[Book] Na Cuceta Complete Hausa Novel by Ummu Maryam

Na Cuceta

Title: Na Cuceta

Author: Ummu Maryam

Category: Love Storg

Doc Size: 595KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2018

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya  Ummu Maryam mai suna "Na Cuceta" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: Cikin wani gidan Wanda ke ginin kasa mai dauke da daguna biyu wata yarinya ce wacce bazata wuce shekara shabiyu zuwa sha uku ba ke daka sai tim Tim Kawai kakeji saboda yanda take dakan garin furan dake cikin trumi, daga dayan gefen  Kuma wata matace ke hura wuta sai kafawa murhun bakin take tana hura wutan, duk idanuwanta sun chanza kala saboda yanda hayake ke shiga idonta, wata yar yarinya na gani ta taho da gudu da wata faifai

"Ammi ki hura da wannan....".

Yarinyan ta fada mata, matar dake durkushe gaban murhun dagowa tayi ta sakarwa yarinyan murmushi tare dacewa "Yauwa...nagode binto..." Matar ta fada tana amsan faifan daga hannun yarinyan.

Da ganin Matan da yanayin gidan kasan gidan kasan masu karfin haline sosai don komai NA gidan is low to the last core, yarinya dake dakan goge zufan goshinta tayi ta kalli matar da aka kira da ammi tace.

"Gaskiya ammi gobe mu kai injin...NA gaji da daka Wallahi hannuna duk ya kumbura.. Nidai NA gaji..." Tafada tana turo baki tare da kallon tafin hannunta ya kumbura saboda yawan daka

 Ammi kallon ta tayi Sannan ta maida dubanta ga muhur  "In banda abinki dije AI kin San da wannan dakan muke samun abinda zaa bawa awakan nan ...in an kai inji ba su bamu dusa..." Ammi ra fada tana hura wutan, dija Kara turo baki tayi.

"Wai ammi dole ne mu bar wayan nan awakan?... A saida su mana Kawai..." Tafada in I don't care manner, ammi kallon ta tayi ta tabe baki.

"Ai babu abinda kika Sani..maza ki kara kar su saude su bar ki yau ma..." Ammi ta fada mata bayan ta gama hura wutan. Dija kara turo baki tayi

"Nidai NA gaji....binto..." Ta kwalawa kanwarta kira, 

"Naam...." Yarinya ta amsa mata

"Zo ki tayani...." Tafada tana barin tabaryar cikin turmin, ammi kallon ta tayi 

"Wai ke wace irin banzar yarinya ce?...yanzu binto zaki barwa dakan furan?.... Dalla ki maida hankali kar lokaci ya kure...sakara Kawai.." Ammi ta fada tana debo taliyan kadi daga kan igiya tana zubawa cikin kwarya dake hannun ta. 

Dija tana turo baki ta dake furan ammi tayi molding dinshi ta zuba mata cikin roban da take zuwa talla da ita Sannan tayi mata gammo, 

"In kin saida ki sayo magi da hamsin... Fulawa quarter..sai ki sayo sabulu guda daya Dan hamsin da biyar..." Ammi ta fada mata tana Dora mata gammon bisa kanta, dija dai Bata ce kala ba don in da zaa kashe ta ya fiye mata wannan tallan da take amma Kuma Bata Iya kin zuwa saboda ta nan suke samun mostly abinda suke amfani dashi da yau da kullum, furan ammi ta dauki ra aza mata bisa gammon har lokacin Bata bar kumbure2 ba.

Also Download: Za Ki San Ko Ni Waye Complete by Ummu Maryam

"Wai ke meke damunki?..." Ammi ta tambayeta, kara turo baki tayi

"Ni wallahi ammi banason talla... In munje garejin daura duk yawancin mazan yan iska ne...." Baki ammi ta bude tana kallon ta, dija ta cigaba dacewa

"Sai suce sai sun taba mutum Sannan su sayi furan sa...." Idanuwa ammi ta zaro tana mamakin abinda yarta take fada mata, kallon yarinyan tayi ta kalli kirjinta dake dauke da boobs yan kanana da basu gama developing ba, 

"Wallahi ammi jiya wani cemin yayi in zauna kan kafanshi ya sayi dukkan furan..." Ta fada tana fashewa da kuka, da Sauri ammi ta sauke furan daga kanta tana cewa

"Wai da gaske kike?..." 

