[Book] Masarautar Jordan Complete Hausa Novel by Maman Fareesah

Masarautar Jordan

Title: Masarautar Jordan

Author: Maman Fareesah

Category: Fiction

Doc Size: 524KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2020

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya Maman Fareesa mai suna "Masarautar Jordan" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: Fasa ihu Anim yayi cikin karaje, ya shiga fasa duk wani abu me amfani a gurin, juyawa yayi yana kallon bokan. Take idanunshi suka zama yellow,  wani irin hayaki  ya fita  da mugun gudu suka shige idanun bokan, take bokan ya sheka ihu yana shure-shure. Tuni ya sheka lahira, shi kuma Anim ya koma ya zauna, yana numfashi.

*"SAFINAH! ta yaudara ta auri wani bani ba! Sai na bata kyauta ba musamman"

      *Flashback*

A ranar da motar Anim tayi hatsari, ba a cire shi a raye ba ya rasu. Kasancewar akan Idon Hjy Nuratu! Aka yi abin sai suka yi amfani da damar su suka ɗauki gawar zuwa gidan wani tsohon maharbi amma bokane. Kallonsu yayi cikin mamaki yace.

"Abinda kuke bukata akwai hatsari sosai."

         Cikin ko ina kula mamie tace.

"Duk hatsarinsa ina son a lalata rayuwar yarinyar ce, ta yadda bazata farin ciki ba, kuma kaga ya mutu da burin mallakarta, idan muka daga shi da wannan burin Toh zai addabi rayuwarta."

   Shiru bokan yayi yana kallon gasar Anim wanda jini ke fita a cikin sa, tashi yayi ya shiga dakin shi can sai gashi ya fito, yace.

"Mu kama gawar zuwa ciki"

Haƙa suka kama shi zuwa cikin dakin, suka shimfida sannan, ya share gefen guda ya fara kunna candry, ja,baki,fari,.... Aka shimfida wani har kyale, suka daura shi akai sannan suka koma gefen, bokan ya cigaba da aikinsa.

         Sun kusan awa guda suna abu guda Kafin bukatar su ta biya, dan dakin guguwa ce ta cika dakin Can ta lafa sannan suka ganshi zauna kanshi sunkuya.

    "Anim Matawalle!"

       Sake kiranshi sukayi amma bai d'ago kansa ba, sai da suka yi a karo na uku ya d'ago kanshi da Idanunsa da suka koma yellow.

     "Mun tashe ka ne dan ka dauki fansan abinda aka maka, idan bai maka ba zaka iya komawarsu kayi kwanciyar ka."

          Wani baƙin ruwa ne ya shiga sauka a Idanunsa, ya fashe da kuka, basu dakatarshi ba.

    "Sai na hana kowa nutsuwa sai na cusa musu damuwa da bakin ciki. Sannan na kashe SAFINAH haka ne zai kashe wutar fansan dake ci a ruhina."

            Sun jima suna kara mishi hudubar tsiya, sannan suka barshi a dakin.

     (Motar sau dama mutane na tambaye akan ghost, shin akwai su? Scale Basu domin duk wanda ya mutu ya mutu ne dan aya guda ce mutuwa, mushrikai batattu sune suke haifar da ghost, ta hanyar amfani Ni da demons, bakaken ifiritai dan haka sai ku duba halin da Anim yaƙe ciki, kuma abinda na manta shine su Demons suna, aiki da Burin dake rn mutum ne, da burin da ya mutu akai.)

  ........ Tun daga ranar Anim ya fara wannan abubuwan da suka faru a baya, kallon gawan bokan yayi sannan ya tsallaka shi.

      ***

Rufa min akayi suka shiga min fifita, Khalilah suka shigo da Ummi. Ruwa Batul ta watsa min, ajiyar zuciya na sauke tare da atishawa. Kuka nake son nayi amma yaki zuwa min lumshe idanuna nayi. Tare da juya musu baya.

     Fita Duk sukai aka bar ummi ita ɗaya a dakin.

      "Sam banga abin damuwa ba! Tunda....

