kanta ta had'a mata tea mai kauri ta d'an juyashi dan ya yi huce kad'an sanna ta Mika mata ta turamata plate kin Kwai da biredin gabanta ta fara ci wani lokaci ma Inna Beeba da kanta take bata a baki.

Aqeelah na tsaye tana kallon su  Inna ta ce " ke mayar banza lafiya kika tsaremu da ido kina kallon mu kamar baki tab'a ganin mu ba iyeeee yar lele ta ce" ni har tasa na shake  cikin ladabi Aqeelah ta dukar da kanta kasa ta ce " Inna nima banfa karyaba wani wulakantance kallon Inna ta wurgama Aqeelah sanna ta kalleta sama kasa ta ce "  kije ki d'auko kunun jiya na abban Ku da ya rage kisha maza ki huce talla jakar Banza ,  yar lele ta bushe da dariya ta fara wurgama Aqeelah habaici Hummm kuma  wai agaban uwar tata.

Madafa Aqeelah ta nufa ta d'auko robar kunun ta fara sha har ma ya fara tsami haka ta shanye shi tas saida ta wanke robar sanna ta zo ta d'auko robar talarta ta huce salama tayi musu ta ce ta tashi amma da harara sukka raka bayan ta har ta bar gidan.

Itakuma yar lele bayan ta gama kudi akabata masu yawa wai ta hau nappen saura kuma ta yi anfani da su a makarantar idan kuma ta dawo nappen zata hau wai ba a son tana shan wahala cewar Inna Beeba . yar lele bata tab'a fashin zuwa school ba amma islamiya batama zuwa KO itada Inna Beeba KO  cikakkar alwalla basu iyaba sai cin mutunci wannan Shine first wurin su.

Abbansu shi tun asuba yake fita kasuwa sai dare yake dawowa baisant wainar da ake tuyawaba a gidan ba koda ma yasani ba abunda zai yi saboda an mayar da shi mijin Hajia wato Inna Beeba ta mallakeci sai abunda ta ce kamar wani karamin yaro haka yake bin umarninta kuma duk sharin da ta kulla ma Aqeelah Gurin Abbansu sai ta Sami nasara dan kawai a ci uwarta KO amata fad'a kuma duk Tallar nan da takeyi Inna Beeba bata gani bata siyamata komai kullun cikin tsumma take kamar wata buzuwa haka zata kawo mata kud'in ta Cif KO kaundala bata kashewa amma KO sisi bata bata saidai zage zage wannan kenan.

Yar lele idan ta fita gidan nasu yawon banzanta take zuwa don tana yin wata sati BIYU UKU bataje school ba Saïda jefi jefi takan dan leka sai dai taje yawonta idan lokacin tashi ya yi ta shigo nappen ta dawo gida yar lele jaka ce ta bugawa a jarida dumin komai bata ganewa a school sai iskanci kuma batada kawaye sai Maza Inna Beeba batayi boko ba shiyasa batasan tsiyar da yar lele takeyi ba tana nan tana buga gaba da ita wai tanason Aseeyah ta Zama babbar Doctor shiyasa take ji da ita batason abunda zai sameta kuma ko an gayamata Aseeyah bata zuwa school har abada bata yarda kuma duk wanda ya kawo kararta Saidai ya koma da kunya saboda cin mutuncin da Inna Beeba zata ratatoma sai dai kace Allah ya shirya yanzu babu mai kawo karar yar lele saboda KO ankawo kararta Inna Beeba bata yarda.

Ta ce " ita tasan d'iyarta baza ta aikataba duk sharin ne ake yi mata idan da Aqeelah ce to zata yarda kuma Aseeyah karya take shararama Inna Beeba ita kuma dan tana gara ta yarda wani lokaci yar lele har ce mata take wai a school Ance akawo kud'in exams KO kuma ta ce wai principal ya ce  akawo kud'in rula kud'in Pen kud'in shiga class kud'in kaza kud'in masa Inna Beeba dan batayi boko ba shiyasa Aseeyah ta Sami damar yi mata karya kuma KO nawa ta ce Inna Beeba sai ta bata kud'in babu bincike wannan kenan.

Duk abunda Aseeyah keyi Aqeelah agaban idonta  taita shara rawa uwarta karya KO tausayin ta batayi Aqeelah dake wahala tafi ta ma tausayin Inna Beeba wannan kenan.

Aqeelah Inna Beeba ta sa aka cireta daga school kawai don tayi mata talla ta shiga tafito saida ta sa Abbansu ya cireta daga school kin kawai dan tazan yimusu talla da aikin gida wanni lokaci ana Barinta ta tafi islamiya idan Inna Beeba ta ga dama kuma Aqeelah akwai ilimi sosai kanta nada saurin d'okar Abu amma an hana ta zuwa school islamiya ma ta sabka amma har yanzu ba'amata Walima ba harda ne takeyi idan tasamu anbarta taje kuma litattafai dayawo ta sauke su kamar su kawa'idi ,  Ahalari , ishmawi sira da dai sauran su.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post