"Wallahi ammi... Da ...gaske...nake....kullum haka suke mana...wasu sun girmi kawu nanu amma duk yan iska me...ni wallahi ammi banason talla..." Ta karasa maganar ta cikin matsanacin kuka, ahankali ammi ta zauna kan Dan kujeran dake gaban ta tayi tagumi Kawai sai ta fara hawaye, 

"Ya Allah.. Gamu gareka...ga yar marainiyarka gareka...ya rabbi kar ka bari a cutar da yar marainiyarka...." Tafada cikin kuka, kallon dija dake hawaye tayi Sannan tace

"Dija...inda nasan yanda zanyi da ko kadan bazakiyi tallaba...amma ke kanki kinsan halin da muke ciki... Kin koshi da taliyan da kika CI?..." Ammi ta tambayeta, cikin kuka ta gyada mata kai alaman AA,

"To kin gani...dukda tallan da kike ba koshi muke ba...kiyi hakuri ...wata rana sai labari..." Ammi ta fada cikin kuka, dija Dan turo baki ta kara tana cewa

"To ammi ki yiwa inna ladio magana mana ko zata samo min gidan aiki a birni kaman yanda Ladidi takeyi...." Idanuwa ammi ta zaro,

"Allah ya sauwake...ban yarda kije aikatau....ke Kawai Allah ya rufa mana asiri..Kuma kar ki yarda wani ya taba koda akaifanki ne balle jikin ki...kina jina?..." Ahankali ta gyada mata kai ta Kara cewa.

"Nidai ammi..nafison..." Sallama wasu age mate dinta yasa tayi shuru Bata karasa maganar da tayi niyyan fada ba, yan fura2 ne kusan su takwas suka shigo Dan karamin gidan

"Kam yau anci saa kin shirya baki tsaya bata mana lokaci ba..." Inji daya daga cikin yanmatan, hararanta dija tayi 

"To uwar iyayi..." Inji dija, ammi Dora mata furan tayi tana cewa

"Kar ki manta abinda NA fada maki..kinji?.." 

"To ammi..." Tafada Sannan suka fita daga gidan, daman da akwai wani mai motan dake daukan su daga kauyansu zuwan cikin garin daura dake jihar katsina. Ammi daki ta shiga, nima binta dakin nayi, ina ganin yanayin rayuwarsu nace alhamdulillah Allah dai yasa babu wayanda ke zaune a irin wannan gidan a zahirin rayuwa don their life is low beyond words, tagumi ammi tayi tana tunanin yaushe wahalan su zai kare don kullum gani take kaman is getting worse, gashi yaranta hudu Kuma dija ce babban cikin su, 

"Hmmm..ya rabbi ka tausaya mana..." Tafada tana Dan mikewa kan tabarman dake kasan dakin da ko cement babu.

A chan wani bangare NA Kano kam wani gida ne cike ana ta bude akwatuna da alaman lefe aka kawo, duk wacce ka gani kasan yan Hutu ne don every body around is glowing kaman  babu wahala cikin duniya. 

"Amma wannan kayan sun hadu da yawa..kayan kaman na mata biyu?.." Inji wata mata, Dariya Matan wurin suka saki Sannan daya daga cikin su tace

"Ai yanda mutum yake hakan komai nace yake...baku ganin yanda diyar tawa take kaman ita tayi kanta?..." Inji wata mata, guda daya daga cikin su ta saki don murna.

A daya daga cikin dakunan gidan kam wata beautiful lady ce zaune kanta babu headtie sai yanmata biyu zaune kusa daita sai hira suke, da alaman lefen ta aka kawo, 

"Kinsan wallahi sai kin bani wannan swiss lace din...tunda an kawo maki uban kaya..." Inji daya daga cikin yanmatan dakin, wacce akayiwa magana Dariya ta saki Wanda yasa hakorin Makkah dake bakinta ya bayyana,

"Dan wannan babu case..." Shuru tayi ta kalli wayanta daya fara ringing, murmushi ta saki tana dauka wayan, yanmatan kallon juna sukayi suna cewa

"Halan angon ne?..." 

"Yes...babyna ne..." Tafada tana picking wayan, 

"Baby..." Ta fada cikin sexy voice, daga Chan bangaren aka saki murmushi, wani saurayi ne zaune a office, yana Dan buga pen dake hannun shi ahankali kan desk dake gabanshi, yana jin muryan Mufida ya ajiye pen din tare da yin mika Sannan yace

"My angel ya kike?..."

"Lafiya lau...ya kake ya rayuwa?.." 

"Alhamdulillah... An kawo kaya ko?.." Ya tambayeta in a low voice

"Yes baby....is so beautiful..." Tafada cikin whisper, Dariya yayi yana biting lip dinshi ahankali Sannan yace

"Not as beautiful as you...ai in ma shigo Kano sai NA kara kai personal shopping.. Kayanda babu idanuwan da zai gani sai ni kadai..." Murmushi mufida tayi tana sauraron yazid cikin so da kauna, 

"Is that necessary?.." Ta tambayeshi ahankali,

"Yes mana...ai wannan da kika gani choice din Hajiya karama ne...ni zanyi nawa bayan sun gama nasu..." Yarinyan da bazata wuce shekara 22 ba ta saki murmushi Sannan tace

"Baby yaushe zaka dawo?..." Ta tambaya ahankali, 

"In biki sauran sati biyu..." 