*"""

...... "An rigada an daura toh me nasuma kiyi hakuri ki rungume kaddararki, karki zama mara godiyar Allah mana, idan kina haka ya kike son Ni naji, don Allah ki kwantar da hankalinki, kuma kiyi biyayya ga mijin da aka baki. Koda kuwa jinjirine, toh kiyi mishi biyayya, idan kika min haka kin gama min kome,"

           Kuka ne ya kwace min, shi kenan sun rabani da Dr. Rufe idanuna nayi. Naki magana haka ta gama min nasiha ta fita, taja min kofar haƙa na cigaba da kuka, su kuwa basu fasa shagalinsu ba, ina jin Yadda gidan ya kaure da hayaniya, ji nake kaman kaina zai kunne, ga zazzaɓin da ya rufe ni.

       Babu wanda ya kuma bin kaina, sai wajen karfe uku Ummi tashigo min da lafayya, peach colour. Ta shiga ban daki ta haɗa min ruwan wanka, haka tasani a gaba har ban daki, ta taimaka min na cire kayana sannan tafita, a sannu na shiga cikin ruwan wankan, Banda kamshin turaren wanka babu abinda ke tashi.  Banɗakin gaza fitowa nayi sai da ta min magana, sannan na fito. A hankali take shirya ni.

   "SAFINAH!!! Yanzun kin fita daga ikonmu kin shiga ƙarƙashin ikon abokin rayuwarki! Kin buɗe wani sabon shafin rayuwarki, wanda yake d'auke da kalubale da yawa tare da matakai hawa hawa, a yanzun kina matakin farko na Amarya.

    A yanzun yan uwansa da danginsa zasu zo domin samun alaƙa a tsakaninku, idan kina da dabara sai ki janye su. Zuwa jikinsu, dukda wasu dangin ba a iya musu amma dole ki rufe idanunki ki kuma mikar da hannunki a koyaushe hannunki ya zama shine a sama da nasu, Mahaifiyarshi, dole koyi yadda zaki kyautata mata, badan kome ba sai dan ya haifa miki miji,  ta kuma bar miki shi, wannan matar ta cancanci a yaba mata, sai dai ki sani wasu suna da kawazuci akan yaransu, koda zata fito miki da wani hali kiyi mata uzuri, dan ita ɗaya tasha wahalar shi, dan yau ta nuna jin zafin ta akanshi karki ga laifinsu, dan ko kece kika wayi gari ana juya miki akalar yaronki sai inda karfinki ya ƙare.  

Sai matakin zamantakewa, babbar matsalar da muke fuskanta a cikin wannan karni shine mata sun koma kamar Jakuna akan jima'i, no shi din kamar jijjiyar bishiyar Aurece, ko nace hanyan bishiyar aure. Sannan idan babu ita a cikin rayuwar aure toh ana fuskantar kalubale, wanda yakan kai har kotu a raba auren, idan kuma aka samu yayi yawa shima akan iya raba auren,, sabida zai zama cutuwa. Abinda yasa mai miki magana saboda Yadda wasu matan suke mu'amala da magungunar mata, wanda sanadin haka ya haifar musu da matsala, kafin ki fara shan maganin ki fara duba wani Irin miji gareki, dan akwai maza dayawa. 

Wani ko ya'ya yaga mace, toh yanzun zai shiga cikin lalura bukata, wani kuma idan mace zata kwance gayarta ta kwanta a gabanshi fesa zai tsallakata ya wucce, wani kuma da zaran sun shiga fagen fama da mace, ko minti biyar baya kaiwa zai sauka, wani kuma har sai ki ce mishi kin gaji bazaki iya ba, yake iya jin tausayinki, ya kyaleki, idan kina fahimci miji ko yana da buƙata amma baya komawa, maganin mata banɗaki bane, sai dai fruit. Da tsarki da ruwan zafi, idan kuma kika fahimci yana da matukar damuwa toh dole ko zama me haɗa maganin mata da kanka domin bana son ko sayi magani a gurin kowa.

    Sai matakin mijin shi kanshi sai kin iya zama dashi, in ba haka toh ko shekara baza a rufa ba zai sakoki, shi na miji ko ya'ya yake yana ma'aurata son girma, wani lokacin kai za'a batawa amma dan a zauna lafiya zaki bashi hakuri, kuma yayita shan kamshin sai jiki kamar ki rufe shi da duka ya miki laifi kina bashi  hakuri yana ce miki.

