[Book] Life Partner Complete Hausa Novel by Real Teemarh

Life Partner


Title: Life Partner

Author: Real Teemarh

Category: Love Story

Doc Size: 364KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya "Maman Usee" mai suna "Yar Baiwah" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: A firgice ta mike tana kallan agogan dake manne a bangon dakin, ta zare manyan idanuwanta waje ta ce"What!!! Past 8". 

Quickly ta janye duvet din dake jikinta ta shige bathroom hankalinta a tashe, bayan 6 minutes ta fito daure da towel ta nufi gaban mirror, comb ta dauka ta fara combing gashinta, nan da nan ta gama ta dauka ribbon tayi packing smooth hair dinta waje daya, daga nan ta fara robbing body lotion shap-shap. 

Cikin few minutes ta gama ta nufi press dinta ta dauko doguwar riga baki ta saka kafin ta dauko veil dinsa ta yafa ta jawo side bag dinta dake jikin bag hanger sannan ta fice a dakin, daidai shoe rack ta tsaya ta dauka flat shoe sannan ta kama hanyar stairs cikin sauri ta fara saukowa. 

Ba kowa a falon sai TV dake kunne sai karan standing fan, hakan yasa ta wuce kitchen da gudu tana fadin "Ummi! Ummi!" Kafin ta karasa shiga kitchen din Ummi ta fito rike da warmer, kana kallanta kaga mahaifiyar yarinyar saboda tsantsar kama da suke. Ummi ta mata wani irin kallo ta ce"Are u ok? What's the essence of running" ta ce" Ummi ina da appointment a clinic yau fa" ta karashe maganar in a hurry, Ummi ta dalla mata harara ta ce"Wa kika gayawa to?", a hankali ta dan gyara veil dinta ta ce"I'm sorry Ummi, jiya da doctor hisham ya kirani kin riga kin rife kofa, and i didn't woke up early today". Ummi ta ajiye warmer din hannunta akan dinning ta ce"Kije Mustapha ya kaiki, i think i don't have to go,". Silently ta ce "To saina dawo" daga haka ta fice a kitchen din ta nufi kofar fita. 

Babban gidane na gani na fada, yana dauke da shuke shuken flowers all over, part guda biyu ne daya na kallan daya sai kuma BQ daga gefe sannan parking lot a tsakiyan apartments din wanda ke dauke da motoci 6. 

Da sauri ta karasa jikin motar tana kallan Mustapha ta ce"Na makara fa Musty, kuma cewa yayi he's leaving the country today" ta karashe maganar tana shiga back seat, Mustapha ya rife kofar ya zagayo cikin hanzari ya shiga driver seat ya kunna motar yana fadin "Yanzu zamu isa Hajiya Karama, aini inasan shiga asibitin nan kodan ina ganin turawa, ance nasu nema asibitin ko?". 

Murmushi tayi me kyau ta ce"Sure, amma ai mutanenmu na nan suna aiki a caan" Mustapha ya washe baki ya ce"wa yake ta bakar fata Hajiya karama, ai turawan sunfi dadin gani, kaii Allah yayi halitta, farare kal kal dasu kamar ka bigesu jini ya fito, nifa ban ta6a ganin turawa ido da ido ba a garin kano sai a asibitin nan" ta ce"To menene abin san gani a jikin bature Mustapha, sai wani zuzutawa kake" cikin sauri ya ce"Ai wallahi Hajiya karama bature abin a ganshi ne, aini dana zauna kallan bakar mace gara a kaini gaban tsohuwar baturiya naita kallanta ina maimaitawa", dariya sosai tayi kafin ta ce"Wato dai Mustapha bakasan ganinmu kenan, kace  baturiya zaka nemo" zaro ido yayi ya ce"Na isa ince banasan ganinki, ai wallahi dana fara ganinki na zata bakyajin hausa sai larabci" dariya ta fashe dashi tana girgiza kai, duk drivers din da suke yi a gidansu tafi san Mustapha saboda idan yana mata hira yana sata nishadi, ko bata da lafiya inya shigo gaisheta sai yasan yadda yayi ya sata murmushi. 

Yana parking ta fito a motar tana kallansa ta ce"To zan shiga Mustapha, ga turawa nan aita kallansu, idan na fito ka fadamin wacce ka za6a" bata jira amsarsa ba ta wuce ciki saboda sauri da take.Kamar me counting steps ta shiga clinic din very gentle, office din dake gefenta by d left ta nufa ta fara knocking a hankali, ta ciki aka bata izinin shiga sannan ta bude kofar a hankali ta shiga,   Doctor hisham kawai take kalla tana murmushi ta karasa ciki ta ce"Morning Dr"  ya mayar mata da murmushi ya ce"Morning Fatima,  how are u?" A hankali ta ce "I'm fine Dr, i though u are leaving now". 

