[Book] Lamarin Duniya Complete Hausa Novel by Khadija Candy

Lamarin Duniya

Title: Lamarin Duniya

Author: Khadija Candy

Category: Fiction

Doc Size: 81KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2020

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya "Khadija Candy" mai suna "Lamarin Duniya" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: Cike da gajiya ta shigo parlor kamar  zata fadi kana ganinta kasan jikinta babu karfi saida ta kawo kusa da hajiya shafa Sannan ta zube zaune kasan carpet.

Cikin kasalalliyar murya ta shiga mata magana hajiya na kare aikina fuska a hade ta kalleta cikin isa tace tohm mie zan miki.

Kasa tayi da kanta dan ganin irin kallon da take mata tace daman gida zan wuce dauke kanta tayi daga hararar da take mata tace to nidai yau abinci kadan nayi kiyi hakuri a gaida gida bata ce mata komaba ta tashi cike da damuwa ta nufi kofar fita.

Da sauri kdeey dake dining area ta kwala mata kira fatima a hankali ta juyo naam aunty kdeey tana sude hannu tace zo ki dauki wannan abincin ni na koshi.

Karasawa tayi ta dauki plate din ta kalleta tace na gode, murmushi tayi tace ki hada dana yaya umar yana kitchen kai kawai ta daga mata ta fice.

Tana shigowa gida jidda ta nufo.ta DA gudu tana fadin batula sannu da zuwa yauwa sannu ina umma DA yatsa Jidda ta  

Nuna mata ita " gata can" ta shiga kokarin karbar ledar dake hannunta sakar mata ledar tayi ta karasa karkashin bushiyar durumi inda umma take it  kwance zauna tayi  saman tabarma Tana sauke ajiyar zuciya.

Tasa hannu a hankali tana shafa fuskar umma tana murmushi mutsawa ta farayi sannan ta bude ido suna hada ido ta tashi zaune da sauri tana gyara daurin dankwalinta 

"sannu batula kin dawo " "ae umma na dawo" juyawa tayi ta kalli jidda dake juye abincin dake cikin ledar a roba tace "ki karaso nan kuci da umma mana ", "to bari na karasa ".

Also Download:

Bayan ta kare ta taso rike da abinci  ta nufo gurin da suke zaunawa tayi tare da dire abincin gaban umma tana fadin " gashi kusa hannu muci ni yunwa nake ji Kuma ma abincin ba shida yawa  " fatima tace " to ya za'aiyi yau hajiya bata baniba cewa tayi bata girka abinci da yawa ba wannan ma ragowar yayanta ne".

Kallon abincin umma tayi tana hadeye yawu tace " to kuci nidai naci abinci makota dazu " kallonta fatima tayi " haba umma wane irin makota kuma kufa na kawowa dan ni wlh naci acan." 

Kawar da fuska umma tayi tace " to ai saiki kara dan nasan baki koshiba " Fatima tace " dan Allah umma kici wlh ni naci a can wadda Kdeey ta raga sai nazo muku DA wannan Kuma kinji Na rantse ai " juyowa umma tayi ta zira hannunta cikin robar abincin da sauri2 take cin abincin  dan ba karamar yunwa takejiba Fatima dake kallonta idonta suka ciko da kwalla DA sauri ta kawarda fuskarta dan kar umma ta.gani tashi ta nufi daki.

Washe gari fatima ta shirya cikin kudaddiyar atamfarta sai shafe2 fuska take da raggagin kayan kwaliyarta tana karewa ta dauki  hijab tasa ta nufo umman dake shan koko+kosai da malam rufa'i ya aiko mata tana fadin " ni zan tafi umma " jidda ta kalleta." bazaki kisha kokon ba "?

Umma ta riko ta " zauna kisha kokon sannan kitafi kinma yi latti " turo baki tayi " ni wlh aikin nan ya fara isata ace mutum tun safe in yaje bazai dawo ba sai maraice kuma bako wani albashin kwarai ba kuma ba abincin kirki ". 

Umma tace " kiyi hakuri nima ina nan ina nema kinga dana samu sai ki daina zauna kisha kokon " a a umma kusha kawai ni can zan karya kinsan bason koko nakeyi ba " 

umma tace " ai dakin sha ko kadan ne karki fita baki karya ba " dukawa tayi tayi ludayi daya ta tashi " nikan na tafi " umma tace"to Allah ya tsare yayi miki albarka " murmushi tayi tace " amin umma sai na dawo " daga mata kai umma tayi, tafice.

Tana isa parlor ta fara wuce wa a dining area ta tararda su suna karyawa cikin ladabi ta isa gurin cikin girmama wa ta shiga gaisu hajiya shafa  " hajiya ina kwana anty Kdeey yaya umar nabila an ashi tafiya "? 

Duk suka amsa Mata  banda HAJIYA shafa 

Kdeey ta kalleta tace " kinyi kyau fatima " murmushi tayi "na gode " ta yunkura zata tashi Hajiya shafa ta watsa mata harara " kekeke zo ki kwashe plates din nan yar raini hankali kullum sai rana tayi falfal kike zuwa ke ishashiya ko "?

Batace  da ita komai ba dan tasan ko hakuri ta bata ba hakura zatayi ba, tana cikin kwashe kwanukan nabila ta kalleta da fuskara kyankyami " waike baki da wasu kayan ne kusan koda yaushe kayan nan kike sawa "?


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post