"Eh ai dan kin renani ne, dan kin ga ke ɗaya ce wallahi kika sake na karo aure zaki sha wahala, dan matukar nasami Macen da zata daina bata min toh"

  Yadda kasan kike da tsiwar nan zaki amsa mishi, wanda kuma yin haka ke tinzirasu yayita fada Yana kunyataki a gaban mutane, haka ba dai dai, bane idan zaki iya hakuri yazo da zafin kan nan,

     Nadan zaki ji zafi amma sai ki shanye kice toh ai wallahi aka hutar dani, yawan aikin gida, kuma ka samomin abokiyar hira, Allah wane nice zan haɗa maka kaya, ke ya gaya miki dan ki fusata ke sai ki maida mishi dan yaji cewa baki da damu akan haka, karshe idan yaga baki damu ba ce miki zai yi mahaukaciya, ke har murna kike dan zan kara aure, k'inga kinyi laifi yazo yana faɗa kin manna mishi hauka, matsalar da muka samu ke nan a cikin alummar hausa, wata mace tana ƙoƙarinta amma mijin baya gani, wata kuma zaki sha mamaki idan.kia ga yadda mijinta yake kokarin Ganin ya kare mata mutumci amma bazata gani ba karawa ma sai ta haɗa mishi da fitsari, wanda haka na cirewa namiji soyayyarki a zuciyarshi, dole mu zamo masu hikima dabara, dan wallahi wani na mijin baki taba cin amininsa sai da dabara, wani kuma kome zaki yi idanunsa na kanki, kiyi ƙoƙarin sanin waye mijinki, dabi'arshi ma'amalarshi da jama'a, babu ruwanki da wayarshi. Sannan mataki na gaba kishi toh kishi ke kawo kishiya, musamman jahili kishin da ake yin nan na kashe  mazaje kishi, halal ne. Amma banda mahaukacin kishi, nayi imani da Allah kin haddace Alkur'ani, tartilil da tafsir, kinsan wasu hukunce-hukuncen akan addini. 

Kuma kina da sani akan addu'o'i, zanyi bakin ciki naji kina daga mishi hankali akan kinji yana waya da wata, sabida kuna ƙoƙarin dakatar da abinda ALLAH yace ne, idan kika nuna bai isa ya kawo miki ita ba, kin isa ki hanashi bin matar layi ce, kuma yaje yayi yadawo gidan yayi wanka, me tsoron Allah shine zai yi a waje amma wanda ya riƙa, a cikin ban dakinki zai yi kuma ya zo ya kwanta a gadon, saboda yace zai aure kince da yayi gwara a yadda Abuja da Bama bamai, kin hanashi, ba dole yaje wajen gun matar banza ba, matukar kika iya da mijinki. Kuma kika masa Adalci a zaman kuma kika nuna mishi dan Allah kike zauna dashi, Wallahi bazai taba cutarki ba, idan kika rike Allah babu yadda ya Isa cutar dake."

  Ummi bata barni a haƙa ba sai da yayita fada min wasu dabarun da yadda zan zauna da mijina yan uwanshi mahaifiyar shi, abokansa da makotansa, uwa uba Yadda zan kilace mishi dukiyar shi, yadda zan kula da al'amuran shi. Sosai ummi tayi min bayani akan rayuwar aure, tun ina jin kunyarta har na sake, tana gama min tace."

"Hmm! Ki daina jin kunyata, dan Ni banga abin jin kunya ba, kiyi ƙoƙarin bin mijinki zaki zama taurariya, sannan iya gyaran jiki aka miki, idan an kwana biyu ki min magana akwai haɗin da za'a kawo min daga Maiduguri. 

Kin nutsu don Allah ki bar wautar nan kingan rayuwar aure, kin ajiye kuka da shirme ki, bana son rigimar, ki zauna lafiya da kowa koda wasa bana son rashin kunyar nan, sai miskilancin nan ki ajiye a gefe, ki rungume Rayuwar Aurenki. Ban sani ba amma toh Allah ya baku zaman lafiya da kwanciyar hankali."

Daga haka tayi ficce abinta, can sai ga Nanah Asma'u da abinci, kasa ci nai sabida bana jin dadin kome...

     ....... Da yamma ina kwance suka kawo me makeup, aikuwa nace bani so, indai dan Ashraf za a min kwalliya wallahi bazanyi, ba kai kira na tsani Ashraf, ehhe.