Dr hisham ya kalli wristwatch din hannunsa ya ce"I have 1 hour left, have a seat" ya karashe magana yana nuna mata kan sofa,  juyawa tayi a hankali zata zauna ta ce"But Dr pls i don't want injection this time around i need just dru... " shiru tayi tana kallan Mutumin dake zaune kan sofa yana danna waya, saam bata kula da mutum a wajen ba, and his face look very familia, ta dan hade gira in a very low voice ta ce"Morning" ba tare daya dago ba ya ce"Same" daga haka yaci gaba da danna wayarsa, ta juyo tana kallan Dr dake rubutu ta ce"Can i have them now?" Ya ce"Yes wait a minutes, how is Abba?" Ta zauna kan hannun kujeran ta ce"He's fine".

Very gentle mutumin gefenta ya tashi ya ya karasa wajen Dr Hisham ya mika masa hannu ya ce"Dr I'm going, thanks for all" Dr yayi murmushi ya ce"Alright friend Allah ya sauwake" zame hannunsa yayi cikin na Dr ya mayar cikin pocket dinsa ya ce"Ameen" daga haka ya nufi kofar fita a office din. 

Doctor Hisham ya mika mata takardar daya rubuta mata magunguna ya ce"Gashi, idan kika siya a pharmacy zasu miki explaining just like they used to" ta kar6a takardan ta ce"Thank u, and when are u coming back from cairo?" Ya ce"I'm spending just 5 days, idan akwai matsala u can meet Dr Aryan zai maki komai" ta ce "To nagode", daga haka ta fita a office din ta wuce pharmacy.

Still mutumin nan yana tsaye a wajen, ta samu gefensa ta tsaya tana kallan fuskarsa daya hadeta ko walwala babu unlike ranar daya taimaketa. 

Kallan magungunan da aka masa packaging kawai take, sak irin nata wanda take sha, kenan shima irin ciwanta gareshi? Abinda ta fada cikin ranta kenan. 

Mika nata takardar tayi bayan an sallameshi ya bar wajen, cikin few minutes itama aka mata packaging nata ta biya kudin sannan ta bar pharmacy din cikin gaggawa saboda bataso mutumin ya mata nisa. 

Tana shan kwana ta ganshi a zaune ya limshe idanuwansa kamar me bacci,  ta karasa a hankali ta tsaya a kansa ta ce"Assalamu alaikum"  ya bude manyan idanuwansa cikin cool and sweet voice ya ce"Wa'alaikum salaam" ta danyi murmushi dan batai tinanin zai amsa ta ba, wasa ta farayi da ring din hannunta ta sunkuyar da kanta kasa sannan ta ce"Thank u once again for helping me the other time, lokacin dana farka Salma tace min ka tafi, sai yau Allah ya hadamu, thank u so much" kallanta kawai yake yana sauraronta since she started talking, ya sauke kansa kasa ya ce"Ba komai, ki dinga kula" ta ce "Insha Allah" daga haka ta juya zata tafi ya ce"Your name" ba tare data juyo ba ta ce "Fatima Rafi'ah" ya mike tsaye yana kallanta ya ce"I'm Yusuf Muhammad" sai a lokacin ta juyo ta ce"Nice to meet u, thanks much" daga haka taci gaba da tafiya tanajin ta sauke wani babban nauyi na masa godiya da tayi.

Ta bayanta taji ya ce "Rafi'ah" ta tsaya caak sai kuma ta juyo tana kallansa, da alama binta yake a baya, ya karaso wajenta yana folding hannayensa ya ce"Can u pls pretend as my girlfriend?"

Zaro ido tayi tana kallansa ta ce"What!" Ya gyada mata kai looking into her eyes ya ce"Yes, pls do help" cikin sarkakkiyar murya ta bude hannayenta tana kallansa ta ce"But why?" Hannayensa duka ya saka a pocket dinsa ya ce"I will explain ltr, just go back and have a seat there". 

Kallansa kawai Rafi'ah take with some expression, bayan 2 minutes ta dauke idanta a kansa, dai dai nan phone dinsa ta fara ringing, ya zaro wayar a aljihu ya dauka yana kallan Rafi'ah da kanta ke kasa ya ce"Hello Aunt... Ehh na daukota", from the other side Aunt dinsa ta ce"Zata bimu gida kenan kaga sai mu gaisa da kyau" kansa ya dan shafa ya ce"No no, i told u she can't follow us, just wanted her to great you and then she will live" ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce"Ohk to ku karaso mu gaisa"  ya ce"Alright Aunt". 

Kallan Rafi'ah yayi ya sauke phone dinsa a kunnensa ya ce"Let's go" ta dago tana kallansa sai kuma ta girgiza kai ta ce"Noo, i can't pretend, how will i even start? Driver na jirana kuma" ya ce "Just few minu..." Kafin ya karasa magana ta juya ta fara tafiya, binta ya dingayi da kallo yana tinanin what's  the next thing to do, gashi ya fadawa Aunt dinsa sun iso asibitin. ta danyi tafiya me nisa kafin ta juyo ta kalleshi taga ya koma yana tafiya a hankali, duk sai taji bata kyauta ba, gashi ranar da ciwanta ya tashi he's the first daya taimaka mata a wajen ba tare daya santa ba, why won't her help him too? A hankali kuma ta ce"But i can't pretend, ta ina ma zan fara?" shiru tayi tana tinani, bayan few minutes ta nufeshi da niyyar ta yarda zata taimake sa shima, a inda ta sameshi dazu a nan wajen ta sameshi yana zaune just like before ya kama kansa, cikin sanyin murya ta ce"Na amince" ya dago yana kallanta ya ce"Are u sure?" Ta gyada masa kai, tashi yayi ya nufi wajen parking ta bishi a baya, sai buya take kar Mustapha dake caan gefe ya hangota, front seat Yusuf ya bude mata ya ce"Bismillah" ta shiga ta zauna sannan ya rife ya zagaya mazaunin driver ya sawa motar key suka bar harabar wajen. 