"Haba mai baby...ina missing dinka...ko baka missing dina?...." Ta tambayeshi cikin sanyin murya, Dariya yayi ahankali Sannan yace

"Ina missing dinki mana...in nazo kusa dake inajin kaman in cinyeki shiyasa ban San in zo sai nan da sati biyu..." Kukan karya ta farayi tana cewa

"Yanzu nan da abuja shine bazaka zoba?... Don Allah kazo wannan weekend din...pls..." 

"No...sai in the next two weeks... By then wedding din sauran sati biyu.. Kinji babyna..." Ya karasa maganar cikin whisper, 

"Hmm shikenan...kana ina?.." 

"Office..." 

"Kaci abinci?..." 

No..ko zaki zo ki bani?.." Shuru tayi Bata amsa mashi ba, hiran sukayi for almost an hour Sannan sukayi sallama, mufida wulla kanta kan gado tayi saboda murna, shi kuna ya kashe wayan ya Dora kafa daya kan daya tare da relaxing, karewa gayen kallo nayi sai naga kaman yafi mufidan kyau don ya hadu sosai, he's every ladies dream guy, bai ankaraba yaji an ture mashi kafa daga kan desk dinshi bude idanuwa yayi ya saki murmushi 

"Wai ka baka sallama ne?...kullum always boosting into people's office..." Inji yazid dake gyara zamanshi, Dariya gayen da ya shigo yayi Sannan yace

"Ka koya min sallama

 Mana...ustazz..." Gayen ya fada yana zama kan kujeran dake gabanshi, murmushi Kawai yazid yayi yana cewa

"Ai kasan ban yi karya ba..." 

"Muje muci abinci..." Gayen ya fada mashi, agogon dake kwance hannun shi ya kalla yaga har 3pm,

"Muje..." Yazid ya fada yana mikewa, laptop dinshi ya maida cikin bag tare da wasu files, kara kallon gayen nayi nace hmm am definitely dropping dead don yazid is killing me, tsayawa nayi INA kallon yanda yake abu very slow, komai nashi a nutse babu alaman Sauri ko.hanzari tare dashi, yafi minti goma yana parking abubuwa shi Kuma dayan gayen yana zaune yana kallon shi, sai da ya gama Sannan yace

"Mu tafi..." Yafada yana rataya bag din a shoulder dinshi, gayen kallon shi yayi

"Are sure ka gama don NA san halin ka da delay kaman mace..." Yazid tabe baki yayi yabi ta gefen shi ahankali ya wuce, yanda yake tafiya sai ka rantse bashi da bone ko daya a jikinshi don tafiya shi so sluggish. Gayen mikewa yayi yana cewa 

"Allah ya huci ran ango..."ya fada ya tarda yazid dake tafiya a hankali, banza yayi dashi 

" wai sauran kwana nawa bikinka?.." Gayen ya tambayeshi,

"Four weeks exactly..." 

"Wow...zan je Kano..I can't wait.. Allah ya hadani da mata yar Kano..." Inji gayen

"Ameen sultan..." Sultan kallon shi yayi yace

"Amma nasan kana da younger sisters.. Ka hadani da daya daga cikin su mana..." Sultan ya fada mashi, 

"Ni ba hadani akayi da my mufi ba...kaima ka nemo naka..." Ya amsa mashi atakaice yana danna lifter, kofan ya bude suka shiga ya jingina da jikin lifter yana cewa

"Am so tired.. NA gagara in fara Hutu wallahi..." 

"Ai kai kullum a gajiye kake..lazy guy..." Sultan ya fada mashi.

"Ai am not a racer balle in ce anason inyi gudu,...I believe in easy way ..." 

"Yeah...you believe in easy tunda you are lazy...kasan muje gym wannan weekend din kaga yanda guys ke motsa jiki...." Dariya yazid yayi Wanda ta bayyana well set of teeth dinshi mai dauke da madaidaishin wushirya daga tsakiya 

"Hmm mufida you are one lucky gal....," NA fadawa kaina, 

"Workout kaman wani Dan danbe?... Kai am OK the way I am...Kawai I love my self...I don't need to workout.." Ya fada suna fita daga cikin lifter, hallway suka nufa suna gaisawa da wasu Colleagues nasu na CBN abuja har suka isa parking lot Kowanne su ya dauki elegant car dinshi mai tsadan gaske sukabi bayan juna zuwa wata expensive restaurant inda suka saba cin abinci.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post