   Ganin naki yardar Amin kwalliyar suka kira Ummi aikuwa na bare baki nayita kuka, karshe tace su ake kawai, tunda bana so, haka nayi ta juyin Abuna ashe dinner suka shirya zasu yi, naki kula batun, sai da aka fara mangariba na tuna Dr da yace shi zai zo ya ɗauke dan ya gama mana visa, kuka na cigaba dayi kamar ƙaramar yarinyar, Bayan sallar Isha, aka zo fita dani, dakin ummi aka kaiyi tayi dan abinda zata Iya, sannan aka zo zasu kaini dakin Abba, anan ne nace bansan zancen ba, na rike ummi ina kuka. 

Itama kuka take sabida na riƙe sosai dakyar aka cireni a jikinta ina kuka, sannan suka kaini Palourn Abba nan shima yayi min nashi, sannan ya sakawa Umma da Aunty Inna, da Ya kaka Yayarsu Ummi. Aunty Kuma Yayarsu Abba, suka fita dani, tare da rakiyar mutane. Tunda aka sani a motar na kifa kaina, nake kuka har muka bar gidan, bansan unguwar da suka kaini ba. Na dauki Umma nacewa.

   "Yawwa shiga da bismillah, Ubangiji yasa an kawo ki kenan sai dai ki rakashi ko yarakaki,"

 sai da naji zuciyata ta buga yo taya zanso haka ai duk k'iyayyarsa da nake ji bazan so naga gawan Uban yarana ba.

   Take zuciyata tace.

*Umma Zance ki Inconcluvise 🙅🏽‍♀️, don da yarone angon ba zanyi fatar takaba ba, sai dai Ni narigashi Dan nayi imani da Allah babu Macen da ta isa rabashi da yaransa, idan kuma ta nace zata sheka*

        (Ki min munahuka😏 kice baki sonshi ki kuma koma hmm)

     A baƙin gado akace na zauna, da bismillah nan suka shiga bin gidan wanda yaji kyau bana wasa ba, kitchen dina kuwa kome na ciki orange da brown ne, dakine akayi amfani da minti green da cream. 

Sai falon inda aka hada black & Whiter, kowa sai magana yake akan gidan, tsarin gidan Ni kuwa ina can na cusa kaina tsakanin cibiyoyina, ina jin suka gama suka tafi, sai Batul da Khalilah aka bar min,  bayan tafiyarsu. Sai ga abinci aka  kawo mana, lokacin na shiga ban daki,  bayan tafiyar masu kawo abincin na fito, suna min magana na haye can karshen India best ɗina na kwanta, ban kuma bin takansu barci yayi gaba dani, saboda ciwon kan da nake fama dashi...

      ***

        Da asuba ina tashi nayi wanka da alola, nazo na gabatar da sallah,ina azkar su Khalilah suka tashi ban daki suka shiga, ina jin fitowar su lokacin Ni har na kwanta, barci me karfi yayi gaba dani, dan nasa damuwa a raina. Kuma ya haifar min da zazzaɓin me zafi, har zuwa ranar ina kwance ana hidima. 

Zuwan Dudu dan Sophia ta gaya mishi gani nan ba lafiya allurar da magani ya bani, sannan ya tafi. Ina jin akwai wani abinda za ayi amma ganin bani da lafiya dole suka hakura, Ni kuwa da ake gun gwara nayi pretend bani da lafiya, dan bazan je wata uwar mata dani ina tafe dan jinjirin kanina na nunani a matsayin matar shi tirrr, wallahi bani zuwa ko ena, a gidan ma sabida kar ayi dani yasani yarda aka min kwalliya, amma da bazanyi kome ba. 

Na tsani wannan auren da shi mijin ma, sai na shuka mishi rashin mutunci sani yake zancen, sai yayi Yaren Jordan bayan larabci, sai ya gwammace bai Aureni ba, mayye kawai dama larabawa me suka sani da zaran sunga mace, penis dinsu take tashi toh sai naci Uwar zandariyar ma, dani yake mara kirki ko yaushe yasan dadin mace da har iskancinsa bazai tsaya kan kananun ba sai Ni guzumemiya dani wai zai aura lallai nayi sake Reni me girma ya ratsa tsakaninmu da Ashraf dani yake zancen zan kamashi sai ya gane bai da wayo....

 Anya Didi....

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post