[Book] Kululu Complete Hausa Novel by Mrs AM

Kululu

Title: Kululu

Author: Mrs AM

Category: Love Story

Doc Size: 147KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2016

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya "Mrs AM" mai suna "Kululu" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: Tafe take tana akin mita duk ta danai baye jikinta da kasa kusa da ita na masa don na dauko muku rahoto mamakine ya kamani ganin yarinyar baxatafi shekara goma sha biyu ba, fara ce gas irin farinnan mai sirkin ja bata cika tsayiba don baxa akirata da doguwaba Kuma baxa acirata da gajeriyaba tana dauke da manyan idanu masha Allah da dogon hancin daya dace da round face dinta sai bakinta dan karami da ya sha urban bakin jambaki idanun nan yasha hawayen masoyi haka ma girarta tayi cinku da jar jagira kannan jazir da shi uwa na.

Wata yarinyace sa'ar ta taxo tana cewa HAJJA KULULU don girman Allah kiyi hakuri wallahi subutar baki nai na gayamiki, aiko juyowa tai ta rice kugu tace to dan abu takaxar uba.

Sai naje Inga hege ko hegiyar dazata hannani tana gama fada haka ta juya ta cikagaba da tafia kamar xata tashi sama.

Ai da mugun gudu zainaba tabita tana kara bata hakuri ko kulata bataiba saida taje bakin tafi tukun ta tsaya ta karkace kai gani da daure fuska tamau sannan ta kalli dandazon yan matan dake tsaye suna diban ruwa suna hira jifa jifa Aina'u ce tace kai kawayena kunsan mai naji jiya a dandali.

Ai da sauri indo ta cafe xancen mai kka jiyo ne kawas, Aina'u ce tace hmm wai fa kululu ce take cewa wai ai ke kincika jarabar san iro dan mai gari bayan Kuma shi yace bake yakeso ba ita yake so ba shine fa nikuma kinsanni bana gani ana fada ban mayar ba sai nace ai karyane yafi sonki karkiso kiga nai tamin wallahi, ta karashe maganar tana dafe kanta, indo ce ta dafata tace kedai kawata barni daita hegia mai manyan Ido kamar na mayu, kuluwa dake gefe ta xaro ido tana kara kwalale idon Zainaba kuwa hannu tasa aka tanacewa yau mun shiga uku an tabo ta kula.

Kululu ce ta zagayo ta bayan indo yadda baxa ta ganta ba ta sharara mata mari ji kka taasssaa ai take gurin kowa ya mike suna zare ido ai kululu taba kasa a gwiwa ba ta zagayo ta ta janyo rigar indo tana cewa nice mai idon mayun ko wallahi yau saina ga karshen iskanci yarinya donkinga ynxu na rage masifa ko ta karashe tana zaro ido waje take jikin indo y fara rawa kamar mazari don tasan mai kwatanta a hannun indo sai Allah ai kuwa wani wawan naushin da kululu tai mata a ciki shi y dawo daita daga duniyar tunanin da ta tafi haka kuluwa taita dukanta har ta gaji don kanta ai kuwa tana daga indo sukai ido hudu da ismaila yayan indo ai a guje ta daga indo tana wani walwal da ido taba ballamasa harara yana xuwa kuwa y kwarfeta ta fadi ji kke tummmmm y munata yana cewa banxa wawiya mikewa tai tace ynxu ni ka kwarfe yace anyi xaki ramane, murmushi tai wanda y baiyyanar da beauty point dinta tace Aa ya ismaila duk gurin shiru yai ana kallon kululu jin abinda tace don kowa yasan da wata a kasa karkade jikinta tai ta janyo Abu tace muje kawai binta Abu(zainaba) tai aran tace mai kuma kululu Zara hadama ismaila shiru tai kawai. 

Saida ta bari sukaje lungu sannan ta tsaya tace kawata don Allah kije kasuwa kicema baba habu(Mahaifin su iro) ganinan a gida ina ta zubar da jini niko nace mai kuma zata hada muje dai zuwa) zaro ido waje Abu tai tace kululu mai xaki hade rai tai tace xaki ko baxa kiba ai da sauri tace zani tai gaba kululu kuwa tsayawa tai ta tuntsure da dariya tace wallahi zakaci kaniyarrka ismaila bara tsohonka yaxo hmm.

Also Download: Noor Complete by Mrs AM

A guje ta shiga gida tana haki tanacewa inna inna wai kina ina ne tsohuwa ce yar kimanin shekaru 68 ta fito daga wani daki tana cewa lafia mai y faru kuma yar nema murmushi tai taje kusa da tsohuwar ta rungumeta tana cewa innata innata ina sonki gaskia murmushi inna tai tace nima haka yar jikata, kamar an mintsuneta ta tashi ta shige kichin ta dauko zobo ta jika ta dawo ta zauna suna hira da kakar ta acikin ranta kuwa sai dariya take in ta tuno taasar da zatai in baba habu yaxo (ni dai nace ashuka Alkhairi dai ko y kka ce readers).

Zaune yake a wani makeken daki ya harde kaga daya kan daya wayace a hannunsa yana latsawa fuskarnan tasa a daure kamar  ko yaushe subhanallah na furta lokacin daya dago kyakkawane ajin karshe fari ne mai doguwar fuskar yana da manyan idanu masu dauke da kwayar ido blue yana da dogon hanci siriri kamar pencil ga bakinsa karami mai dauke da red lips yana da saje mai kyau wanda y hade da quarter million dinsa yana da sumar kai mai kyau a takaicedai ya hadu iya haduwa, abokinsane yace MATAWALLE don Allah ka shirya kaga fa kai kadai muke jira, saida yadau tsawon minti 2 sannan y mike Masha Allah nace don ganinsa a tsaye dogone sosai  mai cikar hallitta da haiba yana da faffadan kirgi a hankali y jiyo yana duban abokin nasa sannan yace to na daure ma kafane ku tafiman ai zanxo murmushi kawai Has him yai sannan yace Aa amma ai nafiso muje tare bai tsaya basa ansaba ya wuce y shige wata kofa da nake kyautata zaton bandakine shiko hashim murmushi y karayi yace Allah y shiryeka MATAWALLE ya mike yana mai dauko masa wata rigar yan ball wadda abaya aka rubut.

MATAWALLE saida ya dauko masa duk abinda xai bukata sannan y koma ya zauna.

Fito Abu tai Wanda ya ankarar da kululu ai a sukwane ta mike ta mufi inda ta aje zobonta ta duba aikuwa tai jazir ta debo ta xuba a hannayenta da kafafunta sannan a goshinta ta mike tana tafia da kyar kamar wacce tai hatsari ai a sukwane baba habu y shigo jin kukan kululu.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post