Wata hanya yabi a cikin asibitin inda ya bullo dasu wani sashe daban an rubuta pediatrics clinic & ward, parking yayi ya juyo yana kallanta ya ce"Office dinta yana ciki, zamu shiga" ita dai sai kallansa take cike da mamaki, to menene dalilinsa na karyar budurwa, lokaci daya kuma zuciyarta ya tsinke, tofa kar watarana suzo da Umminta matar ta ganta ta nuna ta santa, wata zuciyar kuma tace bafa komai kije kawai. "Rafi'ah" jin ya kira sunanta yasa ta dawo daga tinanin da take, fitowa tayi shima ya fito sannan yayi gaba ta bishi a baya, tinda take zuwa asibitin bata ta6a shiga wajen ba, yayi kyau sosai, ga doctors turawa da bakake sunata zirya cikin clinic din, suna dai dai office dinta idansa ya sauka akan magungunanta dake hannunta, yasa hannu y kar6a ta tsaya kallansa ya ce"Idan mun fito zan baki" daga haka ya cusa ledan cikin aljihunsa ya murda handle din yana kallanta ya ce"Come in". Da sallama ya shiga tana biye dashi a baya, ya danyi murmushi yana kallan Aunt din  tasa ya ce"Yau dai na cika alkawari ko?" Fara'a sosai matar take tana kallan Rafi'ah da kanta ke kasa ta ce"Masha Allah, u made it brother, wallahi na zata zakamin just like the other time" tasowa matar tayi daga mazauninta ta rungume Rafi'ah da zuciyarta ke bugawa, ta kama hannunta tana murmushi ta ce"Sannu da zuwa Kanwata pls have a seat"  ta zauna  tana kallan matar da take ta farin cikin, kallo daya zaka mata ka gane she is so happy at that time. 

Yusuf ya kalli Rafi'ah dake zaune kan kujerar office din ya ce"Sweetheart meet  our first born, she's Anty Khadija by name" murmushin karfin hali tayi ta ce"Ina yini Anty" Anty Khadija ta kamo hannunta ta ce"Lafiya kalau kanwata, fatan kuna lafiya, yasu Mamanki?" Cike da nutsuwa ta ce"Suna nan lafiya kalau". 

Daga haka Anty Khadija ta mike ta bude fridge din dake office din ta dauko mata drink da glass cup ta ajiye mata a gabanta ta ce"I hope watarana zakije har gida ki gaisheni" murmushi Rafi'ah tayi ta langwa6ar da kanta kawai, Yusuf dake danna wayarsa ya dago yana kallan Aunt din nasa, sai dai baice komai ba, Anty Khadija ta kamo hannunta ta ce "Ur name sister" silenty ta ce"I'm Fatima but ana kirana Rafi'ah" Murmushi me kyau Anty Khadija ta sakar mata kafin ta ce"Wonderful, u are bearing our Mum's name" kara saukar da kanta tayi tana ta wasa da ring din hannunta, Anty Khadija ta mike ta ce"Bari na kira a kawo maki abinci" Yusuf ya dago da sauri ya ce"A'a Aunty yanzu zata tafi fa" harara Anty ta maka masa ta ce"Bafa Yusuf nace za'a kawowa ba" ya mike yana kallan Rafi'ah ya ce "Let's go" Anty Khadija ta bude baki tana kallansa ta ce"Are u ok Yusuf, ko ruwa ka barta tasha mana" har zaiyi magana wayar Rafi'ah ya fara ringing, ta kurawa screen din ido tana kallo ganin sunan Umminta yayi appearing, nan da nan kirjinta ya hau bugawa da karfi, karfa ta kira Doctor yace mata ya sallameta tin dazu. 

"Who's that Fatima?" Muryar Anty Khadija da taji ne yasa ta mike tana kallanta ta ce"Is my Mum, i think i have to go Aunt, thanks for d care and i appreciate" Anty Khadija ta sauke ajiyar zuciya ta ce"Ohk, Allah ya tsare, ki gaida mutanen gida" daga haka ta kalli Yusuf dake shafa tulin gashin kansa ta ce"Burinka ya cika" ya danyi murmushi ya ce"Watarana zata zo maki gida Aunt" daga haka ya nufi kofa Rafi'ah ta bishi a baya tana kara yiwa Aunty Khadija sallama, binsu tayi a baya ta rakasu har mota sannan ta dawo ciki  daga nan yaja suka bar wajen. Suna komawa inda ya dauketa tayi saurin bude kofar zata nufi nasu motar ya riko hannunta ya ce"Your drugs".

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post